BAYAN WUYA part 22

891 44 1
                                    

🌷🌷 *BAYAN WUYA*........ 🌷🌷
                       🌷

*( it torchs the herts of the readers based on true life story)*

  *writing - by*
*ameenart Umar fana (AUFANA)*

🌷 *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....*🌷
[ *tsintsiya madaurinki daya*]

   *DEDICATED TO - hussaina uthman abubakar ( ummun meenal)*

_WANNAN page din gabadansa na badashi ga kungiyar Nan Mai albarka Mai tarin shahararrun marubuta wato INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION Allah ya Kara daukaka ki tareda marrubutanki Ameen summa ameen_


*PAGE 105-110*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

  **********  *********

TIN 9:00am suka shirya baba yasaka akaisu da motarsa wacca yake Hawa coz yanaji da Yan jikokinsa bye bye suka masu Sannan suka wuce ya Salam 😳 INTI tafada ganin yanda gidansu ya canja Kamar ma bashibane ai kwa da  gudu INTI tashiga ciki tana Kiran mama2 atsorace mama tafito don ganin meke faruwa INTI tagani tazo da gudu ta rungumeta dariya tayi Sannan tace yar mamanta kin tayarman da hankali khadija ce ta gaidata ta amsa cikin faraah Sannan suka shiga cikin falo zama sukayi mama tace kun karya kuwa hmm wlh komai bamuciba Kai haba kuna nufin hjy  bata baku Kari ba komai bata bamu ba ita ko dai hjy batasan baa barin amare da yunwa ba toh kuzo ku Diba  kuci khadija ce ta tashi tashiga kitchen ta zubo masu ita dai *INTISAR* mamaki duk ya cika ta Wai yau sune acikin irin wannan dankareren gini Allah kenan Mai canza rayuwa yadda yaso suna cikin falo suna shan fira kawai INTI taji Ana kwalla mata Kira daga bakin gate atsorace ta fita wazangani haka my sweet frnd rungume junansu sukayi nayi missing naki kawata lkc da muke school surayya ke fada man Wai Abba yazo ya daukeki wlh banji dadiba Allah sarki yar Uwa ta Abba daya daukeni makaranta yasaka ni University daka ABUJA school dinmu daya da yaya Hussain bai fada maki ba LA wlh bai fada man Kai amma wlh nayi farinciki suna tafiya suke mgn Har suka iso cikin falo suka zauna surayya ce tafito daga kitchen LA aunty zainab yaushe kikazo mama zo GA aunty zainab dariya tayi tace autar mama yanzu nazo Allah sarki sannu da zuwa yww ciki suka shiga ta gaida mama Sannan suka wuce dakinsu INTI aka fara firar yaushe gamo cikin Yan kwanaki khadeeja tasaba da zainab

*ABUJA CITY*

Company dady sun kammala WA MAJID gininsa coz akwai akwai kayan aiki ga kudi Kuma five millions dady yabawa MAJID Wai ya Kara a gininsa aikwa gini ne akayi nagani na fada

Aunty Salma na dubai wajen hado lefe two weeks tayi Sannan ta dawo gida Nigeria woww zo kuga lefe ya hadu karshen haduwa set na akwati biyar kowace damke take da Kaya ba momy ba hardady ya yaba da lefen MAJID yaji dadi sosai dalla2 motoci dady yabada guda hudu don Kai lefe aunty Salma ce da safiyya Sai Aysha matar MUHSIN frnd na MAJID sune zasuje Mota uku duk ajwatayyane Sai dayar Kuma suka shiga tin 10:30 suka kama hanyar kebbi asauka lfy

*KEBBI CITY*

MUTAN Sudan sun iso INTI taji dadi sosai don harda aleeyah akazo mata NE kawai suka zo maza Sai ranar daurin aure zasu zo aikwa Nan su INTI aka fara Shirin biki kusan kullum yanzu basa zama gida saboda hajaniyar Shiri

Su aunty Salma sun iso kebbi gidansu suka Bude suka shiga Bayan sun huta ne Aysha ta wuce gidanta dayake dama kebbi kayanta suke aunty Salma family house nasu sukaje suka Kai lefen suma suka gani suma sun yaba dashi sosai Sai 4:15pm Sannan aka wuce cikin wasu dalla2 motoci don Kai lefe gidan Abba Ibrahim aka Kai momyn su khadeeja kuwa ashe shirye take tasaka anyi kala2 girke girke da snakes kala2 acikin  babban falon gidan na baki aka sauke su saida suka ci suka Sha Sannan aka baje lefe domin gani masha Allahu barikallah babu ne Kawai babu komai yaji Salma sun Dan jima Sannan suka wuce kwana biyu da kawo lefen INTI aka kawo na khadeeja Shima dai Kam yayi barikallah

*ABDUL-MAJID* yazo kebbi tareda friends nasa sunzo sun kawowa su INTI invitation cards aikwa ranar su INTI wuni sukayi suna rabon I-V Mota daya MAJID ya basu aka kaisu koina harda frnds dinsu na kalgo University sun kaima Sai dare Sannan suka dawo

*AFTER TWO WEEKS*

Gida ya cika da Yan Uwa Sai farin ciki ake gwaggo ASMA'U kuwa tasaka su *INTISAR* gaba Sai gyaran su take da DILKA DA KURKUR HALAWA DA TSIME kowace rana nata Kala daban kwana biyu su INTI sun canza farar fatar nan ta goge takara fita tass tass komai na jikinta *INTISAR* ya bayyana tindaga kirjinta mazaunanta dakuma hips nata ita kanta tasan ta canza domin kuwa gyaran su ake bana wasa ba kudi gwaggwonsu tabiya masu yawa shiyasa ake masu gyaran kwarai

Yaune zaayi kamu don haka tin 5:15pm aka wuce da da amare wajen make up..............



Kubiyoni 🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀

  AUFANA for life 😘😘😍🌷🌷🌷

BAYAN WUYA Where stories live. Discover now