BAYAN WUYA part 3

1.3K 76 0
                                    

🌷🌷 *BAYAN WUYA*........ 🌷🌷
                         🌷

*(it torchs the herts of the readers based on true life story)*

     *writing - by*
*ameenart Umar fana (AUFANA)*

         *DEDICATED TO - HUSSAINA USMAN ABUBAKAR (UMMUN MEENAL)*

_FATIMA MAMSSS (MAMIN AUFANA) this page it's for you my mami na nakine kekadai saboda kedin ta daban ce Taki kalar ma ta daban ce Allah ya tsare man ke ya kareki daga sharrin duk wani Mai sharri ameen ki shoshale abunki mami na I hert you my mami_😘😍

*PAGE 10-15*

*BISMILLAHI RAHMANIR RAHIM*

Jiki asanyaye ba kwari yatashi yana kuka yaja hannun *SARAH* suka kama hanyar fita mama naganin haka tafa wata irin Kara anan take tafadi kasa simammiya Ahmad NE yayi kanta yana kuka Mai tsananin tashin hankali Mota yaje yadauko domin Kai mama asibiti kwananta biyu a hospital Sannan suka dawo gida

Su Ibrahim duk sunji abunda ke faruwa as'mau tayi kuka tayi kuka sosai ba halin zuwa ROKON Abba saboda itama idan taje toh laifin zai iya shafanta don haka mama ta hanata babban abunda yake daga musu hankali shine tsattsauran furucinda Abba yayi na fitar da abubakar daga cikin zuriarshi abun bakara min daga musu hankali yayiba  shi kanshi Abba abun yadameshi sosai korar dansa dayayi gudan jininsa gashi Kuma yana mugun ji dashi amma Ina zuciya batada Kashi

Fitar da su abubakar sukayi direct gidansa dayake ginawa ya nufa da ita saboda baima San Ina zai kaitaba gidan dama kadan yarage a karasa aikinsa daki biyu NE da toilet biyu Bayan sun isane yabar ta yafita domin samo mata abunci saboda shi tsananin tashin hankalin da yake ciki yasashi baya Jin yunwa acikin dayan dakin ya kwana ita Kuma takwana a dayan dasafe ma abunci yasiyo musu sukaci Bayan yayi wanka ya shirya saiya fita ALAWA DA DABINO ya siya direct masallaci yaje baawani bata lkc ba yabiya sadakin *SARAH* naira DUBU ashirin dayake dama shirye yake anan take Kuma aka daura aurensu  Sannan aka Raba ALAWA da DABINO yakamo hanya zuwa gida

Allah sarki abubakar da Sarah Allah ya albarkaci auren ku ameen 👏

Bayan iso gida ne yamata bayanin komai yanda akayi taji dadi sosai amma Kuma tayi kuka ba rashin iyayenta a kusa da ita  🌷🌷🌷🌷🌷

Watansu uku da aure *SARAH* tasamu ciki wata goma Sha daya ta haifi kyawawan yayanta guda biyu wato twins mace da namiji makwabciya makwabciyar su ce kemata wankan jego kwana biyu da haihuwa hassana ta rasu tabar Hussain ahaka sukaci gaba da rayuwarsu Inda suke kula da yaronsu Har sukayi kwana SITTIN  shekararta biyu da haihuwa tasake samun wani cikin ta santalo yarta kyakkyawa Mai kama da mamanta sak mahaifiyar SARAH tabiyo Inda akayi suna Akasaka wa ya suna *INTISAR* wanda mahaifiyata ne tasaka mata shi Alhamdul komai Nataliya nrml SARAH taci gaba da rainon yayanta Bayan shekara uku SARAH tasake samun ciki tasake haifar ya Akasaka mata sunan mahaifiyar SARAH wato *BADEEYAH* but suna kiranta da SURAYYAH abubakar na matukar kula da iyalin sa yana ji dasu matuka gasu dukkansu kyawawane baram ma *INTISAR* wacca sak mahaifiyar SARAH tabiyo GA gashi Mai tsawo Mai santsi GA dara2 idanu GA siririn hanci Kamar biro Abin rubutun Yan boko 😁😁😁

Hussain nada shekara 5 *INTISAR*  nada 3 abubakar yasaka su school ita islamiyya dama suna zuwa anan islamiyya ne tayi Kawa wato ZAINAB a basu komai na karatu NOTEBOOK TEXBOOK DA UNIFORM abunda yarage kawai subfara zuwa dayake Kuma PRIVATE SCHOOL ce

Komai Nataliya nrml yara na karatu yayinda SARAH ta cigaba da rainon surayya abubakar Kuma na business dinsa rayuwa dai Sai godiyar ubangiji amma duk da haka wani lkc abubakar da SARAH idan suka Tina family nasu sukayi kuka sosai daga baya Kuma sunana kansu hakuri saboda basu son yaransu Susan abunda ke faruwa

Babban abunda ke dayawa abubakar hankali shine kaddarori dake ta zuwa masa acikin business dinsa GA asarori dayaketa yi abun yana mugun daga masa hankali gabana sabon ciwo daya ziyarrceshi yamasa zuwan bazata wato diabetic ciwon shuga

Niko nace harma na gishiri saikayi 🤣🤣🤣 tinda kakibin umarnin iyaye hmm Allah ya kyauta

Komai ya jagulewa abubakar ga ciwon Nan yamatsa masa sosai dikda yana zuwa ganin doctor Kuma yanashan medicines sosai baya wasa da shan MAGUNGUNAN sa saidai tayi yawa saboda yanzu ma bakowanne abinci yake ci ba

*AFTER TWO YEARS*
Zan iya cewa yanzyanzu gidan abubakar saidai godiyar ubangiji kudin sayen abincin ci ma saiya gagaresu GA ciwon abubakar yamatsa masa sosai gashi Kuma babu kudin sayen magani

Niko nace anata Kai waketa Kaya 😣😣

Duk halinda iyalin abubakar dashi kansa suke ciki family abubakar suna sane amma ba yanda suka iya mama takanyi kuka sosai akwai wata rana da tadibi abinci tasa Ahmad yakai gidan abubakar lkc da Abba yaji Kamar yadaketa tin lkc bata Kara ba saidai tayita masu adduah

Ku biyoni 🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀
    
         Kuna tareda yar mutan KEBBI ne

BAYAN WUYA Where stories live. Discover now