BAYAN WUYA part 21

995 44 1
                                    

🌷🌷 *BAYAN WUYA*......... 🌷🌷
                        🌷

*( it torchs the herts of the readers based on true life story)*

    *writing - by*
*ameenart Umar fana (AUFANA)*

   
🌷 *INTELLIGENT WRITER'S ASSO...* 🌷
*[ tsintsiya madaurinki daya]*

     
     *DEDICATED TO - hussaina uthman abubakar (ummun meenal)*

*tinda nake a rayuwata bantaba samun wanda ya zagar man iyayena ba Sai yanzu iyayena sune farin ciki na coz sune silar zuwa na duniya toh yau nasamu*
*yoo ke yar bantan uba wlh kinci sa a daban iya zagiba Dana ce ubanki Kuma in Kara maki da jarkaniyarki yar bahaushen mahaukaciya kokin dauka ba musan lbr tsohon najadu ba Mara imanin banza haka kawai Zaki kama tsoho na ki zaga toh wlh don ban iyaba ne da saina ce ubanki Mara imani yar tsohon najadu Mai shan giya da casa Mai tare yammata a titi ehi idan Kuma karya NE toh ki Musa inji*

    *PAGE 100-105*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

******  ******  *******

wani irin farin ciki mama take ciki Wai iyayenta ne da Yan uwanta suka zo ganta yau Har hawayen farin ciki saida tayi su surayya Sai murna ake saidai aleeyah bataji dadi ba coz INTI bata Nan amma ba laifi tinda GA surayya Nan kwanan su daya da zuwa mama da surayya suka shirya suka kaisu gidan baba hjy tayi farin cikin ganin su ba kadan ba tarba ta musamman ta masu da hadaddin girkin ta saida sukaci suka Sha Sannan aka Kara gaisawa shi abi da baffa dama suna falon baba Abba Ibrahim ma yazo yakira su INTI yabasu suka gaisa Kuma sukayi masu barka da zuwa haka ma Yaya Hussain Shima sun gaisa Kuma yace sun kusa hutu dasunyi zai dawo Kuma zaije Sudan baba Ibrahim yabasu lbr baikon *INTISAR* sun yi farin ciki sosai tareda adduar zuwan lkc bikin lfy ranar dai anan suka wuni Sai dare suka koma gida

*ABUJA CITY*

tinda aka sanar da MAJID anyi baiko yake cikin farin ciki harda azumin godiya yayi bacci frnd nasa kuwa sun tayashi murna sosai wata rana ne yadawo daga office dayake yay da wuri suka tashi gidan aunty Salma yaje da yake sundawo suna Nan Nigeria tattaunawa sukayi Akan yanda komai zaizo nrml dafarko dai yanzu kayi batun gininka lefe Kuma dubai zanje na hado inada kawaye acan sosai Kaga Sai inje can in hadoshi toh ai ke aunty Salma matsalar a kebbi fa take karatu murmushi tayi tace wannan duk ba matsala bace ba Sai ka Sama mata admission anan ba saita dawo Nan din da karatu OK haka zaayi Kam haka Sai suka tattauna daga bisani yamata sallama ya wuce gida

UMMU Salma yanzu shahararriyar yar business ce kasashe2 take zuwa business dayake dama shi ta karanta Kuma mijinta baya hana ta coz shine ya bata Jari hat lefe taken hada idan ta Kare Sai biyata balle Kuma kayan mata magungunan mata na Karin NIIMA duk tana sayarwa tananne tahadu da Aysha matar MUHSIN frnd na MAJID itama su taje sayarwa tareda English weres na mata hakan yasa suke mu amalala

Mutan Sudan fa anji dadin kebbi Sai faraa suke da farin ciki komawa zasuyi gida domin suyi Shirin auren INTI amma fa Yaya Hussain yace su jirashi su wuce tare don haka yasa basu wuce ba su Hussain an kammala exam din yuji 2 second semester alhmdlh yanajin dadin karatunsa haryanzu fa first class yake bugu shiyasa MAJID kejin dadin kula dashi sosai yanzu Kamar frnd haka suke ranar litinin 8:30am Hussain yabaro Abuja yakamo hanyar kebbi Sai 4:35pm Sannan iso murna da tarba Mai kyau yasamu Sai yaga duk wurin ya canza masa abun gwanin ban shaawa Sai farin ciki yake da faraa yana hutawa yaje gidansu baba yagaida hjy da baba sun masa barka da zuwa Kuma anfada masa batun aurensu INTI yaji dadi sosai harda yar kwallarsa coz yatina da abbansu
Kwanan Hussain uku da dawowa suka wuce Sudan suka  bar su mama da kewarsu

Su INTI fa karatu ake sosai duk ta rame saboda karatu exam takusa saboda haka yanzu ko su mama sun kirasu basa samu coz kashe wayoyin suke karatu kawai suka saka a gaba INTI duk ta rame sosai khadija Har mamaki take Wai lfy kuwa take idan MA ta tambaita bafada take ba saidai tace karatune kawai wata rana khadija ta Kira Abba a waya tafada masa dakyar INTI yafada masa cewar abban ta take tinani tana yawan mafarkinsa nasiha Abba yamata sosai Sannan yace suyi karatu Kuma su kula da mutuncinsu akoina suke INTI taji dadi sosai tin lkc kullum idan tayi sallah Sai tayiwa abbanta adduah haka dai Har suka fara exam

Allah sarki rayuwa kenan yanzu Kam su INTI basuda matsalar rayuwa alhmdlh saidai godiyar ubangiji don shine yafitar dasu acikin wuya zuwa dadi

Wani tabkeken makeken fili ni MAJID yasiya acikin birnin Abuja ni kaina saida tsinke daganin girman filin wani shahararren Mai zane2 gini yasaka aka samo masa kudi masu yawa ya bashi domin yazana masa gini Mai kyau yako cika aikinsa company dady ne zasuyi aikin ginin Kuma yace shi nanda 1 month yake so yagama komai don haka ba tareda wani bata lkc ba aka soma ginin aiki na tafiya yanda MAJID ke so saidai ba koda yaushe yake zuwa ba saboda aikinsa amma komai na tafiya nrml 

*INTISAR* exam nabasu wuya saboda haka yanzu ko waya ma sundaina yi da MAJID amma fa koda yaushe yana ranta musamman MA idan ta kalli zoben engagement nasu da suka yiwa kansu kamin amasu Sai tayita murmushi ko dariya ita kadai abun dariya yake Bawa khadeeja

Su Abba Ibrahim fa sun fara Shirin biki don aurarda Yaya mata Har biyu koda kanada abun hannun ka akwai Dan wuya don haka yasa yafara Shiri tin yanzu

   *********   ********

Alhmdlh *INTISAR* sun kammala exam dinsu cikin sa a amma fa sunci wuya INTI dabata saba ba duk saita rame amma fa Kam cikar budurci tana Nan saima karuwa take musamman kirjinta don cike yake tab dana shanu ranar da suka gama aranar da dare ta Kira habibinta nurul kalbinta yana daga kiranta abinda yafara cemata my pretty na na am my nurul kalbina Ina fatan kana cikin koshin lfy murmushi yayi yace inako nake cikin koshin lfy idanuwa a makauce suke kunnuwana a kurmance duk suna kirshirwar ki murmushi tayi wanda yake bayyanarda tsintsar kyanta tace insha Allah sunkusa samun ruwanda zasuyi maganin kishirwar da taje take damunsu wani irin dadi da sanyi yaji yana ratsashi ratsashi my pretty yaushe zaku dawo ne dariya tayi  tace Sai nanda 2 years Shima dariyar yayi yace Dana kunnawa Garin kebbi wuta Kai Kai Garin namu eh mana haka kawai zasu rikeman mata ta Kai Kai waya baka Abban ki dariya tayi tace yau muka kammala exam insha Allah gobe Sai gida wani dadi yaji coz yayi missing face nata sosai kice jibi tafiya ta kamani kenan ah nidai bance kazo kebbi ba idan kazo toh persions naka fa karka manta fa nanne zaka Sama mana abincin ci koka manta ne banason kafara ciyardamu da haram don haka karinka tsare gaskiya a duk Inda kake kaji ko my dear na insha Allah pretty zan kiyaye shiyasa wlh nake Kara sonki GA ilimi ga kyau ke GA komai ma dariya tayi harsaida fararan hakoran ta suka bayyana dear kadaina fasaman Kai fa haka dai suka Raba dare suna soyewarsu itadai khadeeja baccin ta take

      Tin 9:00am Abba Ibrahim yazo daukansu *INTISAR* Sai 10:30am suka Isa gida coz akwai Nisa ne Sai murna ake da dawowar amare kwanansu biyu da dawowa suka shirya sukaje gidan baba suka gaida shi anan suka wuni Sannan sukaje gidan  gwaggonsu ASMA'U Sai dare suka dawo gobe Kuma gidansu INTI zasuje..............




Kubiyoni 🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀

  AUFANA for life 😘😘😍🌷🌷🌷

BAYAN WUYA Where stories live. Discover now