BAYAN WUYA part 9

1K 60 2
                                    

🌷🌷 *BAYAN WUYA*....... 🌷🌷
                      🌷

*( it torchs the herts of the readers based on true life story)*

     *writing - by*
*ameenart Umar fana (AUFANA)*

        *DEDICATED TO - hussaina uthman abubakar (UMMUN MEENAL)*

_WANNAN page din gabadansa na kine sister Fatima Zahra surbajo Anty na kishoshale Abunki kina raina Kuma in yin ki irin sosai dinnan kina bamu sweet and nice sosai a books dinki Allah ya Kare muna ke daga sharrin mahassada da makiya yakara maki basira da hazaka da kaifin tinani da laushin hannu ameen 💖 I HERT YOU OVER AND OVER 💖😘😍_

*WLH WASU READERS abunda kukeyi Sam bakwa kyautawa karatunnan fa ba wanda nasa dole idan Kaga dama ka karanta bansaka dole ba Nike rubutawa da hannuna Sannan Nike da data na so banga abunda zaisa kamin wulakanci ba nida abuna wlh bana daukan raini saboda haka a kiyaye ehi*

   *PAGE 40-45*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHEM*

*INTISAR* murmushi tayi tace Um.. Um.. nima na amince kin amince dame yafada yana kallonta da murmushi boye fuskar ta tayi INA SONKA mana 🙈 dariya yayi yace toh nagode sosai Allah ya barmu atare fira yake dan yimata wacca bata wuce kalma daya zuwa biyu itako tana masa murmushi wanda yake balain burgeshi Sai kusan 9:00pm Sannan suka masu sallama suka wuce gida cikin farinciki da nishadi

   Kusan kwana hudu kenan *MAJID* nazuwa gidansu *INTISAR* susha firarsu harda mama fa sukan suna Sansa Sambashida girman Kai irin na sauran yayan masu kudin kamin yazo Sai yayiwa su *INTISAR* tsaraba musamman surayya sarakunan son sweet da chocolate ganar company dadyn MAJID komai natafiya nrml don haka yafara Shirin komawa ABUJA saboda hutunsa kadan yarage ranar Tuesday zai wuce don haka ranar Monday da dare yaje yayiwa kakannin sa da sauran yanuwa bankwana a gidansu INTI yadade saboda duk ta bata fuska Taki tasaki ranta saida yayita bata hankuri yana kwantar mata da hankali Sannan tasaki ranta fira sukayi sosai Sai wurin 10:30 ya wuce *INTISAR* harda Yan hawaye

Toh su *INTISAR* ankamu an tsunduma kogin SO 😜😂

        **********

*ABUJA CITY*
MAJID ya sauka gida lfy yasa tarya Kam ba karama ba don momy girki tasa aka masa na musamman aka gyara masa part dinsa Sai kyalli yake Bayan ya huta NE yasami dady yamasa bayanin komai daya gudana gameda gininsa yaji dadi sosai Kuma yakara sakawa dansa albarka yace Shima nanda 2 weeks zanje can kebbi yaga yanda ginin ke tafiya

Kwanan *MAJID* biyar da dawowa yakoma aiki yanzu aiki sosai suke a office dakyar yaje baiyi tiater ba gatarin patients agabansa masu bukatar kulawa saboda haka bashida lkc kansa ma balle nawani baya komawa gida Sai kusan 10-11pm Da yakoma Kuma batun samun hutu yake momy Har tausayi yake bata sosai

     ***************

*KEBBI CITY*
INTISAR karatu suke sosai amma duk da haka tana matsanancin tinanin *MAJID* wanda ya tafi yabarta mama Har takula da ita amma data tambaita zatace bakomai

Kwanaki natafiya watanni na shudewa su *INTISAR* ana ss2 first term saboda haka yanzu Kam karatu suke sosai saboda sunkusa shiga ajin karshe Abu daya zuwa biyu ke damunta nafarko rashin *MAJID* datayi na biyu Kuma rashin lfy mahaifiyar ta wani Abu ne yafito wa mama a cinya Har yafara girma sunansa *KARO* sunje asibiti anmata engections anbata medicines wanda idan Tasha Wai zai watse to harta shanye amma shuru rashin kudi yasa basu koma ba toh abun yana mugun daga musu hankali saidai ba yanda zasuyi kawai dai sun zubawa sarauta Allah ido

Wata ranar litinin ne *INTISAR* ta tashi da matsanancin ciwon ciki amma Taki sanarda kowa ahaka sukaje school tanata fama a ajima haka tayita fama kwata2 karatun ma bata fahimsar sa tini ZAINAB tagano batada lfy ta tambaita meke DAMUNTA dakyar ta fada mata cikinta ke ciwo can kawai Sai taji Abu yafito mata ta gabanta arazane ta fadawa ZAINAB dakyar tasamu aka tashi breakfast ZAINAB ce taje ta sanarda teachers nasu mata saboda *INTISAR* kuka taketa yi clinic akaje da ita ashe PERIOD ne engections suka mata Tasha magani Sannan suka wanka mata kayanta Sannan suka bata sabon pant da pad dakuma yanda zatayi amfani da pad din duk tayi daidai saidai Sai take jin kanta wata iri alamu rashin sabo kenan GA Kuma kunya datakeji saboda teachers dinsu mata su uku ne suka zo da ita kwantawa tayi cikin 10 minutes tayi bacci saboda alluran da aka mata harda masu saka bacci aciki

      **************

Saida aka kusa tashi daga school Sannan *INTISAR* daga baccin.......


Kubiyo🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀

       AUFANA for life 😘😘😍🌷🌷🌷

BAYAN WUYA Where stories live. Discover now