💞 NOOR
27
"Zahra ki bi ta kinji, kada ki damu. Ki zama mai juriya da hakuri kada ki yadda wani ya wulakanta ki, duk abinda ta fada shi zakiyi. In Sha Allah zamu sake haduwa" matar ta fada tana kuka tare da rungume karamar yarinyar da aka kira da zahra. Can ta sake ta ta hau doki, nan yarinyar tasa kuka tare da fadin "Umma" da karfi.
Firgigit na farka daga baccin da nake bakina dauke da addu'a, su waye wannan da nayi mafarkinsu? Wacece Zahra? Na yima kaina tambayar da bani da amsarsu a yanzu. Addu'a nayi sannan na koma na kwanta, zuciyata cike da sake-sake.Washegari koda nayi sallar asubha, nan kan sallayar bacci yayi awon gaba dani.
Tala ta shigo da sallamar ta, nan ta taddani ina bacci hakan yasa ta gyara dakin farko. A nutse take aikin gudun karta tada ni, data gama ta kawo kalaci ta ajiye sannan ta fita. Bani na farka ba sai goma, nan na fada wanka da sauri, ban wani dade ba na fito na shirya, fitowa nayi na tadda Tala bata nan, ganin kalaci a gurin yasa cikina yin wani kara alamar yunwa. Akushin na bubbude nan naga farfesun nama ne, gurasa sai dahuwar kayan lambu. Farfesun na zuba naci da gurasar, kayan marmari naci nayi hamdala na mike.Tala ce ta shigo hannunta dauke da wani kunshin kaya a farin yadi mai santsi. Tunda ta shigo kamshi ya mamaye gurin wanda ya dusashe kamshin turaren da akasa a dakin. Mamaki ne ya kamani sabida ganin ta mikomin wannan kaya, na jima sannan na zauna ba tare da na amsa ba nace ta bude. Budewa tayi nan wata farar doguwar riga ta bayyana, tana dagata sai ga alkyabba ruwan zinare an kawata ta da fararen duwatsu masu daukar ido. Murmushi nayi sabida daga ganin kayan nasan daga inda suka fito.
Wata farar takarda karama ta mikomin, budewa nayi na fara karantawa kamar haka "ki saka ki sameni a lambu bayan la'asar"
Turo baki nayi ganin babu wani sallama bare ya kike, ajiye takardar nayi sannan nace ta dauke kayan.
Kai kayan ciki tayi ta ajiye sannan ta fito ta zauna dan nesa dani.
"Naga kaman akwai abinda ke daminki" ta fada cike da kulawa.
Dan juyowa nayi na kalleta ba tare da nace komai ba, ajiyar zuciya na sauke sannan nace "mafarki nayi da wata zahra"
Nan na kwashe komi na gaya mata. Jinjina kai tayi tare da fadin "Ni a ganina kaman kinsa abun a ranki da yawa ne, shiyasa kikai mafarkin"
"Haka ne" amma a zuciyata ba haka bane, sabida mafarkin ya tsaya min a rai sosai barin ma fuskar matar dana gani, wadda take kama dani.
Munanan zaune aka kira Sallah Azahar, Tala ta tashi ta fita don gabatar da sallah, nima na mike nayi ciki. Bayan na idar ne nayi ta rokon Allah akan Ya kawomin sassaucin komi cikin rayuwa ta.
Tala ce ta shigo dauke da abinci, kallo daya na mata na mata alama da hannu akan ta fita, don a wannan lokacin ina bukatar kadaici sannan banajin yunwa.Gab da la"asar Yarima Fu'ad yayi wanka ya shirya cikin shiga ta alfarma, duk inda ya gifta bayi da dogarai binsa suke da ido, wajen kuwa zai samu tukuicin kamshinsa. A haka ya karasa masallaci yayi sallah sannan ya fito ya doshi wata hanya daban ba wadda zata sadaka da cikin gidan ba.
Wanka na sakeyi nayi sallar La'asar, kayan da aka kawo na saka, sannan na feshe jikina da turaruka masu kamshi. Yar kwalliya nayi, nice harda saka janbaki😂
Fitowa nayi Tala ta biyoni, nan nace mata ta koma ba nisa zanyi ba.
Hanyar Lambu na dosa, can kasan bishiyar da nake zama na hangoshi tsaye ya juya baya, cikin shiga ta alfarma. Murmushi nayi don tuno fuskarsa da nayi, zanso na ganshi cikin shiga irin haka.
Karasawa nayi, nayi sallama cikin wata siririyar muryar da bansan ina da ita ba. Juyowa yayi, muna hada ido nan gabana ya fadi, raina ya baci amma saina dake ban nuna komai ba.
"Noor" Yarima Fu'ad ya furta a sanyaye.
Shiru nayi ban amsa ba don inna yi magana zan iya fashewa da kuka. Ni bashi naso gani ba, nayi zaton sakon da wasikar mallakin Yarima Ameen ne😒.
Katsemin tunani yayi da fadin "kinyi shiru"
Dan yatsina fuska nayi sannan nace "kaina ne ke ciwo"
Ban gama rufe baki ba yayi saurin cewa "Subhanallah! Ai da kin fadamin da baki fito ba. Sannu, muje ciki"
Wucewa nayi yana biye dani har kofar dakina sannan yace "Allah Ya sawake Noor, ki samu ki huta, zan aiko a kawo miki magana"
"To, nagode" na fada tare da shigewa ciki.Haka ya koma sashensa sukuku, kana ganinshi zaka ce baida lafiya, duk yabi ya damu da ciwon kan dana ce.
Ina shiga na cire kayan na canza wasu, Tala na kwalawa kira nace ta kwashesu ta boye inda ba wanda zai sani sai ita koni karta fadamin. Duk da na cire kayan jikina bai daina kamshinsu ba, wanka na shiga nayi na fito na dake kaya na feshe jikina da turaren da Yarima Ameen ya bani. Tala ce ta shigo da kofin silver mai murfi a hannunta.
"Sako ne daga Yarima Fu'ad yace kisha sannan ki kwanta, yana miki bangajiya da ban hakuri, Allah baki lafiya."
"Fita dashi" na fada a takaice.
Sallar Maghriba nayi na dan kwanta akan sallayar, a halin yanzu Yarima Ameen nakeson gani, bansan na kamu da sonshi haka ba. Wata baiwa na kira nace ta bani kayanta, nan na saka ta saka nawa ta hau gadona ta kwanta ta lulluba. Ba wanda zaice bani bace a kwance.
Fitowa nayi na doshi hanyar fita, na gota masu tsaron kofar kenen naji ance "ke" gabana ne ya fadi amma saina dake na juyo, nan naga wata baiwa ta isa gaban sarkin gida ta tsugunna. Ajiyar zuciya na saki ganin ba dani yake ba.
Sashen Yarima Ameen na tasamma, a bakin kofar dakinsa na tsaya. Na jima a haka sannan na tattaro jarumta ta na kwankwasa kofar, shiru ba'a bude ba kuma ace shigo ba don a wannan lokacin nasan yana ciki. Harna juya da niyyar komawa naji an bude kofar, ido muka hada da Fannah, nan ta kalleni cike da mamaki nima kallon da nake mata kenen. Ganin haka kawai na juya, ina jiyo muryarsa yana tambaya waye.#Vote
#Follow
#Comment.

YOU ARE READING
💞NOOR
General FictionStory of Noor and the 5 princes of Ming Empire. Betrayal among them and read as love turns to hatred.