💞 NOOR
By The_Circle
Gudu muke yi sosai amma naki sakin hannun Yar uwa ta, sai da mukayi nisa sosai sannan muka tsaya don mu huta. Kafar Mimi na kalla nagan duk ta farfashe sabida tsabar wahala, ban damu da tawa kafarba ni dai fatana bai wuce mu tsira da ranmu ba. Kaman daga sama naga saukan kibiya a jikina wanda hakan ya sanya na fadi kasa wanwar.
Farkawa ta tayi daidai da shigowarshi cikin dan dakin da aka ajiye ni, nidai nasan na taba ganin wannan fuskar a wani gurin. Tunani na shiga yi don in tuno amma muryarshi ta katse ni "Ya jikin?" Nace "Da sauki amma Don Allah inane nan?"
Kallona yayi shekeke ya kama hanyar fita anan naga tambarin dake bayan rigarshi wanda yake nuni da yana daya daga cikin princes guda biyar na Masarautar Ming. Gabana ne ya fadi tunawa da nayi sune sanadin wahalan da muke ciki don yanzu nasan bani da kowa sai ragowan yan uwana guda biyu amma Mimi kam nasan sun ma kasheta. Wasu hawaye masu zafi ke zuba a kunci na inna tuna har abada mu bayi ne, in muka gudu kuma aka kamamu kisa ne, don ba'a bakin komi muke ba.Asalina
Ni dai sunana Noor, na tashi a wani kauye wanda yake karkashin Babbar Masarautar Ming. Bansan mahaifiya ta ba amma mahaifina yana raye har na kai shekara sha takwas a duniya, ina da yayye biyu, Ya Ali da Yaya Asma'u sai kanwata Mimi. Mun tashi tare da mahaifinmu Malam Adamu, ba abinda muka nema muka rasa sai yanci wanda inda sabo mun saba.
Mahaifinmu yana koya mana dabarun kare kai da na yaki amma kullum maganarsa bata wuce yan uwana su duka ukun su bani kariya wanda na kasa gane dalilin sa, a ganina ai ba nice karama ba.
Da haka a kwasomu a kawo Masarautar Ming sabida kasancewarmu marasa galihu.Cigaban labari
Karan bude kofa naji na dago daga kwanciyar da nayi idona kar akan Mimi, wani farin cikine ya kamani ganin tana cikin koshin lafiya saidai kafafunta da aka nannade da tsumma. Cike da farinciki ta karaso gurina
Tace "Noor kin tashi? Ya jikin? Meke miki ciwo?"
Dariya nayi sanin Mimi rikitacciyar yarinya ce
nace "da sauki ba abinda ke damuna"
tayi saurin cewa "Su Ya Ali suna nan zuwa dubaki, dazu muka hadu" Bance komai ba don nasan ba lallai suzo ba sabida yanayin bangaren aikinsu.
Fita tayi bata jima ba sai gata da abinci dama yunwa nakeji na zauna naci sosai, dana gama ta kwashe kayan ta fita dazu, data dawo ta mikomin wata kwalba na karba nace "menene wannan din?" Bawai dan bansan menene ba nayi tambayar sai don nasan maganine me tsada wanda ake sawa a ciwo kuma yana saurin warkar da ciwo. "Cewa akayi in baki" ta fada a takaice
Na juya kwalbar nace "inji wa? da fatan ba satowa akayi aka baki ba? Ki rufa mana asiri ki tashi ki mayar banaso" kallona tayi tace "Yareema Ameen ne yace a baki, shi ya taimakemu ya dawo damu ba'a kashemu ba, Noor wallahi yana da tausayi kinsan babu shi a cikin gasar nan fa"
Mamaki ne ya kamani jin cewa Yareema me jiran gado, isasshe kuma kasaitaccen cikin Yarimomi biyar na nahiyar Ming shi ya taimakemu. Ajiye kwalbar nayi a gefe kawai na kwanta.
Washegari tun asuba hayaniya tayi yawa a masarautar ga Mimi tanayin sallah ta fita na kasa gane meke faruwa, ina nan zaune har wajen karfe 10 sai gata ta shigo da kalaci, nan take sanar dani Yareema Ameen ne yasa gasar fidda baiwar da zata dinga kula da bangarenshi. Gasar ta kasu kashi uku, na farko hada shayi ne na gargajiya, na biyu kuma takarda za'a baku ku kwafi rubutun dake jikin takardar, wanda yayi saurin gamawa, na uku kuma karatu ne. Ansa gasar nan da kwana uku.
Tunani na farayi akan gasar, tabbas inaso inyi amma ina tsoron abinda zai hadani da Yareema Ameen. Da haka dai na hakura akan zanyi indai har inaso mubar masarautar nan koda ace iya yan uwana ne banda ni.Yau ne ranan gasar, na shirya nasa wankakken kayana na kananan bayi, na kama hanyar da zata sadani da farfajiyar gasar.
#Vote
#Comment
The_Circle
YOU ARE READING
💞NOOR
General FictionStory of Noor and the 5 princes of Ming Empire. Betrayal among them and read as love turns to hatred.