💦💦WACECE ITA? 💦💦 *page 34*
*na ummu zaid👌🏽👌🏽
*vote before readingZaune take a farfajiar anorld hotel, bakin glass tasaka, yayinda jefi jefi take dago kai takalli mutanen dasuke filin hotel din yawanci yammata ne da samari suke sharholiyarsu hankalinta kacokam ta maidashi kan laptop dinta tana aiki ne, muqaddas ne tundaga nesa yake hangota tana masa gizo, "kai it cant be wannan ba zee din dana sani bace,waccen bata kai haka haduwa ba da kyau", haka yayita sake sake zuciarsa na ingizashi kan ya matso yaganta dakyau, ahankali yataso daga kujerar dayake zaune tareda nufo zee wacce kwata kwata hankalinta tamika shi kacokam kan system dinta ne, matsowar dayayi ne yahaddasa masa faduwar gaba ko a mafarki bazae mance fuskarta ba duk kuwa da canzawar datayi takara kyau takara haske, fatarta kamar ta jaririae sumul sumul, zeenatun shi ce, masoyiyarshi, dakyar ya ari dauriya ya yafa tareda fadin "excuse me madam"jin muryar wanda bata zata bane ba zato tadago kanta dasauri tareda kuramasa ido, almost 7 years bata sakashi a idonta ba, yacanza yakara murdewa yanzu har wata yar kasumba ya ajiye ya girma sosae hakan kuwa bakaramin kara mata kyau yayi ba, ahankali muqaddas ya jawo kujerar dake facing dinta yazauna"may i sit here? "kallonsa kawae takeyi kamar moron,ahankali shima yafara tuna irin soyayyar su ta da komae nadawo masa sabo dal, "meyasa narabu da wannan cute damsel din" tamvayar kansa yakeyi, cikeda kasaita yadauki tumbler din dake gaban zee na chapman yayi sipping yana cigaba dakare mata kallo, komae nata ya canza tayi girma ta kara kyau fiyeda zatonsa, madam ba gaysuwa? Kallonsa tayi da niyyar gayshesa ta tuna irin betraying dinta dayayi don hakane yasa ta tsuke fuska tareda cire glasses din dake idonta ta mannashi a saman goshinta datayi turban headwrap, idanuwanta masu kama da zaiba tar a kansa, hakan bakaramin kara haddasa ma muqaddas shaukin so yayi ba, lumshe ido yayi tareda budewa,yakara kallon idonta, ahankali yayi whispering 'i love dos eyes"cikeda masifa zee ta tashi tafara hada kayanta don yanzu bakaramin haushinsa takeji ba, ji takeyi kamar yanzu ne yayi mata abinda yamata, shima tashi yayi dasauri "please zee ki saurereni kiji uzurina wlh i still loves u kiyi hakuri dan Allah" kallonsa tayi tareda kallon hannunsa daya rike mata jaka ta daka masa tsawa"please let go of me" kai wani irin kidahumin mutum ne,a ina kasanni dazaka kama min magana kasake ni kona shayar dakai ruwan mamaki, ba zee din dakasani da bace yanzu wannan ba yarinya bace yar 17years, am a grown woman,u cant fool me anymore, ganin dagaske takeyi don har wasu a wurin attention dinsu yafara zuwa kansu yasa dasauri yasaketa, "i will get you zee wanan masifar dakike min nasan kinasona haryanzu, ni kike jira zee u cant lie to me, naga soyayyata acikin idonki" tsaki taja sosae tareda galla masa harara binta yayi da kallo ganin yanda take tafiya dasauri duk tsinin takalmin kafarta ko damuwa batayi ba har tashige reception din hotel din, ajiyar zucia yasaki me karfi tareda zama shabar kamar kayan wanki, "zeena i love u i promise u bazan barki ba i will marry you" tunani yashiga yi yanda zae bullowa alamaryn tareda mamakin abinda yakawota Sydney yasan dai in karatu ne yaci tagama shi tun 4years back,rufe ido yayi tareda shaqar kamshin turarenta kamar haryanzu tana wajen.
Tunda muqaddas yalura kullum zee sae tafita hakan yasa yake binta duk inda zata saedae taga ya bude taxi yashigo,kuma koda zata shiga taxi dari sae yashiga, ahaka muqaddas yalura cewa bussiness takeyi don har mamakin yanda akayi tasan manyan boutique da industries yakeyi, yau ma tsaye take a bakin hotel din anorld tana jiran taxi, harta hau bata ga muqaddas yabiyota ba, se tasami kanta da rashin jin dadin haka, saboda tana enjoying duk wani magiya da shagwabar dayake mata, wani zubin ko bata da commitment dan kawae yabita take hawa taxi, tsaki tayi sannan tacema driver yakaita amusement park, haka har sati bata ga muqaddas ba wanda bakaramin shiga damuwa tayi ba, tokodae yakoma Nigeria,tambayar kanta tayi wanda a take gabanta ya fadi, No insha Allah betafi ba. Akwanakin nan da zee tayi bata ganshi ba tashiga damuwa duk ta rame kamar ba ita ba,sydney din ma ta isheta kwata kwata don harta sa ran yakoma gidane, yauma zaune take a filin hotel din ta kafa tagumi tunaninsa kawae takeyi don har murmushi taKe inta tuna drama dinsu, hello babe, missing me?firgigit ta dawo hankalinta tareda saurin dago kanta takallesa, watau ita tana nan tunaninsa na addabrta shi har wani kiba yakara, haushin kanta ne yakamata, zucia vata da kashi, zama yayi tareda kura mata idanu ko kiftawa bayayi, babe kiyi hakuri lalurar aikina ce ta tsaida ni baki ganni ba two days,i miss u so much yaushe zaki daena hana zuciarki abinda takeso,in punishment ne wlh nayi nadama, zee kimin uzuri i love u, kuma i promise u bazan kara barin hannunki ba,ina tareda ke, ajiyar zucia zee tasake don tabbas inta bari damarta ta subuce mata zata yi nadama, balle yabata hakuri,ta gwada shi ta hanyoyi da dama, ganin shirun datayine yau bata masa maseefar tata data saba bane yasashi cigaba da fallasa mata asirin zuciarsa, kunsan namiji da iya tsari nan da nan zee ta afka cikin tsarin nasa, ahaka tasaki rai tafara biyemasa be barta takoma daki ba saeda ya tabbatar ya kulleta da soyayyarsa tamau,sosae suka shirya tundaga ranar wata orin soyayya ta kullu a zuciarsu kamar kada su rabu kullum suna tare duk wani guri na shaqatawa ko najin dadi dae duk ba inda basa zuwa.
WACECE ITA?
*PAGE 35*
*NA UMMU ZAYD*
Zeena wace irin maganace kikeyi haka, kirasa wanda kike kulawa sae mutumin daya yaudareki a farko gaskia nikam ban amince ba indae har shawara kike nema a wajena, zeena wacce ke sauraren yayanta tayi shiru,hello kinajina zee zee ta ja numfashi tareda fadin bro haseen naji amma wlh yayi nadama, dogon tsaki yaja kamar ya janyo zeena daga cikin wayar yamata dan banzan duka, ina neman miki mutuncinki kina wani kareshi shikenan tunda baki da zucia, don haryafi zeena jin zafin abinda muqaddas yamata saboda ba karamin so yakema kanwar tasa ba, kit ya kashe waya, yayinda zee tabi wayar da kallo tana jinjina daukar zafin da haseen yayi, kwanciya ta kuma gyarawa tareda kurawa silin din dakin ido tashiga tunani....
My baby yau fa saura kwana uku na koma nigeria don mun gama course din daaka turomu, zee takalle muq cikeda shaukin so tace Allah ya nuna mana jibin lafia, kallonta yakuma yi yace:babe naga kamar akwae abinda ke damunki a ranki please ki fada min ko mennene in dae baefi karfina ba zanmiki maganinshi insha Allah,zee ta furzar da yar iskar dake bakinta tareda kau da kai gefe daya"yaya muq akwae matsala, a zabure ya gyara zama a kujerar dayake tareda fadin"oh no! Wace irin matsalace wannan sweedy please Allah yasa dae basu ummi bane suka ki amincewa da auren mu, girgiza masa kai tayi tareda fadin yaya haseen ne haryanzu yana jin zafin abinda kamana, kuma yanda nakeson yayana zan iya hakuri dakai don na faranta masa rae muq. Cikeda fargaba muq ya dafa goshinsa sae yanzu ya tuna da aminin nasa haseen innalillahi wainna ilahi rajoun, wats wrong with me haka, zee kiyi hakauri just give me ur support insha Allah dana isa nija zan sasanta dashi nasan ban kyauta ba fushi yakeyi dani but anya zee yanzu sae ki iya rabuwa dani?son nawa dakike fadi kinayi yakai so kuwa? "kauda kanta gefe tayi don ita kanta ta san bazata iya rabuwa da muqaddas dinta for the second time ba, a hankali tayi magana muq is time to go dare yafara shiga we shall talk indae ka sasanta da frnd dinka nasan ummi da abba ba matsala bane don haryanzu abba nasonka. Mikewa tayi batareda ta kara waewayarsa ba tashige cikin hotel din. Furzar da iska muq yay me zafi kamin ya tashi yatare taxi duk a rude yake don gaskiya he cant resist loosing his damsel for the second time, zaeyi duk yanda zaeyi yashawo kan haseen don yasan zee da haseen sarae yanda suke kaunar juna zataiya jure hakurin rasashi saboda bro dinta. Muqaddas yana zaune yaji wani abu ya tsirga masa tundaga kanshi har yatsun kafarsa, innalillahi ya fadi tareda dafa kirji kamar wanda ya tashi a mafarki ya ji yana kiran ummi da abbu, hasbunallahu ni meke damuna haka cikeda tashin hanakli ya janyo wayarsa tareda dialling number din ummi saeda yamata 20 missed call bata amsa ba, yajuya yakira abbuh shima d same yaki dauka ammi yayi saurin dialling number dinta don yasan ita kam bazatayi fushi da shiba, itama har 10 missed call ba respond haka yayita kiran numbers din yan gidansu aka rasa me dauka, hankalinsa inyayi dubu yatashi cikeda damuwa, yafara hada kayansa don kam yana sauka yau airprt zekara booking jirgin kt yasan tabbas yama iyayensa laifi ba kadan ba, ko zuwa sallamar dayayi niyyar ma zee beyi ba ya wuce airport sae kiranta yayi yamata bayani, fatan alhery tamasa duk da bataji dadin rashin haduwar tasu ba.har jirginsu ya cika yayinda yake ganin rashin saurin jirgin nasu sae tsaki yake ja akai kai, 6hours sukayi a jirgi sannan suka isa airport din murtala muq hankali tashe don baabu abinda ya tsana irin fushin iyayensa booking flight yayi na kt wanda aka cemasa sae 6pm zasu tafi haka yayi jiran 7hours ko yunwa bayaji sabda tsabar tashin hankali, 1hr ne kawae yakaisu kt,yana sauka yatare taxi yakaishi gidan su lokacin ana kiran sallar ishai, a bakin gate din gidansu yatasaya yabiya dan taxi kudinsa sannan yashiga gidan lokacin abbuh nashirin tafia masallaci kallonsa kawae yayi ya dauke kansa kamar be ganshi ba,jikin muq yakara yin sanyi kalau, lallae abbunsa yayi fushi ssae dashi.
Dakin ummi yafara zuwa wanda tunda yayi sallama bata amsa ba asali ma bata kuma kallon inda yakeba, gwiwa a sake ya ajiye jakar da ke hannunsa tareda gurfanawa akasa bisa gwiwoyjnsa ummi dan Allah kiyafemin,ummi tausayin danta yakamata don tasan ba laefinsa bane nan danan ta yafe masa, haka ma abbuh bayan yadawo yayi kiran muqq din yayi masa fada karshe yakara da naseeha tareda nuna masa illar wofintar da iyaye sosae jikinsa yayi sanyi ya dada bama abbuh hakuri karshe suka cigaba da hirarsu anan muq ke sanarwa abbuh mgnr zee jinjina kai abbu yayi yace:toh Alhamdulilah naji dadin jin mgnar nan dan lokacine daya kamata kayi aure saboda sam bakai saar mace ba inafatan wannan din tazemaka alhery tashi ka tafi ka kwanta tunda gobe zaka kama hanya zanyi mgna da iyayenka mata tukunna, muqaddas yayi godia sannan yamike don shirin barci. Sosae su ammi sukai murna dama can sunfi masa raayin zee din don dae yakine. Bayan muqaddas yakoma abuja da sati biyu abbuh ya wakilta yanuwansa zuwa lagos don neman auren zee wanda general ba tareda bata lokaci ba ya amince don sanin wanene muqaddas din dakuma burin ganin cewa yarsu tadawo gida an tsaeda biki wata shidda kacal, inda sae da komae ya kammala general ke sanar da ummie wacce sosae ranta ya baci amma ya ta iya tunda yariga yabada, biki na saura wata biyu zee ta tattaro ta dawo gida nija dukda bata fasa harkokinta sosae kudi ke shigo mata batada matsala indae ta wannam fannin ne.
.

YOU ARE READING
WACECE ITA??
Spiritualta wayi gari ne da hayhuwar yaron daba tasan wanene ubanshi ba, kwatakwata kwatakwata bata iya tuna ryuwar da tayi abaya, tirkashi littafin wacece ita littafine daya kunshi soyayya, rudani, tashin hankali dakuma tausayi, kubiyoni dan jin wannan kaya...