BAYAN WUYA part 10

999 58 1
                                    

🌷🌷 *BAYAN WUYA*...... 🌷🌷
                     🌷

*(it torchs the herts of the readers based on true life story)*

    *writing - by*
*ameenart Umar fana (AUFANA)*

   *DEDICATED TO - hussaina uthman abubakar (UMMUN MEENAL)*

_sis maimoinath zamuyi missing din BUSHRAH wlh Allah dai yabaki lfy yakawo maki sauki ya Kara maki kaifin basira da hazaka da laushin hannu muna ameen_

_sister ummu Bashir Allah ya bayyanata yatona masu asisri ubangiji Allah ya sa aganeta wlh zamuyi missing din book dinki sosai Allah dai yakara hazaka da kaifin tinani da laushin hannu ameen_

   *PAGE 45-50*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEM*

   ****************

saida aka kusa tashi daga school Sannan *INTISAR* tafarka abinci suka bata Sannan Tasha magani suka Kara yimata wasu allurai ZAINAB ce tashigo Tareda surayya tana rike da jakar *INTISAR* sannu suka mata Sannan tasaka kayanta da aka wanke wadanda suka baci saida Norses suka tabbatar da tasamu sauki Sannan suka barsu suka wuce gida suna cikin tafiya ZAINAB nata tsokanar INTI ita kuwa hararanta take Har suka Isa gida Bayan ta gaida mama daki ta wuce abunta ZAINAB ce tayiwa mama bayanin rashin lfy INTI tace tinda naganta da safe nagane batada lfy Dana tambaita cewa tayi klw take dariya ZAINAB keyi sosai daga bisani ta wuce gida

Yau Kam yar mama ba zaaje tallah ba ko mama tafada tana murmushi kunya ce takama INTISAR hartasa abun cewa ma yau Kam SURAYYA taje tallah su INTI ko jinya ake

     ***************

BAYAN wasu watanni alhmdlh su INTISAR an shiga ss3 saboda haka ba zama ba tsayi da karatu yayinda yayanta Hussain ke taimaka mata sosai wajen karatu saboda yarinyar yana ji da ita kawai basira sosai Har alkawarin yayi idan Allah ya wadata shi toh Sai *INTISAR* taci gaba da karatu Abu daya ke damunsu shine ciwon mama abun yanzu ya girma sosai Har bata ita tafiya dakyau aiki ma su INTI keyi saboda haka INTI abubuwa sun mata yawa GA karatu GA tallah GA aikin gida damarta dai surayya natayata Kuma ko ZAINAB takanzo idan batada aiki gida Sai ta tayasu Har sukare tallah ma wata rana SURAYYA ke zuwa saboda ta fara girma

EXAM dinsu *INTISAR* Sai matsowa take kusa yayinda ciwon mama ke Kara tsananta wani abokin yayanta ne Umar yabawa Hussain shawarar suje da ita asibiti kawai akwai wasu dake bada kudi kawai do ataimaki bayin Allah marasa karfi don haka baiyi wasa ba saida yasamu kudin Mota da kyar yasaka mama da *INTISAR* akabar surayya gidansu zainab basu wani dade ba suka Isa a FEDERAL MEDICAL CENTRAL BIRNIN KEBBI STATE Kati suka fara siya ta ganin doctor Bayan wasu mintuna suka samu ganin doctor anyi photo anyi gwaje2 Sannan aka fito da result sun tabbatar da abun yayi yawa miyasa suka Barta gida haryayi yawa basuzo asibiti ba ba wanda yayi magana acikinsu nadai doctor yayita fada Sannan yamusu bayani kudin aiki naira dubu dari tareda jini Kamar goma hudu saboda tiater saida isasshen jini ai Nan Hussain yayi Suman tsaye ita Kam *INTISAR* banda kuka ba abunda take saboda tasan Ina suka GA koda dubu ashirin ne balle Har dubu dari ita Kam tasan mamanta mutuwa zatayi shikenan tarasa abbanta yanzu Kuma mamanta zata tafi tabarta kuka take sosai Mai tsuma ZUCIYAR Mai sauraro idanun Hussain tini sun kada sun canza Kala tausayinsune yakama doctor amma yarasa wane taimako zai masu ahaka dai suka tashi suka tafi Har suka fita doctor na kallon su mama suka fara sakawa a Mota saboda yanzu ma ko tafiya dakyar take yinsa Bayan sun saka ta Sannan suka shiga suka kama hanyar gida rai abace

     ***************

*ABUJA CITY*
zaune yake a kasaitaccen falon sa yana duba wasu files noking door akayi yayi izini da kowaye ya shigo frnds dinsa ne doctor MUHSIN doctor Umar da doctor Aliyu murmushi yasaka musu tareda Mika masu hannu sukayi musabaha Sannan suka zauna MUHSIN ne ya dauko masu drinks da glasscup suka Sha Bayan sun Kara gaisuwa suka fara Shirin tafiyar su wani aiki da zasuji suyo a karkashin ikon hospital dinsu a kebbi ne MUHSIN ya Kallen Wai frnd Anya kuwa kana shirin tafiyar nan sainake ganin Kamar bakason tafiyar ya fada yana tsokanarsa wani irin harara *MAJID* yayi masa kamin yace ai duk nafiku Shiri Kuma nafikuson son tafiyar dariya sukayi su duka don sunsan kwanan zancen UMAR ne yace saboda aje aga GIMBIYA koh dariya yayi yace sosai MA kuwa ahaka dai sukai ta firar su ta fiyar su 10 ne aka zaba zasuje

     ***************

*KEBBI CITY*
gida suka isa duk basa cikin walwala *INTISAR* haryanzu kuka take mama ce ke lallabata sun iso saboda haka suka fito saida Hussain yakamawa mama Sannan tafito rike yake da ita har suka shiga gida zama mama tayi tadinga yiwa yayanta nasiha Akan komai Kaga yasami bawa toh daga Allah ne Sannan Kuma dama anrubuta masa shi acikin kaddararsa saboda haka su daina damuwa dagowa tayi idanunta sun kada sunfita daga ainihin halittarsu saboda tsananin kukan da tasha mama Har yaushe zamu daina damuwa ba abbanmu ba dangin ki bana Abba mukadai Sai masoya da abokan arkiziki Sannan gaki yanzu ciwo namiki Barazana mama Ina zamu Sami kudi Har naira dubu dar.... Kasa karasawa tayi saboda kuka dayafi karfinta haka yaya Hussain shima kukan yake yana fadan duniya Ina Zaki damu miyasa rayuwa tayi muna haka ya Allah ka kawo muna dauki kuka suka sosai mama ce dafasa dayake duk kusa da ita suke zaune yayana kudaina kuka wata rana Sai kunyi mamakin canjinda ubangiji zai muku amma kila Nima bana nan Ina kushew..... Bata karasa ba kuka yaci karfinta dakyar tasamu ta tsayar dashi tajawosu ajikinta cikin kauna irinta da damahaifi kudaina kuka *BAYAN WUYA SAI DADI* ahaka dai rayuwa tacigaba da tafiya cikin kunci

     **************

*ABUJA CITY*
Shiri suke sosai saboda tafiyar takusa Ranar MONDAY zasu wuce saboda haka Shiri suke sosai

Yau ne MONDAY tin 80:15am suka kamo hanya zuwa kebbi state dayake duk acikin motar hospital dinsu suke............


Kubiyoni 🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀

     AUFANA for life 😘😘😍🌷🌷🌷

BAYAN WUYA Where stories live. Discover now