BAYAN WUYA part 11

917 53 1
                                    

🌷🌷 *BAYAN WUYA*........ 🌷🌷
                      🌷

*(it torchs the herts of the readers based on true life story)*

   *writing - by*
*ameenart Umar fana (AUFANA)*

        *DEDICATED TO - hussaina uthman abubakar (UMMUN MEENAL)*


_Wannan page din gabadansa na Masoya wannan book din ne Ina godiya sosai da kaunarku agareni Allah ya bar zumunci ga shinan naku ne kukadai ku shoshale abunku kudin ma na daban ne inayin ku irin sosai dinnan tnx tnx tnx alot_😘😘😍


    *PAGE 50-55*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHEM*

    ****************
Yaune MONDAY don haka tin 8:15am suka kamo hanyar kebbi state dayake duk acikin motar hospital nasu suke

Sai kusan 60:00pm suka Isa kebbi state a gajiye don haka kowa wajen hutawa yanema shikam naki hankalinsa nagun *INTISAR*dinsa Kuma yanaso yaje gidan kakannin sa ya gaidasu amma ba Hali saboda tafiyar batasu bace ta hukumar hospitalc ce saboda haka abunda yakaisu shi zasuyi kwanan su daya da zuwa suka fara aiki ba wasa acikin FEDERAL MEDICAL CENTRAL HOSPITAL

       ****************

Su *INTISAR* axam ta matso kusa saidai Sam batacikin walwala saboda rashin lfy mama gashi batada isasshen lkc karatu ga tallah ga karatu ga aikin gida gwara ma aikin guda surayya na tayata saboda itama yanzu girma yafara kamata wata ranar ALHAMIS ce su INTI basu zuwa islamiyya don haka tana wajen tallah kasuwa surayya na aikin gida Yaya Hussain Kuma yana wajen kwadagonsa ZAINAB ce tayi sallama tashigo surayya ta Gaidata dayake ita yay nataje tallaba tazo ne tagaida mama da jiki daki tashiga domin gaida mama kawai samunta tayi tana wani irin nishi tarike kafarda ke ciwo hawaye take tana ambaton sunayen ubangiji cikin rudewa da tashin hankali ZAINAB ta isa gunta tana kiranta mama2 abunne ya tashi sannu mama tashi tayi tafito tacewa surayya taje takira Yaya Hussain a gidan Inna Mai ice yanacan yana faskare acan ita zataje takira *INTISAR* a kasuwa toh tace Sannan tasaka hijab dinta tafita itama fita tayi domin Kiran INTI basufi 30 minutes ba suka iso kowannensu cikin kidimewa baram ma *INTISAR* saboda ita kayanta ma na tallah saida ZAINAB ta dauko mata kuka take Mai tsananani ganin mahaifiyarta acikin wani Hali Yaya Hussain ya zamuyi da mama ta fada tana kallon sa rasa abun cewa yayi saboda ji yake duniyar gabadai tamasa kunci gaya ko sisi bashida shi faskarenda ma yakeyi bata biyashiba Sai ya karasa fita yaye ba tareda yace komai ba gidan Inna Mai ice yaje yace don Allah ta bashi kudin mahaifiyarsa ce ba lfy zai kaita asibiti ne idan sun dawo zai karasa mata faskaren bataki ba tabashi naira dubu uku yamata godiya yafita Mai tazi yasamu Sai gida yana isa gida basu wani tsayaba suka dauki mama Sai asibiti taimakon gaggawa aka basu likitoci suka shiga aikinsu Bayan shiga da mama da 30 minutes doctor yafito yakira Yaya Hussain a office *INTISAR* kin zama tayi saida ta bisa saboda taji halinda mahaifiyarsu take ciki doctor bai hanata tashigo ba anan take ya fada masu halinda mahaifiyarsu take ciki idan baayi saurin cire mata abun ba toh zata iya rasa kafarta saboda abun yataru yayi yawa sosai yamata nauyi shiyasa bata iya tafiya da kafar so kuyi sauri kuje ku biya kudin operation Hussain mutuwa yayi anan zaune saboda duk ya rikice ya dimauce yarasa ya zaiyi tinanin sa duk ya tsaya cak duka2 dubu daya ya rage masa toh Ina zai samo kudi yanzu hawaye NE kefita a idonsa *INTISAR*  kuwa kuka take sosai Kamar ranta zai fita tausayinsu ne yakama doctor matuka *INTISAR* tashi tayi ta fita daga office din tana wani irin kuka Mai tsuma ZUCIYAR Mai sauraro tafiya take Sam bata ganin gabanta duhu take gani saboda tsananin tashin hankalin da take ciki batayi aune ba tajita ajikin wani mutum saboda Sam bata ganin hanya.........

Toh 🤔 kowaye wannan mutumin oho 🤷🏼‍♀



Kubiyoni 🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀

   AUFANA for life 😘😘😍🌷🌷🌷

BAYAN WUYA Where stories live. Discover now