19

95 15 2
                                    

💞 NOOR

19

Yarima Ameen ya tambaya Balele wanda idanunsa suka firfito sai zufa yake sharewa, jikinsa banda karkarwa ba abinda yakeyi. Yarima Ameen kuwa tsaye yake jikin makeken window yana kallon waje, tunda yayi tambayar bai juyo ba tunanin irin hukuncin da zai yankewa duk wanda ya kama da sa hannunsa yakeyi.
"Ranka ya dade ni bansan komi akan wannan maganar ba" Balele ya daure ya fada.
"Ku tafi dashi kuyi masa horo mafi tsanani har sai ya fada wanda ya sashi" Yarima Ameen ya fada yana juyowa. Nan dogarai suka kama Balele tare da fita da shi. Zama Yarima Ameen yayi a daya daga cikin kayatattun kujerun dake gurin. Lemun dake gabanshi ajiye bisa tire ya zuba kadan a kofi ya kurba, aje kofin yayi sannan ya jingina cikin kujerar ya lumshe ido kamar me shirin bacci.

Yarima Fu'ad kuwa bin kofar yayi da kallo bayan na fita, mamaki yayi na yadda na nuna kamar bansan meke damunsa ba, koda yake shima bai kyauta Ya fada a zuciyarsa. Mikewa yayi don biyo bayana amma kuma sai ya fasa ya koma ya zauna yana me tunani na fuskarsa dauke da murmushi. Abincin da aka kawo masa baici ba ya bude ya fara ci, sai da ya koshi sannan yasha ruwa ya bude Qur'an din sa ya fara karantawa da muryarsa mai dadin sauraro. Dogaran dake gadin kofar tasa abin ya musu dadi dama sunsan shi me ibadah ne amma fa duk cikinsu Yarima Ameen ya fisu.

Tashi nayi na fita don zagaya gidan sabida shima babba ne ba karami ba amma bai kai sashen Yarima Ameen ba, murmushi ne ya kufce min dana tuna wannan fuskar tasa da murmushin sa wanda sai shekara shekara😂. Lambun dake sashen na shiga wani ni'imtaccen iska me sanyi ta dake ni, lumshe ido nayi ina shakar iskar ina jinta har cikin raina. Shuke-shuke ne kala-kala su lemo, ayaba, gwanda, kwakwa, mangoro, ruman da sauran su, wata bishiya babba na hango wadda ta dauki hankalina, fulawoyi ne farare a jikinta duk sun bude. Karasawa kasanta nayi na zauna tare da daukar daya daga cikin fulawoyin da suka fado, shinshina nayi naji kamshinta ne dadi. Nan na cigaba da zamana sabida na gaji da zaman dakin, jikina ciwo yakeyi sabida tsabar kwanciya.

Yarima Ameen da zama ya taso dan yazo ya sake dubani, yana shigowa gidan dakin da nake ya tasamma. Dakin ya shiga ya tadda bana nan amma hakan bai hanashi zama ba. Turaren da nayi amfani dashi ya gani akan gado, dauka yayi ya shaki kamshin tare da sakin wani kayataccen murmushi. Zamansa ya cigaba dayi don ya jira dawowa ta.

Tashi nayi na dawo cikin gidan, a hanya na hadu da Tala wadda taga shigar Yarima Ameen dakin kuma ta tambaya masu tsaron kofar sunce yana ciki bai fito ba. Mamakine ya kamani, amma kuma ina fargabar kar Yarima Fu'ad ya taddashi dakin kamar dazu don nasan dole zaizo. Sauri nayi tayi har na karasa dakin na shiga, a kujerar dake gefen gadon na ganshi zaune yana kallona. Gaidashi nayi amma maimakon ya amsa sai cemin yayi "Ba'a koya miki sallama bane"
Tsabar sauri ma ni shaf na manta banyi sallama ba dazan shigo, fita nayi na sake shigowa da sallamata, amsawa yayi hade da tabe baki sannan yace "Kin warke kenen"
"Eh" na amsa a takaice.
Bai kuma cewa komi ba, ganin bashi da niyyar tashi ya sani cewa "Zan koma akwai abinda nakeyi a waje dama Tala ce ta fadamin kazo"
"Baki iya karya ba" ya bani amsa.
"Da gaske nake fa" na fada cike da shagwaba wadda ni banma san nayi ba.
Murmushi yayi baice komi ba, mun dade a haka ba wanda ya sake cewa komi.
"Kina da kamshi, inason kamshi" na tsinkayo muryarshi wanda hakan yayi daidai da shigowar Yarima Fu'ad.
Kallona ya tsayayi da alama yaji me Yarima Ameen ya fada, ji nayi jikina yayi sanyi sabida kallon da yamin. Fita yayi ba tare da yace komai ba.
Sautin murmushin Yarima Ameen ne ya dawo dani tunani na. Tashi yayi shima ya fita, yana fita nabi bayan Yarima Fu'ad don dole inje biko😁.

Yarima Fu'ad na fita Shugaban Hadiman cikin gidan nasa yasa aka kira masa, nan ya bada umarnin kar a kuma barin Yarima Ameen ya shigo gidan baki daya. Daidai dogarin na fitowa ni kuma ina shiga, zaune na tadda shi ya zuba ruwa a kofi zai sha, ko sallamar da nayi ma bai amsa ba balle na sa ran zai kalleni. Zama nayi hade da fadin "Wallahi ba abinda kake tunani bane"
Baice komi ba sai murmushi da yayi yana fadin "Karki damu bana iya fushi dake Noor."
Jikina ne yayi sanyi jin kalamansa don banyi zaton haka zakace ba.
"Godiya nake" na fada ina mikewa.
"Saurin me kikeyi haka? Ai kya tsaya muyi hira" ya fada yana sakin murmushin sa mai kayatarwa.
Komawa nayi na zauna ba tare da nace komai ba.
"Ina sonki Noor" Maganar ta daki kunnena. Saurin dago kaina nayi aiko muka hada ido, gabana ne ya fadi amma na kasa tantance me nakeji game dashi kansa ba kalamansa ba. Tabbas ina cikin rudani.

Amintacciyar baiwar Gimbiya Salma ce ta shigo sashen da saurinta, dakin da Gimbiya Salma take ciki wadda take zaune tana shiryawa don zuwa dubo masoyinta Yarima Fu'ad ta shiga.
"Lafiya kika shigo ba ko sallama"? Gimbiya Salma ta fada tana dubanta.
"Amin afuwa ranki ya dade sha'afa nayi" baiwar ta fada tana tsugunnawa.
Tsaki Gimbiya Salma tayi sannan ta tambayeta aiken da tamata.
"Ranki ya dade ina isa na tadda Yarima Faruk ya aiko kiransa" ta fada a sanyaye.
Mikewa Gimbiya Salma tayi fuskarta na nuna tsananin tashin hankali, hanyar fita a dakin tayi yana fadin biyo ni, binta baiwar tayi da sauri.

Dogarin da Mahaifin Yarima Faruk ya saka ya dinga sanya mishi ido akan Balele ne ya rubuta takarda ya bawa wani dogari yace masa ya hau doki maza ya tafi kai masa wasikar.

Koda labarin kama Balele ya isa kunnen Yarima Faruk ba karamin tashin hankali ya shiga ba. Nan ya fara tunanin yadda zaiyi ya hana Balele fadar wani abu.

Pls
#Vote
#Follow
#Comment

💞NOORWhere stories live. Discover now