💞 NOOR
29Wali ya aika a kira Fanna, ba'a jima ba sai gata ta iso, iso ya mata wurin Yareema Ameen wanda yake zaune ranshi a bace.
"Barka da hutawa ranka ya dade" ta fada tana rissinawa.
"Wacce baiwa ce tazo jiya" tambaya ta shige ba zata
Daburcewa tayi ta fara hada karairayinta. Wani kallo ya watsa mata wanda ya sata yin shiru. Rubutu yayi a takarda ya linke ya bata ta kaima Wali.
Fita tayi jiki a salube ta isa inda wali yake bashi takardar. Koda ya bude ya karanta sai yayi murmushi yace mata "Daga yau kin koma madafar cikin gida, bake ba sashin nan"
Da sauri ta tsugunna tana kuka tana rokonsa a barta a nan koda bangaren wanki ne. Tafiyarsa yayi ya barta nan tsugunne tana kuka.*****
A haka rayuwa ta cigaba da ninkawa, yau wannan gobe wancan sau kusan biyar sarkin gida na kama masu son shigowa gidanmu leken asiri ko kuma wani abun sukeson yi.
Yayinda kullum cikin zullumi da fargaba nake ganin ranar tafiyarmu Milan na gabatowa, ranan 'yanci. Yarima Fuad ne ya nema iso gareni, Tala ta gayamin nace ya shigo.
Yana shigowa ya zauna, na umurci Tala ta kawo masa kayan marmari. Koda ta kawo baici ba, sai kallona kawai da yakeyi yaki cewa komai. A raina nace yau yan mulkin na kusa kenen, kuma ina fargaban kar Yarima Fuad ya juyamin baya in muka bar nan. Nima shirun nayi ina tunani, gyaran murya yayi wanda hakan ke nuni da yana bukatan hankalina gareshi, dago kaina nayi muka hada ido na sake sunkuyar da kai.
"NOOR! Ya fada da kakkausan murya.
Shiru nayi ba tare dana amsa ba.
"In Sha Allah aurena da Gimbiya Salma washegarin 'yancinmu amma karki manta da cewa ina tsananin sonki"
Yana gama fadin haka ya mike zai fita, saida yakai bakin kofa na dago kaina nace "In kana sona har haka ka aureni mana, ko kuma kana ganin na maka kaskanci da yawa? ni baiwa ce ada, ko kuma kana ganin ban cancanta ba tunda tuwon girma miyar sa nama kuma gashinan na gani"
A fusace nayi magana, juyowa kawai yayi ya kalleni na dakiku sannan ya fita ba tare da yace komai ba.******
Koda Yareema Fuad ya koma sashensa yayi mamakin maganganu na amma shi basu dameshi sosai ba kamar ace yamin bayani akan shirinsa, ya fahimtar dani cewa bayason Gimbiya Salma.
"Burina da farincikina Noor ce" ya furta a fili.
Takarda ya dauka ya rubuta wasiqa zuwa ga Jaafar.******
Safiyar yau an tashi da ruwan sama, garin yayi ni'ima. Yareema Ameen yana zaune yana shan shayin da sabuwar baiwarsa ta hada, sha kawai yakeyi amma zuciyar sa gabadaya ta tafi tunanin Noor. Babban tashin hankalinsa tafiyata Milan, mafi girman tashin hankalinsa Yareema Fuad ya aureni in mun tafi shi yana nan. Dole ya dauki mataki da gaggawa kafin mu tafi.
Wali ya umurta da ya gaggauta nemo masa gida a garin da yafi kusa da milan. Akwai wani gari Dakari, shine yafi kusa da Milan. Cikin kwana biyu Wali ya samo gida dan madaidaici ya kyau, ya kara tsarashi sosai ya samu wanda zai kula da gidan kamin lokacin da ubangidan nasa zai bukaci amfani dashi.******
Ta bangaren Gimbiya Salma kuwa kwanakin aurenta na gabatowa tashin hankalinta na karuwa duk ta rame amma baa ganewa sosai sabida gyaran da take sha.
Tayi kyau amma kuma bata cikin walwalar ta kaman da, tunaninta daya ne Yareema Fuad, meyasa baiyi musu akan aurenta ba? Anya ba shirya mata wahala da ukuba yayi ba inta aureshi? Meyasa ta kasa bin maganar mahaifiyarta? Anya zatayi farinciki kaman yadda take tsammani a farko?
Sune tambayoyin da ta kasa bawa kanta amsarsu.******
Shiryeshirye akeyi sosai cikin gidan, dangi na kusa dana nesa duk sun hallara, kusan duka dakunan bakin ko wani sashe akwai mutane. Gimbiya Salma ta mutane ce domin akwaita da shiga rai.Tun ranar da Yareema Fuad ya fadamin maganar aurensa bansake bari mun hadu ba, ko ya bukaci iso bana bari. A bangare guda kuma ga kewar Yareema Ameen da nakeyi.
A haka Allah Ya kawomu ranar da muka sami 'yanci. Da sassafe na shirya cikin shiga ta alfarma nayi bangaren Yareema Ameen, bazan iya jira har tsahon lokacin da zaizo gareni ba. Ina fitowa t
Tala ta bani takarda na amsa na bude
""Barka da samun 'yanci rayuwata"
Sai hatimin sa a gefe. Murmushi mai sauti nayi, tabbas Yareema Ameen ina ransa a koda yaushe. Fitowa nayi Tala na biye dani, hadiman gidan sai murna suke tayani. Sashen Yareema Ameen na nufa kai tsaye, duk inda na wuce sai an bini da ido.******
"Ka tabbatar sojojin nan sunkai yawan da nake bukata? Yareema Fuad ya tambaya? Jaafar zai bashi amsa ya hango inuwar mutum bakin kofa sai ya dakata.
Kallon inda yake kallo Yareema Fuad yayi, sai yace "ko waye a kasheshi"
Barin jikin kofan akayi, Jaafar yayi saurin karasawa amma baiga kowa ba, sai yabi kofar baya ta sashen.******
"Assalamu alaika! Ya Fuad in bazamuyi farinciki ba mu hakura. Na hakura"
Gimbiya Salma ta buga hatimin ta a gefe sannan ta linke wasiqar ta mikawa amintacciyar baiwarta ta kaiwa Yareema Fuad.
Koda ta isa sashen, bayanan Mahaifiyar Gimbiya Salma ta bukaci ganinsa. Juyawa tayi da wasiqar tuna kashedin da Uwardakinta tayi mata na cewa hannu da hannu zata bashi.

YOU ARE READING
💞NOOR
Ficção GeralStory of Noor and the 5 princes of Ming Empire. Betrayal among them and read as love turns to hatred.