💞 NOOR
14
"Abba...Ab-bba" ta fada a rude. Kara rike hannunta yayi ya tashi zaune daga gishingiden da yake hankalinshi tashe. "Subhanallahi! Ummusalma meya faru?" Ya fada a rude tare da daukan alkawari cikin zuciyarsa, duk wanda ya aikata wani batanci a gareta tabbas kashesa zaisa ayi, bazai saurarawa duk wanda ya taba mishi 'yar lelen tashi ba.
"Yi shiru kimin bayani" ya umurta. Daidaita nutsuwar ta ta samu tayi duk da ba wani nutsuwa tayi ba sannan ta tattaro izzarta da isarta. "Abba Ya Fu'ad nakeso ka yafewa laifinsa domin rashinsa zai iya zautani. Abba zan iya mutuwa ma saboda rashinsa koda kuwa ni ce wadda yafi tsana a duniya"
Shiru tayi don jiran amsar mahaifin nata, tasan tabbas son da yake mata zaiyi tasiri a gareshi. Baza taso ace yau ce ranar zagayowar haihuwar ta ace kuma ta fara shekarar da mugun abu ba, taya za'a kashe mutum mafi soyuwa bayan mahaifanta da dan uwanta? Wani kukanne ya taso mata amma duk yanda takai da gujewa yin kukan sai da ta fara, muryar mahaifinta ce ta katse mata tunani.
"Yau ni mahaifinki Ahmad Al Omari na yafewa Fu'ad, indai hakan zai saki farin ciki Ummusalma"
Rungume mahaifin nata tayi cike da murna ji takeyi kaman an mata albishir da gidan aljanna, godiya ta shiga yiwa mahaifin nata. Tsinkayo muryar shi tayi yana fadin "Za'a tsareshi a bangaren da yake sauka na tsawon shekara guda har sai ya zama mutum na gari duk da bashi da wani abin Allah wadai sannan a sakeshi ya tafi Milan don ya fara sabuwar rayuwa"
Murnar tace ta koma ciki amma bata da yadda zatayi don tasan barinshi da akayi da rai ma ba karamin abu bane. Jakadiya Sarki ya bama umarni akan ta sanar da hukuncin shi.Filin Ya cika makil da jama'a wasu ma sai kuka suke suna Allah wadai da wannan Sarki saboda rashin imaninsa yakai inda basa tunani. Umurtar Yarima Fu'ad akayi daya hau tudun, ba musu ya hau. Igiyar aka sa mishi a wuya daidai nan wani dogari yace a dakata cikin daga murya ya fadi hukuncin Sarki, nan da nan gurin ya kaure da hayaniya ana yima Yarima Fu'ad san barka ana tayashi murna.
Tunda aka fita da shi nake ta kai kawo a tsakiyar kurkukun namu, gabadaya na fita a hayyacina dama tunda na tashi nake kuka, zuwa yanzu kuwa hawayen ma babu su. Addu'a nake ko wacce iri ce tazo min yinta nake nidai fatana ya kubuta don tabbas ba makawa rashinsa zai illata ni. Ina nan a haka sai ga Gimbiya Salma, kala batace dani ba, gaisheta nayi amma ko inda nake bata kalla ba bare insa ran zata amsa. Bansan dalili ba amma ganinta cikin nutsuwa sai yasa na sami nutsuwa nima duba ga yadda labarin son da takema Yariman nawa ya karade fada.
Can sai ga dogarai sun shigo tare da Yarima Fu'ad, wani ne yayi saurin karasowa ya bude kofar kurkukun da nake ciki. Tunda ya shigo idona dana Gimbiya Salma ke kansa, murmushi ya sakar min tayi tunanin da ita yake ta mayar sai taga idonsa a kaina. Koda ya karaso, nunawa yayi baisan ma da ita a gurin ba ya janyoni ya rungume, ban musa ba nima sai na saki kuka.
"Ya isa akoke matar sarki" ya radamin a kunne na.
Kamar sokuwa haka ta tsaya tana binmu da ido, tsanata da kishina na addabar zuciyarta, kuka ne yaci karfinta tabar wurin zuciyarta na mata suya da irin wulakancin da ya mata.Da daddare muna zaune sai gashi an kawo abincin dare amma yau wani bawa ne ya kawo ba wanda ya saba kawo mana ba. Karbar abincin nayi amma zuciyata ta kasa kwanciya da shi, dibar kadan nayi na zubar a kasa, bai tambayeni dalili ba nima bance dashi komi ba haka zalika ko kallon inda na ajiye akushin baiyi ba.
Zuwa can anjima naga bera kwance kusa da wanda na zubar a kasa, ni harma na manta dashi. Mikewa nayi na isa gurin cike da mamaki, juyawa nayi don in masa magana naga idonsa a kaina. Tabe baki yayi tare da fadin "guba ce a ciki" daga haka bai kuma cewa komai ba. Nima shiru nayi, na nemi guri na zauna."Koda bazai aureni ba to bazai auri wannan yar iskar yarinyar ba, baiwa, kaskantacciya amma Ya Fu'ad ya nunawa duniya ta fini" Gimbiya Salma ta fada tana ci gaba da kuka.
"Lele kefa kika nace sai Fu'ad har yanzu, banda haka mi zakiyi dashi yanzu da bashi da komai, baki san a wani matsayi yake ba, wanda ya rasa Kalmar Yarima har abada" Mahaifiyarta ta fada cikin sigar lallashi. Jin batace komi ba sai kukan takeyi yasa mahaifiyar ta cigaba da magana
"Ga Faruk nan tun kina karama yake sonki kuma har yanzu ba abinda ya canza. Da dane tabbas baki da miji sai Fu'ad domin shi namijin duniya ne burin kowacce mace. Kiyi hakuri ki karbi tayin soyayyar Faruk don shima ba daga baya ba"
"Alfarma daya zakimin Umma wadda ita zata nunamin tsantsan son da kikemin. Ki taimakeni ki yiwa Abba magana ya barni in auri Ya Fu'ad, nasan tabbas kikasa baki bashi da zabi" Gimbiya Salma ta fada tare da hada hannayenta guri daya alamar roko.#follow
#vote
#comment

YOU ARE READING
💞NOOR
Ficción GeneralStory of Noor and the 5 princes of Ming Empire. Betrayal among them and read as love turns to hatred.