WACECE ITA?
NA UMMU ZAYD
VOTE AND COMMENT PLEASE
A kwana a tashi har cikina yakae wata 8 lokacinne kuma duk yanda naso boye cikina kwata kwata bana iya boyewa, kullum ina cikin hijab da jacket nayi wani irin haske fauu kamar bani ba, zaune nake a kasan carpet ina goge undies din mardiyya don ITA harta undies sae na goge mata, falon tashigo ta zauna kan one seater tareda Mike kafa daya kan daya, ta kunna tashar zeeworld inda suke wani film kindred heart, guga ta na cigaba dayi Wanda Sam bansan mardiyya ni take kallo ba jin danayi tace "ke!" Yasanya ni dago kaina dasauri tareda naji want irin faduwar gaba, cigaba tayi da fadin "tashi tsaye" dasauri cikeda tsoro na mike Wanda hakan yasanya ta Kare min kallo gabana na faduwa"lailayo ashar tayi"kan ubara uban nan, kina nufin cikin nan naki be zube ba?"wace irin Sha Sha ce ni da har cikinki yakae watannin Nan ban lura ba?"nidae jikina rawa kawae yakeyi ina jiran ikon Allah da agajinsa,dasauri ta mike tareda kwada min wani gigitaccen marin dayasani daina gani na wasu yan sakanni, "wallahi wallahi nafada maki inhar naga ciki a tareda ke abinda zae biyo baya bamae Dadi bane,kin taro tashin hankali da baza ki iya tsame kanki ciki ba.......fuuu ta yi hanyar bedroom dinta.
Daga tsaye na fada kan kujera kamar an jefa kayan wanki,"innalilahi wainna ilaihi rajiun, Allahumma ajirni fi museebaty, wannan wani irin maseefa ce da balai, dakyar na iya zare socket din iron din na Koma dakina don nema ma kaina mafitar abinda zanyi
"I have to try and tell my family about my issue I can't bear to loose my baby, da gatana da komae a dunia Amma nazama wata iri" nikadae nake ta samvatuna kamar mahaukaciya,dialling number din bro haseen nayi Wanda ringing biyu yadauka, "hello sis how fa?" Amsa masa da "am ok nayi nafara korafi akan rashin zuwan da vasayi wajena, hakuri yayita bani sannan ya jefo min tamabaya" fatan dae lafia ko?" Shiru nayi na Dan sakanni ina kokarin karfafa zuciata akan fadin abinda ke damuna,saeda Yakuma cewa hello tukuna na dawo hayyacina, samun kaina nayi dafada masa" I was pregnant Bros" wani Kara ya saki cikin wayar har saeda na cire kunnena daga wayar sannan yacigaba, I was so excited dear sister, nakusa samun baby, how many months saboda na Fara shiri, Bashi amsa nayi da eight month Bros,dif yayi shiru wuta ta daukemai he knows his sister she cannot get pregnant for good eight month without telling him, kasa yayi da murya yacigaba" lady can you tell me why you didn't tell anyone about your pregnancy?samun kaina nayi da fashewa da kuka,Bros akwae issues am scared to loose my baby, shiyasa na kasa fadawa kowa, daga daya bangaren yace" wait! how? I don't understand you,ki min bayani is something wrong?" Girgiza masa Kai nayi kamr Yana gabana, na bude baki da niyyar fada masa matsalata naji an daure min jijiyoyin harshe na Kam ko iya daga baki banayi, wani irin kuka na fashe dashi tareda cutting call din. Kira na yayita yi daga nashi bangaren Amma Sam nakasa dagawa karshe na kashe wayata don banga amfanin barinta kunne ba.

YOU ARE READING
WACECE ITA??
Spiritualta wayi gari ne da hayhuwar yaron daba tasan wanene ubanshi ba, kwatakwata kwatakwata bata iya tuna ryuwar da tayi abaya, tirkashi littafin wacece ita littafine daya kunshi soyayya, rudani, tashin hankali dakuma tausayi, kubiyoni dan jin wannan kaya...