CHAPTER SIXTEEN

1.5K 110 6
                                    

*💦WACECE ITA?💦*
*PAGE 38*
*NA UMMU ZAYD

Vote and comment,ku faranta min kamar yanda nake faranta muku,ghost readers we would sion fish you out ehe!
.

Tun da farar safiya mardiyya ta tashi abin da bata saba ba sam amma yau saboda tsabar mugunta yasanya ta tashi don ko suhail inzae tafi school nanny ke masa komae kwata kwata babu Shakuwa tsakaninsu, parlourn ta taradda nanyn suhail din tana shiryashi yayinda yar yarinyar ta gaydata ta amsa dakyar sannan ko bi takan danta batay ba ta yi wucewarta dakin zee wacce bayan tayi asuba barci yayi awon gaba da. Kara daure fuska tayi tareda banko kofar dakin, daka mata duka tayi a cinya wanda yasa zee tashi a tsananin firgice, tana kallon mardiyya, kasan ranta wani bacin raene ya taso mata how could she? Amma kuma saeta sami kanta dakasa ma mardiyya komae illa gaysheta da tayi ina kwana aunty, mardiyya ta lailayo ashar tace"uban me kikeyi hakada har zaki kwanta shame shame kina barcin asara! Hala vakisan aikin ki a gidan nan bane, cikeda mamaki zee take kallon mardiyya saukowa tayi tareda bata hakuri, mardiyya tace:ki biyoni main parlour kisameni, tareda juyawa zee ta sauko daga gadonta tareda shiga bayi tayi brush sanan ta nufi main parlourn inda ta taradda mardiyyar ta daura kafa daya kan daya sae girgizawa take ita ala dole ga oga, dan rusunawa zee tayi tareda fadin"gani aunty"mardiyya ce ta kwala ma nanny din suhail kira, sailuba! Yarinyar da sauri ta amsa tareda fitowa don amsa kiran uwargidan nata, yauwa sailuba daga yau na koreki aiki ki tattara kayanki jibi amaidaki garin ku, sailuba ta dago dasauri hankalinta tashe"aunty dan Allah wani laifin nayine haka? In laifi na maki kiyi hakuri ki yafemin wlh zan gyara dan aikin nan dashi na dogara dashi nake taymakawa kaina da iyayena inkika koreni bansan yazanyi ba"mardiy ta katse sailuba"look nanny nifa baki min komae ba wanann shine decission din danaga damar yankewa a cikin gidana, zan taymaka nabaki jarinda zakije ki kama sanaa shima dan kinci albarkacin yarona dakike kularmin dashine tashi ki tafi daga yau zuwa gobe kifara hada kayanki, sailuba cikeda tashin hankalin ta mike da kyar dan har wani jiri take gani dan tasan kozatayi kukan jini mardiyya ba tausaya mata zatay ba, kallon zee tayi wacce ke tsugune tana kara mamakin mugun halin mardiyyar"kekuma nadawo gareki kinga na kore yar aikin yarona na daga yau duk abinda ake masa ke zakiyi taking over yimasa wanka kaishi school, sashi barci ke duk abinda kikasan yaro na bukata ke ce zaki masa, sannan daga yau zaki fara gjrki a gidan nan both breakfast lunch and dinner, kinajina ko, zee dasauri ta karkada kai alamar taji, mardiyya tasaki wata irin shewa tareda ma kanta kirari, yarinya tunda kika sake kika aure min miji yanzu kika soma fuskantar nauin azaba da musgunawa daga wajena ba ruwana da hutun dakika taso a kai abinda nasani yar aiki na daukeki ba wae kishiya ba keda muq sae gani sae hange daga nesa, ita dae zee shiru tamata, sannan mardiyya ta cigaba yanzu kitashi kifara hada mana breakfast kuma waina nakeso kimin da miyar taushe sannan ki dafa min lipton kuma duk zaki abinci ki tabbatar kin tambayeni na tsara maki abinda zaki girka, maza tashi min, jiki a sanyaye zee ta mike tayi hanyar babban kitchen din gidan, nan da nan tahau aiki kamar jaka tanayi tana wanke wanke abinda ta bata cikin awa uku ta kammala komae yunwa takeji hakan yasa ta zuba waenar a plate tafara ci sisae saeda ta ci takoshi ta jera na oga akan dinning sannan taje tafa da mata ta kare.

haka rayuwar zee takasance a gidan aurenta itada muq ta bakin mardiyyar sae kallo daga nesa, sam komae yadaena mata dadi a duniar nan suhail ne ma inya na nan yake dan dauke mata kewa dukda yaron was very quiet beda hayaniya amma ya saki jiki da zee, kullum insu ummi suka kira saetayi kamar tafada mata sae taji wani abu mai nauyi ya tokare mata harshe haka nan zata hakura takasa fadi ita kadae take hadiyar kukanta ita kadae kwata kwata ta fige ta lalace kamar ba wanann fashionista zee din ba.

Tafia ce takama mardiyya kaduna bikinWata kawarta da duk halin dayane sosaae takeji da bikin dan ba karamin shiri sukayi ba mardiiyaa tayi rawar gani don kudin muq dinne ake kashewaa wajen tsara biki yanda kasan bikin wata diyarta don haka da sasaafe ta kira zee tareda fada mata tafia zatay "ki kula da gida sanan kada ki ga wae ba na nan kice zaku ci amanata wlh bazan yarda ba daga ke harshi sae na gasa maku aya a hannu ki kiyaye dokokina muzauna lpy. Xzeena a ranta tace ni yanzu mijinki ba ya gabana don kwata kwata yagama fice mani a rae, haka mardiyyar ta karace surutunta sannan ta shiga dakinta, zee ta mike tafara gyaran gida kasancwaar yau weekend suhail bazaeje makaranta ba, wajen karfe goma muq da mardiyya suka fito daga daki sae fakaicewa yake yana kallon zeenatu a duk dakika guda sonta karuwa yake a zuciarsa amma gashi da karfi da yaji mardiyya ta raba wannan alakar soyayya tasu, ko kallon gefen dayake batay ba ta cigaba da aikace aikacenta, mardiyya sae da ta karama zee da muq warning sosae sannan ta fito don driver ne zae kaita saboda tsabar doki tun ana saura kwana 7 aka tafi.
Dawowa falon yayi bayan ya raka mardiyya, kallon zee yay wacce ke zaune tana cin abincinta,, duk tayi baki ta rame, wani irin tausayinta ne ya rufesa duk ni najawo maki zee ki yafemin, baesani ba ashe a fili yayi mgnar tasa, wanda yasa zee kallon sa tareda jefa masa kallon ka raenamin hankali, magana yayi mata"yammata babu gaysuwane? "ko kallonsa batay ba don yanzu ba karamin haushi yake bata ba sosae da sosae, saeda ta gama cin abincinta ta mike tsam tashiga kitchen tareda wanke hannu ta wuce dakinta dasauri kuwa muq yabi bayanta, tsawa ta daka "ficemin daga dakina muq,!! Ba abinda zaka iya cemin wlh nayi da nasanin Saka rayuwata cikin taka, sosae ta ke fada masa mganganu marasa dadi wanda ko kadan bega laifinta va don yasan she was really hurt, taku kadan yay ya cimmata inda yayi kokarin matse ta sosae a jikinsa wanda hakan yasata fashewa da kuka mecin rae,taping bayanta yake yana bata hkr, am sorry baby kitausayamin ki tausayawa rayuwata tabbas da inada abinda zanyi da zan iya don sama mana mafita, nikaena narasa yanda zanyi nayi maganin balain da matata ta samu a ciki is not my fault, sosae zee tayi shiru tana sauraronsa tabbas gaskia yafada wani namijine hakanan babu wani dalili zae zauna mace na juyasa Kamar waenar safe hka? Ita kanta kullum kokarin fighting abnda ke zuciarta takeyi don ganin ta kwato ma kanta yanci wajen mardiia amma sam haka yaki yiwuwa, tausayinsu ne ya kamata hakan yasa tayi shiru tana ajiyar numfashi a jikinsa, cigaba yay da kwantar mata da hankali hakan kuwa yasa taji natsuwa na shigarta sosae don dama bata iya fushi da muq yanzu ma abin takasa controlling dinsa ne kawae, tuni wani barci yayi awon gaba da ita sosae muq yaji dadi sannan yadan kwantar da ita gefen gadon shima yasami kusa da ita ya kwanta, suhayl ne ya shigo dakin dagudu yafada kan zeena, "aunty i want to eat food" bude idanta tayi dayay nauyi don barcin yamata dadi ta tashi da kyar, kallon inda dadynsa yake yay, aunty me daddy yakeyi a nan,? Janyo shi tayi jikinta don tasan suhail akwae wayau tace"ur daddy is sick shiyasa yay barci anan kaga kuma mumynka bata nan"daga kai yay tareda janyo hannunta suka fito parlour ta hada masa tea sannan ta zuba masa doya da kwae da tayi da safen yanaci yana kallonta wacce sam batamasan tashiga wata duniar ta tunani ba"aunty is it mummy, kiyi hakuri inna girma zan rama maki mummy was very wicked, kallon yaron tayi tareda fadin kul suhail kada na kara jin kace haka mummynka ne inkayi sallah kadinga adduar Allah ya shirye mumynka kaji kada na sake jin haka, oya say sorry,kamar yaron zaeyi kuka yace am sorry aunty, sanan tacigaba da kallon sa, sosae take jin yaron a ranta dukda uwar dan ba kaunaarta takeyi ba, jinin mijinta ne muq din ta, sae wajen karfe goma na safia nnan muqaddas ya tashi breakfast takaima sa daki yaci sanan ya shiga wanka, bayan yafitone yake fada mata yakamata su shirya zasuje lagos don tun waccen satin abbuh yamasa mgna yakamata yaje godia amma tsoron mardiyya yahanasa tafiar tunda yanzu oga vata nan zaeyi amfani da wannan dama tashi ya tafi, zee cikeda murna ta kallesa tareda fadin yaushe zamu tafi yace"probably in munsami flight yau zamu tafi amma kwana daya kawae, batareda bata lokaci ba zee ta amince don yanzu burinta be wuce ace taganta jikin umminta ba, tafada mata damuwarta ko zata bata shawarwari da mafita, wajen karfe 4 na yamma suka isa airport gwanin ban shaawa sae suka fito a amarya da angon sak dukda ba wani kwalliya zee tayi ba tayi kyau sosae dukda ramar da tayi tai duhu.

Kasancewar ummi ta san dazuwansu don zee ta kira tafada mata tun safe yasa koda sukaje an hada masu abinci sallah kawae sukayi suka ci abinci muq bayan ya gaysa da abbu ne yayi mae godia sanan yayi sallama dashi akan zaeje masauki ya kwana abbuh yace haba muqaddas sae kace ba dan gida ba a da ina kake kwana inkazo wajen haseen, ni kam a dana na daukeka ba suruki ba don haka ga dakin baki nan nasan ummi tasa an gyara maka, godia yayi masa sannan ya mike yashige dakin tunda gidan ba bakonsa bane. 
Zeena kuwa ummi ce ta kalleta tareda fadin"daughter naga kin rame Allah yasa lapia ke ana aure ana murmurrwa kina ramewa meke faruwa"zee ta dan kwakulo murmushi tun dazu take son sanar da ummi halin dasuke ciki ita da muq amma kwata kwata takasa sae ta bude baki zatae mgn sae taji tana fadan abinda ba shi takeso ta fadi ba, hakanan tana ji tana gani ta hakura da mgnar, don haka yaznu ma da ummi ta tambayeta murmushi kawae tayi tace"wlh ba komae ummi lpy lau muke zaune babu abinda ke damuna, ummi ta jinjina kai don haka sae ta dauka ko zeenatun tasami cikine. A ranta tana farinciki inhar tunaninta yazama gaskia.

Washe gari da yamma likis jirgin dasukayi booking zae tashi tunda yamma zee take jin wani faduwar gaba don ji yake kamar kada su tafi shikanshi suhail bayaso atafi don sosae ummi ta jashi a jiki don wajenta ya kwana. Amma ya suka iya sallama tayi ma gidan nasu sannan abbuh yasa driver yakaisu tasha zee sae share kwalla takeyi kukan da batayi ba da aurenta yanzu shi takeyi.😂
Suna isa zee ta daura masu indomie suka ci sanann tama suhail wanka ta sashi barci, sae da ta tofeshi da addua sannan tafito daga dakin yaron, dakin ta tashiga ta watsa ruwa tay alwala tareda kabbara sallar ishai tahada da shafai da wutiri, don tasaba yinsu kullum, tana kan darduma muqaddas  yashigo dakin shima cikin shirin kayan barcinsa sae wani murmushi yakeyi don jinsa yakeyi ango sak zee ta kallesa tace hala ko kamanta da sharaddin da matarka ta gindaya mana, nikam gaskia banason tashin hankali kawae katashi katafi dakinka saeda safe, kamar zaeti kuka ya matso kusa da ita please my zee dont say dat kinsan ina sonki mardiyya bata isa tamana abinda Allah bemana va, kidaure muji dadin zaman mu i really miss u so much bae, saosae ya kashe mata jikin wanda shirun da tayi ne yasa yacigaba da watso mata tattausan lafazi masu sanyaya ran duk wani masoyi, ganin danayi abin nasu yasoma canza salo ne yasa ni rufe masu kofa tareda arcewa kaduna don kaima mardiyya rahoton kanun labarae....😂😂😝

WACECE ITA?? Where stories live. Discover now