💞 NOOR
24
Fargabar ta daya kada ace mata ta mutu don sun shaku, tun suna yara suke tare da ita. Shigar alfarma tayi sannan ta fito, kana ganinta zaka gane tana cikin damuwa sosai, tana fitowa bayi suka biyota tare da wasu dogarai bisa umarnin Sarki Ahmad, don cewa yayi indai har za'a iya dauke amintacciyar baiwar ta to itama za'a iya dauke ta ko a nakasta ta. Tana zuwa aka bude mata kofa ta shiga, iso ta nema zuwa gareshi, nan wani dogari ya shiga wata kofa Ya barsu nan tsaye don jiran iso.
Yarima Faruk na zaune yana cin abinci dogarin ya shigo
"Ranka ya dade Gimbiya Salma tana neman iso gareka"
Dago kai yayi ya kalla bawan sannan yace
"A gaya mata ina hutawa ta dawo anjima"
"To ranka ya dade"
Har dogarin ya bude kofa Yarima Faruk ya kirashi, dawowa yayi
"Dame tazo?" Yayi tambayar da yasan ba lalle bawan yasan amsarta ba.
"Daga yanayin ta a tsananin damuwa take" bawan ya fada.
"Yi mata iso" Yarima Faruk ya fada cike da isa.
A bakin kofa suka tsaya shiga tayi ta taddashi zaune yana cin kayan marmari. Kallo daya ya mata yaga kyawun da tayi, murmushi yayi tare da fadin
"Maraba da Gimbiya Salma"
Ganin yadda ya tarbe ta hakan ya kara darsa mata zarginsa a ranta. Zama tayi amma ba wanda yace kala, gajiya tayi da shirun tace "Yaya Farouk don Allah kayi hakuri da abun da nayi maka ka kyale baiwata" ta fada murya na rawa.
"Baiwar ki kuma? Ni meya hadani da ke balle ita?" Ya fada yana kallonta wannan karon.
"Nasan kai kasa aka saceta don Allah ka kyaleta" ta sake fada tana tsugunnawa bisa gwiwoyinta.
Dariya yaso yi amma ya basar kawai tare da fadin "Tashi kije zan neme ki" ya kara hade rai.
"Yaya do..." Yayi saurin katseta da fadin "nace kije zan neme ki"
Mikewa tayi jiki a sanyaye tace ta gode sannan ta fita.Tana fita ya soma dariya, duk da zuciyarsa cike take da mamakin yadda akayi tayi sanyi haka. Nayi tunanin Fu'ad kadai keda wannan tasirin a kanta amma abin mamaki har amintacciyar baiwar ta😐 tabbas tarin sirri ce baiwar nan. Dole na sameta kamin wasu su isa gareta don nasan ba ni kadai bane.Ya fada a zuciyarsa.
Wani dogari yasa a kira mishi, wanda shine yake mishi aikin sirri.
"Ka nemo duk inda baiwar Gimbiya Salma take ku kawomin ita" Yarima Faruk ya bada umarnin.
"To ranka ya dade" dogarin ya amsa.
"Zaka iya tafiya"
"A huta lafiya"
Burin Yarima Faruk bai wuce a samu baiwar nan ba, don da ita zai yi amfani da Gimbiya Salma wajen cimma burinsa.Yaya Asma'u ce tsaye ita da Yawale wanda sai binta da kallo yakeyi tare da jiran amsar da zata basa.
"Na amince" ta furta a sanyaye tare da mikewa don barin gurin.
"Nagode sosai Asma'u! In Sha Allah baza kiyi dana sanin amsarki ba, Allah shige mana gaba" Yawale ya fada yana binta da kallo harta kurewa ganinsa."Wali ka gama binciken kuwa?" Yarima Ameen ya tambaya yana cigaba da rubutun da yake.
"Eh ranka ya dade! Mutumin mahaifinsu ne amma banda ita, kawota mahaifiyar ta tayi garesa, a wannan lokacin mahaifinsa bawan mahaifinta ne, koda matsala ta tashi shi take nema"
"Amma kayi binciken mahaifiyar tata?"
"Nayi ranka ya dade amma basu fadi sunan kakan nata ba balle na mahaifiyar ta, hakan yasa ba zamu iya tabbatarwa in ita bace"
"Shikenen, ka cigaba da binciken ko za'a sami wani abun"
Wali tashi yayi ya fita.
Nan wani bawa ya shigo, gaida Yarima Ameen yayi sannan yace "Baiwa Asma'u tana neman iso, tace mag..."
"Shigo da ita" Yarima Ameen ya katse bawan.
Shigowa tayi da sallamar ta, nan ya amsa tare da fadin karaso ciki mana. Karasowa tayi ta tsugunna tare da gaidashi.
"Dama alfarma nazo nema ranka ya dade" ta fada kanta a kasa.
"Wace irin alfarma kenen?" Yarima Ameen ya tambaya.
"Dama wannan za'a bawa Noor" ta fada tare da mika mishi wani dan karamin abin katako.
Hannu yasa ya karba tare da fadin "Toh"
"Nagode ranka ya dade, a huta lafiya" ta fada.
"Allah Ya sa" ya furta.
Sallama ta mishi ta fita.
Abun ya rike a hannunshi yana jujjuyawa yana tuna inda ya taba ganinshi. Can yayi murmushi tare da fadin "Tabbas na taba ganinshi a gurin Babba lokacin ina yaro"Washegari saiga Yarima Ameen da sassafe, iso ya nema nan ya shigo. Zama yayi a daya daga cikin gujerun dakin, nan Tala ta hado kayan karin kumallo ta kawo gabanshi ta ajiye. Tashi nayi na tsiyaya mishi shayi a kofi na mika masa, karba yayi tare da min godiya. Sai da ya shanye na kofin tass sannan ya kalleni yace
"Kin tashi lafiya?"
Sai a sannan na tuna ko gaidashi banyi ba ashe.
"Lafiya lau ranka ya dade, an tashi lafiya?" na amsa da sanyayyar murya.
Murmushi yayi sannan yace "Lafiya lau"
Shayin ya sake tsiyayawa yasha. Ajiye kofin yayi sannan yace "kin sawa kanki damuwa duk kin rame"
Kallonsa nayi don tabbatar dashi yayi maganar amma banga alama ba duk da muryarsa ce.
"Na baki izinin kallo na duk da baki tambaya ba"
Murmushi nayi jin furucin nasa.
Hannu yasa a aljihu ya ciro sannan yace "gashi inji Asma'u" yayi furucin tare da mikomin wani dan katako.
Karba nayi nace "menene wannan din?"
"Nima bansani ba, cewa tayi kawai a baki" yayi furucin yana mikewa. Sallama yamin sannan ya fita.#Comment
#Follow
#Vote

YOU ARE READING
💞NOOR
Ficción GeneralStory of Noor and the 5 princes of Ming Empire. Betrayal among them and read as love turns to hatred.