8

113 13 0
                                    

💞 Noor
      
        8

Tsaye nake a bakin kofar tunda ya aika nazo ina jiran iso, gashi ba halin in tafi. Ina nan tsaye sai ga Yarima Fu'ad ya shigo kaman an jefo shi, yana ganina ya saki murmushi tare da rage saurinsa har ya karaso gurina.
Ajiyar zuciya ya saki tare da murda kofar ya shiga, ina iya jiyo duk maganar da suke akaina, Yarima Fu'ad dai ya nace akan lalle sai ya bashi ni shi kuma ya dage akan lalle sai in har na yadda zan bishi shi kuma ya mishi alkawarin barinshi ya tafi dani.  Da haka ya fito, dap dani ya tsaya nayi saurin yin baya ya, riko hannuna yayi ya fara tafiya nikam na tirje, juyowa yayi yamin wani mugun kallo hakan yasa ni yin kasa da kaina. Cigaba yayi da tafiya rike da hannun nawa har sai da mukabar sashen sannan ya tsaya tare da sakin hannuna.
"Dago kanki" ya furta a umurce
Kallonsa nayi fuskar nan ba yabo ba fallasa, kafeni yayi da ido nayi kasa da nawa.
"Noor" ya fada a sanyaye, da sauri na dago na kallesa sabida jin sunana a bakinshi, murmushi yamin
"Don Allah ki bini Milan, ni kuma na miki alkawarin 'yanci na har abada ke da duk wani makusancinki"
Shiru nayi ina tunani, ya cigaba da cewa "Ameen ya riga daya amince amma yace dole sai da amincewar ki, na baki zuwa jibi kiyi tunani sabida nan da kwana uku zuwa hudu zamu wuce"
Sai a sannan nayi magana "Nagode ranka ya dade, kamar yadda ka fada zan yi tunani in sanar da kai zuwa jibi"
Da haka na wuce banko sake waiwayowa ba, ya dade a tsaye inda na barshi kamin daga bisani ya tafi.

Sallah naje na gabatar kamin na koma bakin kofar na sake magana, sai sannan ya bani damar shiga. Zaune yake ya tankwashe kafa yana rubutu akan karamin teburin dake gabanshi, fuskar nan tasa kamar kullum ba fara'a. Tsugunnawa nayi daga inda nake , dagowa yayi ya kalleni tare da cewa "Kawomin shayi, kada ya cika zafi kuma kada ya cika sanyi"
"To ranka ya dade" na amsa tare da ficewa.
Shayin na kawo kamar yadda ya umurta na ajiye a gefe tare da tsiyaya mishi a kofi na mikamai. Kin karba yayi na ajiye a gefe amma ban tashi ba. Nuni yamin da wani kofi dake gefe, na tashi na dauko, shayin ya umurceni dana zuba, zubawa nayi na mikamai. Bai dago ba sai cewa yayi "sha" ba musu na kai kofin bakina, ban cire ba sai da na shanye, sai lokacin ya dauki nashi shayin ya fara sha.

Koda su Yarima Faruk suka fita nan yaga tawagar mahaifinsa zasu shigo fada, sauka yayi daga kan dokin ya karasa gurinsa ya mika gaisuwa. Gefe sukayi shi da mahaifin nasa, nan yake shaida mishi abinda ya kawosa Masarautar, baice komi ba amma ransa a bace yake, sallama yama mahaifin nasa ya bar gurin. Murmushi ya kakalo sabida kar sauran su fahimci akwai wani abu, dokinsa ya hau ya kada sukai gaba.

Iso aka yiwa sarkin wambi gurin Sarki, shiga yayi ya shiga mika gaisuwa tare da dadin baki. Tsurutsuru yayi da ido kamin ya fara magana
"Allah Ya ja zamaninka dama abinda yasa nazo da kaina ba aike ba sabida maganar me mahimmanci ce, amma ni kaina tsoron fadar ta nake ranka ya dade"
Sarki Ahmad ya gyara zama yayi tare da yar dariya yace "Haba Zannun har akwai abinda zai tsoratar da kai? Fadi koma menene ina jinka"
"Ranka ya dade abin ne da mamaki wai ace har kaman Sarkin Milan ya isa cin dunduniyar ka , ya ha'ince ka, dadin dadawa ma so yake ya zama Sarkin Daular Ming wadda wannan kuma kujerarka ce ranka ya dade. Allah ya huci zuciyarka Sarkin sarakuna"
Shiru sarki yayi baice komai ba, jin yayi shiru yasa fargaba da tsoro suka cika zuciyar sarkin wambi.
"Wace shaida kake da ita akan zancenka?" Sarki ya fada da alamar bacin rai a maganarsa.
"Barde shima shaida ne, sannan rank ya dade duk yabi sauran masarautun yama bayi alkawarin 'yanci muddin ya zama  Sarkin Daular Ming. Ya tara sojoji masu yawan gaske ya fake dana tsaron matsaya ne"  sarkin wambi ya fada yana huhhura hanci shi a dole anyiwa Sarki Ahmad ba dai dai ba.
"Kashi kaje zanyi bincike akai, in har na kamashi da laifin hakan to zuri'arsa gaba daya zasu hallaka, in bashi da laifi to hukunci zai hau kanka"  Sarki ya fada da kakkausar murya.
Jiki a sabule sarkin wambi ya mishi a huta lfy kana ya fita.

Ina nan zaune ya gama shan shayinsa ya cigaba da rubutun sa. Nayi tsammanin ma ya manta dani a gurin har saida aka kira Maghriba sannan yace na tashi. Dakina na wuce nayi sallar, ina idarwa na fito da sauri sabida in samu in gana da Yaya Asma'u. Dakinsu  Mimi na shiga nayi sa'a ko suna nan, tare da su mukaje gurin Yaya Asma'u, muna zuwa ta rungume mu sannan ta jamu can gefe muka zauna. Yadda mukayi da Yarima Fu'ad na zayyana musu, nan nace musu shawara nake nema.
Yaya Asma'u kam sa yanzu tayi magana "Noor kinsan dai umarni ne daga mahaifin mu cewar mu kula dake da duk abinda kikeso. A ganina Yarima Fu'ad  ba zai taba cutar ki ba sabida duk alamu sun nuna shi mai sonki ne. Amma ke wani hukunci kika yanke?"

#vote
#comment

💞NOORWhere stories live. Discover now