BAYAN WUYA part 1

4.4K 160 5
                                    

🌷🌷 *BAYAN WUYA*...... 🌷🌷NA AU FANA
                       🌷

*(it torchs the herts of the readers based on true life story)*

     *writing - by*
             *ameenart Umar fana (AUFANA)*

        *DEDICATED TO UMMUN MEENAL*
*momcy kedin ta daban ce shiyasa nake na daban ne gashinan ki shoshale Abunki Sai yanda kika ga dama dashi saboda naki salon na daban ne I love you lovy lovy*😘😍

*BAZAN TABA MANTAWA DAKU BA KUNA RAINA KUDIN NA DABANNE MUNA ROKON ALLAH YA KARE MUNA KU DAGA SHARRIN DUK WANI ABUN SHARRIN AMEEN*
*aunty Aysha A garkuwa*
*aunty maimounat O, G*
*aunty Zahra surbajo*
*sis ummu Bashir*
*sis cool hafsat*
*sis Badeeyah (beauty Queen)*
*sis Queen hafsy*
*sis Hubbey*
*KU DIN NA DABANNE*😘😍

    *PAGE 1-5*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

*KEBBI CITY*.....
wani gida ne nahango Mai dauke da daki biyu da toilet biyu wata yarinya ce nahango kyakkyawar gaske fara ce amma ba tas ba daga can dayan dakin naji wata murya tana cewa *INTISAR* kiyi hanzari kifita da wuri domin ki dawo da wuri domin kuje islamiyya da wuri Kar mlm ya dake ku

Toh mama ai nakusa kammalawa insha Allah yau koda ban sayar ba zan dawo da wuri domin muje islamiyya saboda nasan halin mlm hussaina bashida sauki wajen duka
Shap2 ta shirya ta dauki kayanta na talla zata fita kenan sainaga wata yarinya kyakkyawa tafito daga dayan dakin wanda nasan nasune na bacci Anty *INTI* zanje don Allah kije dani murmushi *INTISAR*tayi tace little sis kiyi hakuri wata rana kema Zaki fara insha Allah Kinga sauri nake kiyi  hakuri kinji me kike so nasiyo maki idan zan dawo sweet da biskit tace

Murmushi *INTI* tayi tace toh sainadwo kiyi man adduah nasayar gaba dai kin je toh Anty na zanyi ALLAH ya bada saa ameen Mai little sis MAMA natafi saina dawo toh *INTISAR*Allah ya bada sa a ameen
Fitarwa keda wuya saitaji ankira sunanta koda ta jiyo saitayi murmushi saboda *INTISAR*bata cika yin dariya ba sosai murmushi ne nafaye yi       aa *ZAINABU ABU MAI TAGWAYEN SUNA* kina nufin kema yau dai kice da wuri Zaki fita eh wlh kinsan halin mlm Hussain bashida dama wurin bugun letti shiyasa nake son na dawo da wuri ALLAH SARKI wlh Nima shiyasa nake son naje da wuri

Kai su *INTISAR* akwai tsoron duka Kamar sis maimounat 🙊🙊😂😂

Wata kasuwa Naga sun Isa Mai dauke da shuke2 ITATUWA  wurin saikaga yayi sanyi waje suka samu daban suka sauke kayansu Sannan suka zauna daga gefen titi wanda yaraba kasuwar biyu daga bangare daya wani makeken COMPANY ne ake ginawa saboda haka ma aikatan company suna zuwa Nan kasuwa suna sayen abinci suci

Hakan yasa su *INTISAR* suke aje abinci anan Kuma suna ciniki sosai ahaka Har suka saba da ma aikatan *INTISAR DA AMINIYARTA ZAINAB* sunyi daban da sauran masu tallah GA natsuwa GA tsabta hakan yasa anfi sayen nasu biyata sauran wata rana ne *ZAINAB* kawar ta ba tazo ba ita kadai ce tazo kuma alhmdlh tayi ciniki sosai karfe 4:00pm tayi don haka ta fara Shirin zuwa gida saboda zuwa islamiyya don *INTISAR*Sam bata wasa da karatun ta Dana yar uwarta wato *SURAYYA* autarsu su kenan son karatun da *ZAINAB* keyi shine yahada ta da *INTISAR*Kuma class dinsu daya da ita harma school dinsu na boko daya Kuma class dinsu daya
Tafara Shirin zuwa gida kawai saita hango wasu Samari su biyu tana ganinsu ta ganesu sune shekaranjiya da jiya suka zo suka sayi abincinta yauma Kuma sune suka zo yauma murmushi tayi musu Sannan ta gaidasu dayan NE yace mata akwai abinci kuwa eh akwai OK plss zuba muna toh a plate biyu ta zuba musu tasaka komai Sannan  ta Mika musu shi dayan dai binta kawai yake da  kallo

Yayi Nisa sosai cikin kallon ta wanda ita bata ma San yanayi ba abokin sa Mai suna *MUHSIN* shine yadan bigeshi ya Kira sunashi *ABDUL-MAJID* Sai Sannan ya dawo daga zuria tinanin da yayi ya karbi abinci ba tareda yace komai ba

*ABDUL-MAJID MUKHTAR* kyakkyawa NE na gaske mahaifin sa shahararren Mai kudi ne tsohon *DOCTOR*ne yana kula da iyalin sa sosai *ABDUL-MAJID* yayi karatunsa ne a *FEDERAL UNIVERSITY A ENGLAND* Inda Shima yaranci Doctor ahalin yanzu ma yana aiki ne a *FEDERAL HOSPITAL* dake *ABUJA* yanzun ma a banda ya kawo KEBBI STATE shine mahaifin sane yake Gina sabon company shine Sai ya turo shi domin ya kula da aikin *MUHSIN* abokinshine atare sukayi  karatu a England
Wannan  kenan

Saida suka kammala cin abinci Sannan ta tattara kayanta ta wanke suka bata kudi wadanda suka fi karfin na abincinta kin karba tayi sukayi2 Taki ta karba dole suka bata na abinci ta ta wuce zuwa gida
Binta sukayi da kallo
Wannan kenan

*ASALIN LABARI*

BAYAN WUYA Where stories live. Discover now