*💦💦WACECE ITA?💦
*page 25*
*na ummu zaid*👌🏽 Halo sister INA yini, zee ta amsa lpy lau ya kwanan Abdul shakur, lpy lau,kinsan fa bikin yaya suraj ya matso ankon ki a dinka nan kokuwa in zaid zezo namasa mgna ya kawo miki, zee tace a dinkamin anan KT din kawae kice munkusa rakashewa Allah ya nuna mana,Allah yayi albarka nagode sister, luby tace kinfara gidiar taki ko? hira suka cigaba dayi game da abubwan dazaa tsara da bikin kasancewar dama su luby basu taba bikin namiji ba yaya suraj dinne na farko danyaki aure seyazu Allah yayi,
Abbuh kabar maganar siyen gadon su nuwaera zanyi masu insha Allah nayi MA order din wasu daga Dubai, Abbuh yace Anya zaka iya gadaje har shidda Dan su umminsu sunce wae gado biyu wae akeyi, muqaddas yayi shiru sannan yace" ae na Zata dai dai akeyi Amma zanyi sauran abbuh, abbuh yace" kabar maganar nan kayi Dayan zanyi sauran Allah yamaka albarka, aransa yaji dadin adduar da AbbunSa yamasa, amsawa yayida ameen sannan sukayi sallama, mardiyya na cikin Daki bakin Ciki Kamar yakasheta Duk Abinda Suke fadi tanajinsu danhaka NE tafara magana ita kadae " kam Balain nan wlh bazae yiwuba, surutae takeyi ita daya Kamar mahaukacia Komae ya Tsaya mata tunda karkuzu ya mutu haryau bata hadu da bokan dazae mata aiki kamar yankan wuka ba, GA sholy Kuma number dinta kwata kwata bezuwa taje gidanta yafi a kirga Se acemata sunyi tafia, muqaddas dinma yanda yakejin tsoronta da yanzu Yarage kashi 50 cikin dari Zata bashi command Akan Komae yabita Amma dazaran takawo masa wargi Akan yanuwansa sukeyin kaca kaca, kwatakwata batada nutsuwa mafita kawae take nema( dama Duk Wanda baya neman mafita wajen ubangiji baya samun nutsuwa)
Yaune zee zasu bikin Yayan lubabatu danhaka tunda safe tashirya tahada musu kayansu bawan Allah se murnar yakeyi zasuje gidansu Abdul, Inna takalli zeenatu" wlh tafiyar nan daza kuyi jinake Kamar kadaku tafi, gidan zemun shiru dayawa zeenatu, zee tayi dariya "Inna Kenan babu yanda Banyi dakeba Akan mutafi kinki" Inna ta amshe "kada kimaidani tsohuwar kawae senaje nayi zaune gidan yara gotae gotae Har Sati guda kudae Allah yakaiku Lpy", zee ta amsa da ameen Tana cigaba dahada masu kayansu cikin akwatinsu......
Se yamma likis suka isa katsina saboda lalacewar da motarsu tayi a tsakar daji, da murna luby ta tari su zeenatu dan har tasha taje tadauko su, hira sukeyi cikeda farincikin ganin juna, zee tace" yabakizo da abdul yazo ya tare danuwansa ba, ahanya anmin magna zaazo wajen abdul har Nagaji da amsawa, luby tayi daria wlh namanta dashi kwata kwata inata dokin ganin sister , ahaka suka karasa gida sannan zee ta kai kayanta vq yayinda abdul da bawan Allah aka fara murnar ganin juna shaquwarsu abin mamaki ne kwarae saboda ba wani haduwa sukeyi ba sosae.
.
.
Yaune kamun su nuwaera da murjana kannen muqaddas, bayanda beyi da mardiyya tazo ba takiya tabige da karyar batada lpy hakanan yakyalleta yakamo hanyar kt, murjana itace zata auri suraj yayan luby, su luby amara kirjin biki kamar itace amaryar tunda safe aka gayyato me lalle dameyin dilka da kitso tamusu itada kanneta dasu zee, don yanzu maman luby tasan meke tsakanin luby da zee tun farko fatan alkairi tayimata dakuma jinjina ga diyarta na taymako, inna me abinci kuwa haryau ganin wautar luby takeyi, "zee kifito afara maki kitson tunda yammatan sunfison amasu gyaran jiki da lalle, zee tace nifa wlh da banyi niyyar yin kitson ba, luby ta amshe Alah kuwa baki isa ba, kawae kifito min" haka zee tafito aka fara yaryada mata kitso kowa semaganar kyan kitson yakeyi tinkan agama abinka da farar mace kuma gashinta baki ne wuluk me yawan gaske, luby itakuma tazauna akafara mata dilka da halawa, se yamma likis suka sallame masu gyaran jiki, zee kuwa ansha kyau, me makeup suka kira tayi masu makeup nan da nan sukafito sukayi ras, kowa se maganr zeenatu akeyi yanda tayi kyau, kanwar luby maryam kecewa "maman bawan Allah kinganki kuwa? yanda kikasan budurwa masha Allah daria sukayi sannan, aka fara tafiya wajen kamu, katon fili ne sosae kasancewar bikin yammata uku zaayi hall bazae dauki yawan mutanen dazasuzo ba, iya tsaruwa wajen ya tsaru wajen dangin angwaye kowanne daban brides family ma wajensu daban, inda suka ga an rubuta suraj family da fitila na haskwa su luby sukaje suka zauna, yayinda wajen ke tashin wakar kamshi kamshi yana tashi......., sosae aka tsara bikin amare suka shigo aka soma gudanar da abinda yakawo jamaa, kiran dangin suraj akayi su zo su sayi bakin amarya su luby cikeda murna sukatashi itada kanwar mamansu luby anty aisha, luby takalli zee maman bawan Allah kitaso muje mana, zee tace gaskia kuje kawae bawan Allah ya isheni da rigima kinsan bayason mutane, luby ta kamo hannunta badan taso fita filinba tabiyo ta dauke da bawan Allah, ummi dake zaune can gefe cikin kawayenta ta hango zee wacce taketa murmushi gabanta ne yadan fadi don tamata fuskar sani sosae, ahaka dae suka biya kudin sa lalle dubu 40 sannan aka fesawa amarya turare, ummi tace ma ammi nikuwa a dangin mijin murjana naga wata tamin kama da matar muqaddas, ammi tace ina take, savoda cikar mutane tanemeta tarasa, don haka ma tamanta da alamaryn dan mutane sunmusu yawa, cikin tsari da kwanciyar hankali aka gama komae sannan akatashi daga taro kowa yaja amare ana kashe hotuna, masu selfie na dagawa😁, luby taja hannun murjana suyi pictures haka suka dinga kashe pictures sannan sukama amaryarsu sallama suka fIto dan tafiya, bawan Allah nata Kuka dan har jikinsa yasoma zafi zee tariga su luby fita waje, kota ina motoci ne birjik dan haka motarsu taje ta tsaya tana rirriga bawan Allah taciremasa riga daga shi sae vest kawae, ajiyesa tayi akasa dan tagaji da ruko se ganin yaro tayi ya filla dagudu yaje ya rungume wani soja, yaron akwae son sojoji dasauri tabishi tareda riko hannunsa tafara bama mutumin hakuri, murmushi yamata" bakomae watakila namsa kama da babanshi ne fine boy," daukarshi tayi wanda dagowar dazatayi suka hada ido da muqaddas wanda ketahowa yatadda sojan dasuke tsaye.........
💦💦WACECE ITA? 💦💦 *page 26* *na ummu zaid👌🏽👌🏽*
**Faduwar gaba kowannensu yasami kansa a ciki, ita dae zee mutuwar tsaye kawae tayi ganin mutumin da kullum take gani cikin mafarkinta, yayinda muqaddas ke tsaye cikeda confusion tabbas yasan wannan matar, kafin ya farfado daga tunaninsa zeenatu tabace ma ganinsa se hangota yayi tashige cikin wata mota kirar pontiac maroon, soja dae tsaye yayi yana kallon ikon Allah lafia kake kuwa muqaddas? Ajiyar zucia yayi sannan yace wlh lpy lau commander kawae matar nan tamin kama dawata ce sosae da sosae shiyasa nake kokarin tuna inda nasanta, soja yace come on friend bar zancen nan ure just hallucinating, wannan ma ai daga gani matar aure ce dan ga babynta nan suna kama, share kawae janshi yayi lokacin matar commander ta iso suka shiga mota.................. Da daddare bayan an natsa zee kebama luby labarin dream guy dinta dakuma mutumin data gani mekama dashi dazu, luby ta kwashe da daria to kodae kinfara gane gane ne kuma, zee tace am so serious luby ba gane gane bane, luby tace to banamiki musu ba Allah yasa muji alhery, ameen ta amsa sannan suka cigaba da labarinsu....................
Muqaddas ne zaune akan resting chair din dake dakinsa shikam wannan matar ta bala'in Tsaya masa a rai he knows her ba tun yau, cigaba da tunani yayi gameda ita kwata kwata yakasa tunata, nan da nan jiri yafara dibansa yasan ciwonsa keson tashi dan haka a kagauce yafara dialling number din abbuh kan kace kwabo yazube anan yafara convulsing, abbuh ne ya dauka tareda fadin assalamu alaikum, jin shiru yayi yawane yasaka shi kashewa, tareda sake kiran muqaddas din amma baiyi responding ba, har abbuh ya sharesa kuma seyaji hankalinsa be kwanta ba don yanzu muqaddas din yabar wajensa,tashi yayi Tareda daukan waya yayi sashen mazan gidan wanda yana bude kofar dakin muqaddas din yaganshi yashe yanata gafari nan da nan abbuh yasaki salati tareda komawa waje da sauri, cin karo yayi da hisham kannin muqaddas din yadawo daga waje yace, "hisham maza yima wani yaron magana kudauko yayan ku a dakinsa ku kawoshi dakina," abbuh wani abun ne yasami brother? Abbuh yadaka masa tsawa" bance ka tsaya tambayata ba kayi abinda nace kayi sauri, sannan yashige dakinsa, ummi na zaune tace lpy abbuh, bata amsa yayi" jikin muqaddas ne yatashi cikeda tashin hankali ummi ta fara masa addua, segasu hisham ciccibe da muqaddas din duk jikinsa ya saki, ajiyesa sukayi tsakar parlourn abbuh, sannan suka zauna kusa dashi abbuh yace hisham dinga tofa masa addua bari mugani inya sake convulsing dinnan senamasa allura ummi jeki ki kirawo mamansa(ammi), dakyar ummi ta tashi takira ammi wacce shaf tamanta batasaka riga ba daga ita se daurin kirji, Kallonta yayi yace ammi jeki kisaka hijab, se lokacin ta tuna dayanda tafito sannan takoma tasako hijab, kara muqaddas yasaki me firgitarwa wanda su kansu abin ya maseefar basu tsoro tashi yayi dagudu yayinda hisham da sani suka taro shi wani karfi ne yazo masa ya zubar dasu tareda ficewa a guje, dagudu su hisham suka fito tareda bawa megadi umurnin ya kulle gidan, jin kofar dayayi a kullene yasakashi kwalla gigitarciyar kara me amon muryoyi fiyeda daya, hakan yasa duk yan biki akafito saboda karar tayi yawa amare se kuka akeyi ammi kuwa itama nan tazauna tana kukan se ummi ce me karfin halin basu hakuri, itama daurewa kawae takeyi wae yanzu muqaddas dinta ne acikin irin wannan halin? Mazan dasukazo bikine a ka taru aka danne muqaddas yayinda da wani danuwan ammi dayazo daga garinsu ya umurci sukaishi daki, ihu yakeyi yana bige bige haka aka daukesa akayi dakin abbu dashi yan ganin kwaf kuwa kowa soyake yashigo yaga yanda zaayi, masu tsoro kuwa tuni sun shige daki a sittin irinsu ameera da salma😂😯
Danuwan ammi ne ya cemasu"kusake shi" yayinda muqaddas din kekorin tashi yadaka masa tsawa, kyam yatsaya yana kallon malam uwaisu sannan malam yace zauna nace"babu gardama kuwa yazauna, malam yacigaba" zaka fadamana mekakeyi jikinsa? Shiru yayi yaqi magana malam uwaisu yafara karatu nan da nan muqaddas yafara gurnani sannan yafara fadin" zan rabu dashi wlh aiko ni akai kayi hakuri, malam yadaka masa tsawa waye ya aikoka, aljani yayi shiru can yace kayi hakuri nariga nadau alkawary duk rintsi bazan fada ba,malam yacigaba da addua wanda kan kace kwabo aljani ya arce, jikin muqaddas yasaki yafara nannauyan barci, malam yace wannan aljanin me taurin kaine gudu yayi alhaji kucigaba da nema masa magani inya tashi zedanji sauki, abbuh yayi godia sannan yace kowa yaje ya kwanta,anan muqaddas din ze kwana, haka kowa yatashi ammi taki tashi, abbuh yace, maman yara kije ki kwanta mana? Make kafada tayi kamar yarinya wanda abbuh seda yadan dara, a ransa yana mamakin irin soyayyar dake tsakanin ammin da muqaddas bawanda zece ba ita ta hayfeshi ba sam. Cikin dare wajen karfe 3 muqaddas ya farka zama yayi tareda kurawa ammi kallo wacce take zaune kan kujera barci yakwasheta tausayinta ne yakamashi dan yasan tabbas crises dinsa ne yatashi, tunanin matar yakuma yi wanda nan da nan tafadomasa a rae zeenat! Yafada da karfi tareda fashewa da wani gunjin kuka, ammi ta tashi a firgice tana salati, muqaddas lpy? daedae sanda abbuh yafito daga uwar daka, ganin irin kukan da yaronsa keyi bakaramin daga masa hankali yayi ba, tambayarsa suka shiga yi gameda abinda ke faruwa dakyar yabude baki yace" zeenatu abbuh, ina matata tashiga? " abbuh ne yace alhamdulilah tareda yin sujudu shukur, yace komae yayi farko zeyi karshe kayi hakuri kaji?gobe da safe zamuyi magana ka kwanta kayi barci, ammi tace" ba lokacin barci bane yanzu lokacin amsar addua ne kayi shiru hakanan katashi kayi alwala kazo kayi sallah ka roki Allah ya yaye maka damuwarka, kada kai kawae yayi kamar wani agamar lizard tareda tashi yashiga toilet kamar wanda kwae yafashewa a ciki.........
💦💦WACECE ITA?💦💦 *page 27* *na ummu zaid*👌🏽 Zee wae yau lafianki kuwa tundazu nake rokonki kiyi wanka mutafi gida kinki, zee takalli luby tace" sister wlh jikina ne yasaki babu dadi ga faduwar gaba dana tashi da'eta, luby tace kiyi hkr zee kidinga fadin la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu mina zaleemin Allah zemiki saukin koma menene kitashi kisaka kaya mutafi ga bawan Allah can maryam tashiryashi kinjiko? To ta amsa sannan ta tashi ta shirya bawata kwalliya tayiba yar hoda tadan mutssika tareda wet lip tayi head wrap dinta na turban don lace suka dinka maroon da prussian blue sunyi kyau sosae, tayafa gyalenta maroon se haskawa kawae takeyi gwanin ban shaawa,luby takalleta tareda fadin "tabarakallahu ahsanal kaliqeen, wlh banga laifin zaid daya rude kanki ba zeenatu", zee tayi murmushi tareda jefawa luby purse din hannunta takauce dasauri tana dariya, ahaka suka fito kowa seyaba kwalliyarsu yakeyi.
Abangaren muqaddas kuwa dakyar yashirya kasancewar suraj sekiransa yakeyi daga daurin aure zasuyi reception muqaddas abokinsa ne sosae bussiness yahadasu, kamar wanda zaama dole ya murza hula tareda daura agogon quartz yasaka nubella shoe dinsa iya kyau yayi kyau dan dinkin babbar riga anko sukayida suraj din kalar kowa daban, makullin motarsa yadauka kirar ford fara tas, yafito dan tafiya daurin auren, a babban masallacin nan na banu commasie jamaa da dama suka halarci daurin auren yammatan abbuh daga nan su muqaddas suka wuce reception dinsu, komae ya kayatar kwarae dagaske, suraj yacema muqaddas "guy how fa? Zamu wuce gidan ne tukun kaga kayan dana dinka kazaba min wanda yakamata ko? " Muqadas ya amshe" nifa banason salo dacan wake zaba maka kayan, yanzufa ni surukinka ne atoh", dakyar dae suraj ya lallaba muqaddas yabishi gida amma badan ranshy naso ba ya yarda.... ..... Bawan Allah ne yafito waje yana wasa a kofar gida, daedae lokacin dasu muqaddas sukayi parking a harabar tsakar gidan kasancewar gidan nada girma sosae, zaid ne yafara hango vawan Alllah seda gabanshi yadan fadi don yaron yamasa kama da nuwaera sosae, suraj yace "mekuma kake kallone? Nuna masa yaron yayi yace" that boy yamin kama da nuwaera" shidae suraj ko kallon wajen beyiba yashige dakinsa tareda fadin inka gama kallonsa ka shigo, yafito shi yayi da hannu alamar yataho,shidae yaron yashiga ransa sosae, dagudu bawan Allah yataho yacemasa, " uncle" muqaddas yarike masa hannu tareda fadin yasunanka, bashi amsa yayida sunana bawan Allah, abin bakaramin bama Muqadas dariya yayiba shiga dashi dakin yayi shiko yaro se surutu yakeyi yana biye masa.
Zee ke tambayar maryam kanwar luby wae bakiga bawan Allah bane? Maryam ta amsa da a'a ,nan da nan hankalin zee yatashi don ba dakin dabataje nemosa ba bayanan, dan hakane tayi tunanin fita waje nemansa, hanyar bq tafara dubawa nan ta hango takalmin bawan Allah, don haka tasoma kiransa my baby! Bawan Allah! Ahaka ta zo dakin suraj inda taji muryar bawan Allah nata zuba surutu, sallama tayi a kofar dakin wanda ya haddasawa muqaddas faduwar gaba ko amafarki yaji muryar nan bazae manta da ita ba, bawan Allah najin muryar ta yafito dagudu tareda fadin mummy, "kaniyarka bana hanaka yawo ba,bawan Allah, oya wucemin muje" muqaddas neyafito dasauri tareda fadin zeena! Juyowa tayi taga dream guy dinta ne wanda mamakin yanda akai yasanta yasata yin mutuwar tsaye, ahankali kamar wanda yakejin tsoronta yatako zuwa gareta, " my love nine zaid mijinki, baki ganenibane?, kur takura masa idanu tanason ta tuno wani abu gameda shi wanda sam bata tunaba, gabanta ne ke faduwa tareda saurin niyyar barin wajen, suraj dake daki ne yafito jin maganar da muqaddas din kamar almara, dasauri muqaddas yarike ma zeena hannu yayinda suraj ke tambayar lpy? Kallonta yayi "please kada kitafi kibarni kada ki karamin nisa, kitaymakeni", bawan Allah kuwa ganin halin da mummynsa ke ciki yasa yaron rungume kafar mummynsa kamar zaa rabasu, kuka zee tafara yayinda muqaddas yarike mata hannu katakam, suraj yasaka baki friend lpynka kalau kuwa? Kasaketa mana dont be so foolish! Muqaddas yadago da rinannun idanuwansa dasuka kada sukayi ja kamar wuta yace" she is my wife! I wont let her go,she must follow me home! Ganin rigimar tayi yawane yasanya suraj kiran wayar luby, hello sis please hurry and meet me at boys quarters its urgent, sannan yakafa tagumi yana kallon ikon Allah, zee kuka takeyi tana rokonsa yasaketa shikuwa kare rirriketa yakeyi yazaman musu tamkar mahaukaci sabon kamu, luby takaraso a kagauce ganin abinda ke faruwa da abinda Muqadas keta fadi "matatace! Luby takarasa wajen muqaddas tace, please brother kasaketa she is confused, kayi hakuri let us settle dis issue right now, dakyar da magiya muqaddas ya saketa sannan tafada jikin luby tareda fashewa da kuka, yaronta na tayata mummy kidaena kuka inna girma zanma uncle duka shima yayi kuka, kallon zee yayi yace" wannan yarona ne ko zeenatu? I feel it jinina ne dakika tafi da cikinsa, please answer my question" luby tace please brother allow her kadaena tada mata hankali abi komae a sannu, kakira family dinka semuje gidan gaba daya muji meke faruwa, se sannan muqaddas yayi tunanin kiran gida dan yangidansu zee ma sunzo ma su muqaddas biki, dakyar ya lalubo aljihunsa ya ciro wayarshi,daga dayan bangaren aka dauka hello kana inane muqaddas ga surukanka nason kugaysa yanzu nake shirin kiranka, murya a shake yace abbuh zeenatu, abbu cikeda fargaba ya amsa, meyafaru da zeenatun tell me, sake fadin yake naganata abbuh naganta she is right here by my side, abbuh jiki na rawa yace alhamdulilah, kana ina ne, muqaddas yace ina gidan su suraj, abbuh yace ok wait yanzu zan aiko haseen yadauko ka, yace no abbuh yanzu zamuzo. Toh wasa farin girki,koyaya zeenatu zata hadu da iyayenta, ya labarin mardiyya intaji anga zeenatu? Just follow me the chronicle has just begun.....

YOU ARE READING
WACECE ITA??
Spiritualta wayi gari ne da hayhuwar yaron daba tasan wanene ubanshi ba, kwatakwata kwatakwata bata iya tuna ryuwar da tayi abaya, tirkashi littafin wacece ita littafine daya kunshi soyayya, rudani, tashin hankali dakuma tausayi, kubiyoni dan jin wannan kaya...