💞 NOOR
20
Koda Gimbiya Salma ta fito daga sashen nata nan take jin labarin kama Balelen, bata zarce ko ina ba sai kurkukun masarautar tasu ta Ming. Tana shiga tasa a nemo mata shugaban masu kula da kurkukun, yana zuwa ta nemi ganin Balele, bai musa ba don bai kawo komi a ransa ba. Tana zaune ya tura wasu dogarai su taho da Balele, basu wani jima ba sai gashi tafe yana biye dasu hannunshi da kafafunshi duk ansa masa ankwa, kamanninsa har sun fara canjawa don ba karamar azaba yasha ba a dan lokacin da bai wuce awa daya ba. Tunda ya fito gabanta ke faduwa, sai addu'a take kada ya furta ko kalma daya gaban su balle su zarge tasan wani abu. Kallon su tayi sannan cike da kasaita takai dubanta kan baiwarta tana fadin
"Ina bukatar sirri" duk fita sukayi amma baiwarta ta tsaya bakin kofa sabida gudun 'yan labe.
Kallon Balele tayi wanda haushinsa takeji kaman ta shakeshi sannan tace "Tambaya daya zan maka kuma amsa daya nake bukata"
Baice komi ba sabida a wahale yake. Ganin haka ya sata cigaba da magana "Wa yasa ka kashe Yarima Fu'ad da Noor?"
Saurin dago kanshi yayi cike da mamaki, yasan me take nufi da fara kiran sunan Yarima Fu'ad kamin na Noor din, wani miyau me daci ya hadiya zufa na karyo mishi, wannan shine hanya da zata kubutar da shi, da yayi karya yasan abinda zata iya aikatawa.
"Yarima Faruk ne" ya fada kai tsaye.
Mikewa tayi cike da tashin hankali, Yarima Faruk, Faruk fa? Duk yadda suke da Fu'ad? I'naah bazai yiwu ba, duk ita kadai take zancenta a zuciya. Amma sanin cewa Yarima Faruk yana sonta sosai ita kuma Yarima Fu'ad takeso kuma ya sani yasa mamakin da take ya tafi. Zama tayi sannan ta saki wani malalacin murmushi sannan tace "Lokaci yayi da zan nunawa Yarima Faruk bambancin mu"
Ta fada tana mikewa don barin wajen, tana fitowa aka shiga aka maida sa. Bata damu da kin yima Balelen gargadi akan karya fadi komi ba, ita tasan me zatayi.Sashen Yarima Fu'ad ta isa, muna tsaka da hira sai ji mukayi ana nema mata iso, kallona Yarima Fu'ad yayi sai kawai na tsinci kaina da yin murmushi sannan na daga masa kai. Shigowa tayi kaman an turota amma da sallamar ta, amsawa mukayi. Nan ta gaida Yarima Fu'ad cike da shagwaba, ban damu ba don nasan bata ita yake ba. Gaidata nayi amma ta nuna ma bataji ba, fuskar Yarima Fu'ad ce ta canja nan yace mata "Bakiji Noor na gaidaki bane"
"Banji ba!" Ta fada tana dan kallo inda nake zaune. Can ta muskuta sannan ta kafeni da ido tana fadin "Ina bukatar ganawa da masoyina"
Murmushi na sakar mata jin kalar tata wautar sannan nace "Lokacinsa duk naki ne ranki ya dade" sannan na tashi na fita, inajin idanunsa akaina.Daki na shiga amma bani da abinyi don haka ganin Maghriba ta gabato ya sani dauro alwala na zauna azkhar din yammaci. Bayan anyi sallah ne Tala ta shigo ta kawomin abinci lokacin ina karatun alkur'ani, nan ta zauna tana sauraro har na idda karatun. Nan na tambayeta an kaima Yarima Fu'ad abinci kawai don son jin ko Gimbiya Salma na nan ko ta tafi.
"Eh ranki ya dade! Abincin mutum biyu aka aiko mu kai" ta amsa.
"Bako yayi kenen?" Na sake tambayar ta.
"Shi da Yarima Haisam ne ranki ya dade"
Wata ajiyar zuciya nayi wadda bansan dalilin ta ba. Abincin na fara ci, kadan naci naji na koshi sai na dauki madara me zafi a kofi na shanye abu na.Sarkin wambi ne zaune gefe kuma matarsa ce mahaifiyar Yarima Faruk, kallo daya zaka mata ka hango tsananin kamarsu da Yarima Faruk din. Murmushi tayi tana ajiye kofin dake hannunta sannan ta fuskanci mijin nata tace
"A ganina ya kamata ace Faruk ya dawo gida, na kasa gane wannan aiki da kace yana maka a Ming"
Ta fada cike da kewar dan nata, har ga Allah ta gaji da wannan uzurin da mijin ke bata kan dan nata, kwatakwata hankalinta bai kwanta da hakan ba.
Murmushin su na manya yayi sannan yace
"Uwargida ran gida! Banda ke da abinki dan naki ai ya kusa dawowa. Bazai sake nisa ya dade har haka ba sai dai in wani muhimmin abu ne, kiyi hakuri"
Nan yayi ta lallashinta akan tayi hakuri ya kusa dawowa.Tunda naga anyi sallar Isha kuma ba Yarima Ameen ba labarinsa nasan ba zai sake shigowa ba watakila sai gobe. Ina nan zaune da Tala muna yar hira har Yarima Fu'ad ya shigo ya mana sai da safe, banyi mamakin kin cewa komi game da Gimbiya Salma da yayi ba ganin ko shigowa baiyi ba diga bakin kofa Ya tsaya.
Washegari bayan na tashi Tala take shaida min cewa Yarima Fu'ad yace akai abincina sashen sa tare zamu karya. Nikam ba haka naso ba amma ba yadda na iya. Dama nayi wanka, kaya na canja zuwa wasu farare, ba abinda na shafawa fuskata haka na fita na nufi Sashen nashi. Ina shiga bakina dauke da sallama ya amsa can na hangoshi zaune bisa kilisa ga abinci kala kala an aje mana. Zama nayi na gaidashi ya amsa yana tambaya ta ya jiki nace na warke fa. Babu wanda ya sake cewa komai muka fara cin abincin cikin kwanciyar hankali, ina ankare da shi duk wani motsina a idonsa nakeyi duk sai naji na takura, ban wani koshi ba na tashi nace na koshi tare da mishi sallama na miki.
"Cin abincin nan ya tunamin zamanmu na kurkuku duk da nan ma ba bambanci" ya fada yana murmushi.
Murmushin na mayar masa ina fadin "Komi me wucewa ne" sannan nasa kai na fita."Kayi hakuri ranka ya dade amma Yarima Fu'ad yace karmu sake bari ka shiga in ba haka ba a bakin ranmu" Dogarin ya fada yana kallon Yarima Ameen.
Wani kallo da Yarima Ameen ya masa ya sa shi matsawa daga bakin kofar. Shiga Yarima Ameen yayi, kai tsaye ya tasamma dakin Yarima Fu'ad. Karo naji nayi da mutum nayi saurin dagowa muka hada ido da Yarima Ameen."A kiramin Yarima Faruk yanzu" Gimbiya Salma ta umurci wani bawanta.
Fita yayi da sauri, ya dan jima sai ga wata baiwa ta shigo, nan ta gaya mata isowar Yarima Faruk din. Fitowa daga dakin tayi ta tadda shi zaune bisa kujerun dake wajen, taku take cike da izza har ta isa ta zauna.#Follow
#Vote
#Comment
YOU ARE READING
💞NOOR
Narrativa generaleStory of Noor and the 5 princes of Ming Empire. Betrayal among them and read as love turns to hatred.