BAYAN WUYA part 2

1.9K 82 8
                                    

🌷🌷 *BAYAN WUYA*🌷🌷
                  🌷

*(it torchs the herts of the readers based on true life story)*

      *writing - by*
*ameenart Umar fana (AUFANA)*

          *DEDICATED TO HUSSAINA USMAN ABUBAKAR (UMMUN MEENAL)*

_WANNAN page din gabadansa na mutan KEBBI state ne ban manta dakuba Kuna raina sosai gashinan nakune ku shoshale abunku kudin ma na daban ne inasonku over_😘😘😘😍

*readers kuyi hakuri da tyaiping error don Allah Kuma kusani kukara sani Ana mugun tare*🤝😍

*PAGE 5-10*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEEEEM*

*ASALIN LABARI*.....

ALHJ MUSTAPHAH tsohon *BARRISTER*ne yanada mata daya hjy *FATIMA*da yara guda hudu alhj *mustapha*mutum ne Mai tsattsauran raayi magana daya yake baya biyu Allah ya azurtashi da Yaya *IBRAHIM ABUBAKAR AS'MAU AHMAD* alhmdlh duk sunyi karatu Kuma sun kammala Ibrahim doctor ne abubakar Kuma business yake saboda dama shi yakaranta Ahmad bai karasa karatun ba da yake low yake karatu Sai as'mau itama digiri ne da ita
Anyi bikin Ibrahim da as'mau Kuma duk wadanda suke so suka aura yayinda Ahmad yaci gaba da karatunsa shikuwa abubakar yaci gaba da business dinsa yanzu yayi kwari sosai harma kasashe zuwa yake yin kasuwanci
ABUBAKAR sunje kasar *SUDAN*acan yahadu da wata balaraba Mai suna *SARAH ABDUL-JALAL*anan take shakuwa tashiga tsakaninsu bawani jimawa suka fara soyayya koda *SARAH* ta gabatar da abubakar agun iyayenta amatsayin wanda takeso Kuma takeson aura ba karamin fushi iyayenta sukayi ba saboda sun zaba mata wanda zata aura saidai bata saniba

Niko nace lallai akwai cakwakiya 😂😂

Bayan yaje gidan su ne da 2 days yafara Shirin dawowa gida don ayi Shirin zuwa nema masa auren *SARAH* airport yanufa suka shiga ✈ luuuu Sai NIGERIA

Bayan ya iso gida antaryeshi da murna bazan ma mamanshi abar kaunansa kwanansa 5 da dawowa wata ranar ASSABAR ne abban su yakirashi a falon sa ba tareda bata lkc ba ya amsa Kiran Abba
*ABUBAKAR*Abba ne yakirashi na am Abba toh alhmdlh ka kammala karatu Kuma kanada sanaar yi don haka yanzu aure kadai yarage ma babban abunda nakeso na gayama shine nahada auren ka da Maryam yar aminina kabir    ai abubakar baisan lkc da yayi saurin dagowa ba saboda tashin hankalin da yaga yanason bakuntar sa Abba dama da mgnr aure na nazo Nigeria nasamu mata a Ina take abunda Abba yace kenan atakaice sunanta *SARAH ABDUL-JALAL*yar kasar Sudan ce Abba baice komai ba can yace tashi kabarmin falona ba musu ya tashi saboda yasan halin mahaifin nasa

Two days kenan da maganar da Abba yayi masa amma Har yanzu bai Kara ganin fara AR mahaifinsaba yau ASSABAR abubakar baje kasuwa ba yana kwance Sai faman tinanin SARAH yake can saiyaji ankirashi a phone nasa koda ya duba Sai yaga new number ahankali ya daga ai dasauri ya Mike tsaye jin murnar abar kaunarshi cikin wani irin yanayi na damuwa da alama ma kuka take yi cikin harsher trance take masa bayani saboda bata iya hausa ba anan take hankalina ya tashi

Abubakar kazo ka daukeni zasu aramin wanda banaso plss come and help me plss 😭😭 kuka NE ta fashe dashi Inda shiko ya Kara shiga tashin hankali bawani bata lkc anan take ya shirya Sai airport yashiga jirgi Sai SUDAN bai je gidansu SARAH Ba Sai da dare suka shirya shi da abokinsa suka je gidan ba tareda kowa yasani ba suka dauko SARAH wacca ake hidima bakinta daga nan basu wane dade ba suka hau jirgi zuwa NIGERIA



Koda suka iso dare yayi don haka yanzu tinanin yake Ina zai kaita yana cikin tinani ne Sai kawai ya yake shawarar kaita gida gun mama wata kil su tausaya musu

Toh su male Abu kenan toh Allah ya sa abbana ya amince ameen 👏👏👏👏👏👏

Direct gidansu ya wuce da ita koda suka Isa gidan abbansu da Ahmad sunje madallah mama Kuma tana dakinta tana sallah don haka falo ya nufa da ita Bayan sun zauna Sai ya kawo mata drink Tasha ji n shigowa da mama taji anyi NE yasa tafini domin ganin suwaye ai kusan Suman tsaye tayi ganin abubakar da yarinya wacca  dagani  ta dakuma shi garta kasan Bayar KASAR ceba gabanka NE ya fadi kardai ace yarinyar Nan balaraba ce abubakar yaje ya dauko musu Tabb tashin hankali wanda baasakamasa rana karasa mama tayi acikin falon

tambayoyi NE mama ta jerowa abubakar Kamar haka abubakar *wace ce wannan yar wace daga Ina take* bai iya ce mata komai ba shiga Abba da Ahmad sun  dawo daga masallaci falon  suma suka shigo binsa sukayi da kallo kamin Abba yace abubakar wacece wannan cikin rawar murya yafara basu labari komai daya faru saida yakare duka Abba ya nuna sa da yatsa Sadiq ka rainani

_KAI Allah dai ya biyaka Abba Kai kadai ke Kiran sunan Nan na SADIQ_🙈🙈🙈

Tsawa Mai karfi Abba ya dakawa abubakar Sadiq ka rainani kabijirewa zabina yar aminnina *Maryam* Dazan hazaka aure da ita kabijire ka watsamin kasa a ido ka nunamin ban Isa gareka ba to wlh wlh kasani idan har kaki zabina ka auri wannan ya nuna SARAH wacca tinda aka fara fitinar tayi shuru tana kallo duk da  Bayard take jiba amma tana fahimtar su toh wlh bani bakai Kuma bakai ba dukkannin zuriah ta Kuma na fitar dakai acikin yayana tashin hankali mama ce zatayi magana Abba ya daga mata hannu alamari tayi masa shuru shuru tayi amma kuka take sosai haka ma Ahmad balle Kuma abubakar wanda tsananin tashin hankali ya bayyana a fuskar shi Abba yakama hanya zai fita abubakar ya bishi da gudu yakike kafarsa yana kuka Mai tsuma ZUCIYAR Mai sauraro abbana karkayi fushi dani don Allah ka yafeman abbana Tsawa Mai karfi ya daka masa kamin nafito daga ciki ka tabbatar kabar min gidana in Har ba tsohon naka bane

_Allah sarki SADIQ Har yabani tausayi wlh_😭😭😭😭

*wasa farin aiki*

Kubiyo 🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀

BAYAN WUYA Where stories live. Discover now