💞 NOOR
17A daren Barde ya turo wasu dogaran aka kara tsaro bisa umarnin Sarki Ahmad. Dakin da nake Yarima Fu'ad ya shigo don duba halin da nake ciki kamin ya kwanta, ya jima zaune sannan ya fadawa Tala data kiyaye bada magani da kuma wajen kula dani. Koda ya fito ya tadda dogarai biyu bakin kofar umarni ya bayar akan wasu biyun su karu.
Koda ya koma dakinsa bacci ya kauracewa idonsa sai juyi yake a gado. Tashi yayi ya dauro alwala, ta tada sallah, daya sallamar ya sake tadawa har saida yaji ya samu nutsuwa sannan yayi addu'o'i. Yana linke sallayar ne yaji motsi, isa yayi bakin window ya leka daidai lokacin kuma yaga giftawar mutum, yayi tunanin ko dogarai ne suke zagaye amma hankalinshi yaki kwanciya da hakan. Tashi yayi ya fito riqe da takobinsa nan ya tadda dogaran kofarsa tsaye, tambayar sa sukayi ko da wani abu yace babu yana wucewa, biyosa sukayi yace su koma sannan yayi sashen dakin da nake. Yana zuwa ya tadda dogaran duka su hudun suna bacci da alama wani abun aka musu, saurin bude dakin yayi wanda ya bayyana wani mutum cikin bakin kaya ya saita takobinsa saitin kirjina, ga Tala itama a gefe da alama baccin aka sata koma ya kashe ta. Jin an bude kofar yasa mutumin juyowa amma fuskarsa a rufe take, nan yayo kan Yarima Fu'ad da niyyar kasheshi amma da alama baisan ko wanne shi ba don Yarima Fu'ad jarumi ne, duk wani yaki mahaifinsa dashi yake zuwa. Nan suka shiga fafatawa har Yarima Fu'ad ya yanke shi a hannu, dogaran dake waje kuma jin karan takobi yasa suka garzayo don su duba. Jin alamun gudu na tunkaro inda suke mutumin yayi ture Yarima Fu'ad yayi baya shi kuma ya tasamma window don guduwa, daidai zai dirga Yarima Fu'ad ya yanke shi sosai a baya amma duk da haka sai da ya gudu. Dogarai na karasowa ya nuna musu window nan suka bi bayanshi, ganin sign jini a kasa yasa suka nemo fitilu suna bin digon har suka je bayan fadar, nan suka tadda kayan mutumin alamun canjawa yayi. Dawowa sukayi bakin gadona suka taddashi, nan suka shaidawa Yarima Fu'ad abinda ya faru, shiru yayi na dan wasu mintuna kamin yace "Duk inda yake bazai kai gobeba don na yanke shi sosai"
Nan suka tafi da niyyar binciken Masarautar da kewaye.
Sai yanzu hankalinshi ya kai ga Tala dake kwance nan yasa wani bawa ya watsa mata ruwa, nan ta farfado tana sauke ajiyar zuciya akai-akai.
Yarima Fu'ad na nan zaune bakin gadon har bacci ya daukesa bai sani ba.Cikin daren wani bawan Yarima Ameen ya shaida mishi abinda ya faru, a haka ya fito zuwa sashen ba tare da ansan da fitowar tashi ba. Yana isowa bakin kofar dakina dogaran suka bude mishi, kasa shiga yayi ganin Yarima Fu'ad zaune idonshi a rufe. Juyawa yayi yana jin wani yanayi shi ba bacin rai ba amma ya kasa gane menene. Kishi! Wata zuciyar ta fada mishi. "I'naah" ya fada a fili. Yana komawa sashen nashi ya shiga daki ya kwanta amma bacci ya kaurace mishi, yana nan a haka har aka kira Sallah.
"Sale ya karasa maboyar amma ya mutu" wani bawa yake shaidawa Balele. Nan ya tashi tsaye yana huci rai a bace ba tare da yace komai ba ya fice wasu suka rufa mishi baya. Can karshen Masarautar suka nufa, yana dosar maboyar ya tadda dogarai a bakin dakin. Juyawa sukayi ya nufi Sashen Gimbiya Salma hankalinshi a mutukar tashe.
A hanya yaci karo da ita ta fito shawagi amma kana ganinta kasan hankalinta ba'a kwance yake ba don yanzu labari ya iso mata cewa mahaifin nata yasa ayi bincike a kama duk wani wanda sunansa ya fito ko da gangan ne koda kuma waye. Kallon Balele tayi a wulakance tayi nuni da tana bukatar sirri nan hadimanta suka matsa aka barta daga ita sai shi.
"Basai kace komai ba, kasan hukuncin ka in kayi kuskure ai" ta fada cike da izza
"Tuba nake ranki ya dade, Allah Ya huci zuciyarki" ya fada murya na rawa.
"Ka karba sako gurin amintacciyar baiwa ta, inason ka bar garin nan nan bada jimawa ba, kayi nesa har sai na neme ka" ta fada tana juyawa.
"Godiya nake ranki ya dade" ya fada yana karasawa gurin amintacciyar baiwar ta ta.
Tabbas ba haka yaso ba amma bashi da zabi don yasan abu daya ne ya hanata kasheshi wato gudun abinda zai biyo baya"Bayan gari ya waye Yarima Ameen ya nufi cikin gida bangaren Sarki Ahmad, nan yasa jakadiya ta mishi iso. Da sallamar sa ya shiga, nan ya gaidashi ya amsa. Shiru ne ya biyo baya har saidai Sarki Ahmad ya nisa yace
"Fadi meke tafe dakai Ameenu" Sarki Ahmad yace yana gyara zama.
"Baffa dama so nakeyi binciken harin da aka kaiwa su Fu'ad ya dawo hannuna" ya fada yana kasa da kai.
"Shikenen" ya fada a takaice.
"Godiya nake ranka ya dade" yayi mishi sallama ya fita.
Sashen Yarima Fu'ad ya nufa, yana zuwa yasa a tattaro mishi dogaran dake tsare da gidan, nan ya shiga tambayarsu daya bayan daya daga bisani ya nufi can inda aka tsinci gawar Sale.Yarima Fu'ad kuwa ana kiran sallah ya farka, ganinshi bakin gadona yasa shi saurin mikewa ya nufi dakinsa don yayi alwala ya tafi masallaci. Sai da gari ya fara sha sannan ya baro masallacin, yana shigowa zuwa yayi ya fara dubani sannan ya koma dakinsa ya kwanta.
Yarima Ameen kuwa daga bayan masarautar dawowa yayi gidan Yarima Fu'ad, yana shigowa dakin da nake ya shiga, nan ya zauna bakin gadon. Kuramin ido yayi na wani lokaci sannan yasa Tala ta kawo mishi ruwa a kofi, da sauri ta fita sai gata ta dawo dauke da ruwan. Karba yayi ya fara addu'a a ciki, ya dade yana karanto addu'o'i sannan ya gama, mikawa Tala yayi yace ta shafamin a jiki da fuska. Karba tayi ta shiga shafamin kamar yadda yace, bayan ta gama ta fita don mayar da kofin. Riqo hannuna yayi, ya kasa fassara yanayin da yakejin zuciyarsa ciki, tabbas yana tausayi na amma son ne ya kasa gasgatawa, sakin hannun nawa yayi ya mike don barin dakin. Tsayawa yayi cak sakamakon........
#Vote
#follow
#comment

YOU ARE READING
💞NOOR
General FictionStory of Noor and the 5 princes of Ming Empire. Betrayal among them and read as love turns to hatred.