💞Noor
5
"Guba fa kace? Ta yaya?" Ya fada yana kallon likitan da ya gama mai bayani
Sallama likitan yayi ya tafi. Tuna maganganun likitan ya sake yi "akwai wani babban Al'amari
tattare da baiwar nan ranka ya dade domin gubar na da karfi sosai da mutum bazai rayu ba
amma abin mamaki ta galabaita matuka sai dai bata mata illa sosai ba. In Sha Allah zan dawo
gbe in sake dubata" tashi yayi ya doshi cikin gida don dolene ya ga kakansa don su tattauna."Yawwa Aliyu! Kai nake ta nema wlh," Habu dogari ya fada yana dafa Ya Ali,
"ai gani ka ganni yanzu" Ya Ali ya fada yana cigaba da aikinsa. Ganin haka yasa Habu dogari yin magana
"Don Allah alfarma nake nema, aikena akayi kuma wlh akwai aikin da Gimbiya Salma ta sani. Shine nace ko zaka taimaka ka kaimin aiken?"
Har ga Allah Ya Ali beyi niyyar zuwa ba amma abotarsa da Habu dogari ta wuce haka. "Ina sakon yake?" Ya fada yana mika hannu.
"Gashi, sashen Babba za'a kai sunsan da sakon" ya fada yana mikama Ya Ali wani dan karamin akwatin karfe.
"Nagode Aliyu don ka ceceni gurin Gimbiya Salma" Habu dogari ya fada yana washe baki.
Koda Ya Ali ya isa sashen babba, wani dogari ya bawa sakon dai dai lokacin Yarima Ameen ya fito kenen, kan idon shi aka bada sakon. Wucewa yayi ba tare da yace komai ba.
Bangaren bayi ya wuce kai tsaye ya shigo dakina kamar kullum fuskar nan tashi ba fara'a, sallama yayi ciki ciki kamar an masa dole. Cikin dakin ya karaso, Khairiyya ta yunkura zata tashi ya dakatar da ita, idonsa na kaina tun shigowarshi dakin sai yanzu ya maidasu ga Khairiyya
"Ya jikin nata?" Ya tambaya cike nutsuwa.
"Dd...da sauki" Khairiyya ta fada a dan tsorace.
Bai sake cewa komai ba ya fita daga dakin. Yana fita ba jimawa Yareema Fu'ad ya shigo dakin kamar an wurgoshi, da sauri ya karaso bakin gadon da nake ya tsugunna yana kallon fuskata datayi fayau. Rufe idona nayi ganin yaki magana kuma ya tsuramin manyan idanunsa.
"Mage" ya fada da alamun damuwa a muryarsa.
Ban bude idona ba kuma bance komi ba, hakan ya bashi damar ci gaba da magana
"Yanzu Yarima Ameen ke fadamin shi ne nazo inga jikin naki" shiru yayi na wasu yan dakiku don yayi tunanin bacci yayi gaba dani. Juyawa yayi ga Khairiyya data idar da sallah yace "Allah Ya sawake" ya tashi ya fita bai ko tsaya jin amsarta ba.
Bangaren Yareema Ameen ya nufa, ya taddashi yana duba wasu takaddu kamar kullum. Zama yayi ya sauke ajiyar zuciya mai karfi.
"Ameen don Allah in zan koma Milan kabarmin Noor in tafi da ita" Ya fada a marairaice. Jin shiru kuma sanin ba lalle ya amsa mishi ba yasa ya cigaba da fadin
"wahala take sha anan, gashi har an kusa salwantar min da rayuwar ta a banza sabida rashin tsaron dake sashen naka"
Jin maganar daya fada yasa ya dago kai yana mishi kallon reni yace "Wacece kuma haka?"
"Lalle kai dan renin wayo ne, kana nufin baka masan wadda nake magana akai ba ko me?" Yareema Fu'ad ya fada yana tsare shi da ido.
Bude baki yayi zaiyi magana wani bawa ya shigo a guje, daga ganinshi kasan cikin tashin hankali yake ya tsugunna yana cewa
"ka gafarce ni ranka ya dade amma ana nemanka da gaggawa a bangaren Babba"
"Tashi ka je gashinan zuwa" Yareema Fu'ad ya bashi ansa.
Dogarin na fita suma suka mike, sashen Babba sukayi, Kai tsaye suka shiga basu nemi iso ba. A kwance a kasa ya tadda Babba, gefe kuma ga mahaifiyarsa tana ta sharar kwalla, hakan ya tabbatar mishi da cewa ya rasu kenen. Umartar bayin akayi dasu fita, ya rage daga shi, mahaifiyarsa sai amintaccen bawan kakan nasa. Yareema Fu'ad dama ganin kowa ya fita shima ya sulale ya fice.
"Ya akai haka ta faru?" Yareema Ameen yayi tambayar yana kallon Wali (amintaccen bawan Babba)
A rikice ya fara bayani "Ranka ya dade muna zaune aka kawo sakon wani dan akwati karami, dogarin ma da aka tambaya daga ina yace ba'a fada mishi ba. Akwatin sak wanda ake kawo zuma daga Marafa ne, ganin haka na bude naga zuma ce ciki saina kawo mishi. Ya fara sha sai ya tashi yace zai shiga daga ciki shine ya fadi bakinsa na fidda kumfa, shi ne na aika a kira likita kuma a kira ka"
Jinjina kai kawai yayi, ya koma kusa da mahaifiyarsa yana lallashi. Ana haka sai ga likita ya karaso, nan ya shiga dubasa ya tabbatar da guba yasha, magunguna ya bashi tare da tabbatar musu In Sha Allah zai sami lfy.
Bayan tafiyar likita ya umurci Wali daya kira masa dogaran kofa, bayan sunzo ya umurci wanda Ya Ali ya bama sakon yace ya kirasa suzo tare, ya sallami saura.
Alkawari yayi na duk wanda yake dasa hannu a ciki sai ya halaka shi.
Ya Ali na cikin cin abincin da wata baiwa ta kawo mishi kyauta sai ga dogarai sunzo tafiya da shi. Akan idon Mimi aka tafi da shi. Bata jira komai ba ta taho gurina don ta shaida min, duk da ciwon da nakeji hakan bai hanani tashi tana rike dani ba muka nufi sashen.

YOU ARE READING
💞NOOR
Ficção GeralStory of Noor and the 5 princes of Ming Empire. Betrayal among them and read as love turns to hatred.