WACECE ITA?
NA UMMU ZAYD.
Hello Happy jumuat my wattpadians da fatan zaayi jumua cikin koshin lapiya, inshallah Allah littafin Wacece ita zae Kare a chapter nagaba.
Meanwhile, don't forget to vote and comment.A gurguje.
Alamaryn duniya ya tsananta ga mardiyya, kwata kwata zuciarta ta Gaza sukuni ko kadan,ba irin tashin hankalin dabata gani, ita batan kawarta sholly yafi komae daga Mata hankali, tana cikin taraddadin mutuwar karkuzu ga kuma batan shollyn dazata Mata hanya zuwa wani wajen, komae ya kwance Mata muqaddas ya balain canza Mata Bata iya controlling dinsa.
Komae bae Kara firgitata ba saeda ta ga muqaddas da bakin fuskar dabata sani ba sunyi dakin mardiyya, saeda suka fito da kayan dakin tas sannan aka kawo sababbi masu matukar daukar hankali aka Sanya Mata,


sosae ta firgice ta rasa natsuwarta, abinda take tunani gameda ganin zeenatun ne ya Kara tabbata, "ina wallahi bazae yiwu ba dole insan matakin dazan dauka", dialling number din kawarta charas tayi inda takara jin tashin hankalin dayafi Wanda take ciki, Jin cewar cheras da sholly tare suka mutu suna kan aikata luwadi da wani alhaji, inda alhajin yayi mugun illatasu harsaeda wani nama yafito ta duburarsu karshe sukayi mutuwar kaskanci gawarsu tayi Baki kirin, da sauri mardiyya ta zari mukullin mota ta fice daga gidan dirrect inda aka Kai su cheras din taje, Koda tayi Ido biyu da su bakaramin tashin hankali ta shiga ba,rasa bakin mgna tayi,idansu a zare ya kafe ga wani irin Baki da gawarsu tayi abin babu kyan gani, dasauri ta yi riverse ta juya zuwa gida jikinta na wani irin tsuma sosae.
Komae na dunia tuni yafice a cikin zuciar mardiyya inda take wani tsoron Allah ya kamata , duk tayi sanyi, rannan wunin ranar a sabule tayishi da ta rufe Ido gawar su sholly kemata gizo.
Shiko Dan mulkin Koda yadawo ya tarar da halin daya ga tanaciki kota kanta bebi ba don ta tarbar amaryashi yakeyi ba ita ba.
Da dare Kamar kullum, don yanzu ya balain kafa Mata dokoki, yazama tsayayyen namiji a gidansa baya daukar wargi ko kadan , mardiyya ce ta zo ta tsugunna agabanshi tareda sunkuyar dakanta kasa, sweet" da gefen Ido ya kalleta Wanda duk kallo guda Kara jin sabuwar tsanarta yakeyi, kullum abinda yafi basa mamaki na yanda akayi ya auri mardiyya yakeyi, duk kyan datake dashi Sam baya burgeshi don shi he was selective ba duk mace ke burgeshi ba komae kyanta, Amma kaddara ta rigayi fata.
Kara Kiran sunansa tayi jikin ta na dada tsuma batareda ta damu ba tafara magna" nasan yanxu babu macen daka tsana kamata a duniyan,nasan nayi abubuwa a duniyan da dama Wanda koni bazan iya yafewa kaina ba ballanta ubangijina, kokuma wadanda na cusgunawa a rayuwata, hakkin mutane dayawa ya Isa yakaini wutar jahannama, baban suhail in nadamar abubuwan Dana aikata abaya Dan Allah ka yafemin sannan inaso na fada maka abubuwan dabaka sani ba gameda mutuwar danka suhail da batan zeenat da komae daya shafeka, Wanda nasan ba lallaene kayafemin ba ballantana wadanda na mawa"
Shiru yayi tare da zuba mata jajayen idanunsa a kanta Jin ta ambaci mutuwar danshi daya ke matukar so a rayuwarsa.
Kara nisawa tayi tareda zayyana Masa duk abubuwan data aikata Wanda tsabar kaduwa yasa muqaddas ya ji gaba daya wuta ta daukemasa jijiyoyin wuyarsa dakansa sun mike tsaye tsabar tashin hanakali, Ashe a duniaya akwae mutane marasa imani Kamar su mardiyya?
Innalilahi wainna ilaihi rajiun kawae yake Fadi haryasamu abubuwan dayake ji suka soma lafa Masa, lallae ya yarda mace tafi shaidan iya kaidi,
Dakyar ya iya tattaro Dan ragowar miyan bakinsa yafara magna" mardiyya bansan abinda zan cema ki ba bansan irin tsinuwar dazan maki ba, Amma kije na barki da ubangiji shikadae zaemana sakayya kodan jinin dakika kashe na bawan Allah da baetaba yima ubangijinsa laifi ba ,Allah ya isa tsakanin dake,Allah ya cigaba damin sakayya,kije nasakeki saki uku!! zama dake tamkar wata annoba ce wacce Bata da ranar karewa,hakkinmu kawae ya isheki rashin zama lafiya har abada!" Daki ya shige dasauri don a yanda yakejin zafi a ransa zae iya ma mardiyya mugun dukan dazae kaeta kushewarta.
YOU ARE READING
WACECE ITA??
Espiritualta wayi gari ne da hayhuwar yaron daba tasan wanene ubanshi ba, kwatakwata kwatakwata bata iya tuna ryuwar da tayi abaya, tirkashi littafin wacece ita littafine daya kunshi soyayya, rudani, tashin hankali dakuma tausayi, kubiyoni dan jin wannan kaya...