💞 NOOR
3Tashi nayi jiki a sanyaye idanuna cike da kwalla, kasa nayi da kaina ganin ya tsareni da idanu.
"Dauko takarda da alkalami ki biyo ni" ya fada yana bin wata wata kofa. Daukowa nayi na fita, lambu ne a gurin amma diga gefe an gyara gurin da kilisai dasu tum-tum ga rumfar kuma data kara kayata gurin. Yana gishingide jikin wani tum-tum da fruits a gabanshi, karasowa nayi na tsugunna. Littafi ya mikomin yana cewa "kwafeshi zakiyi tas na baki zuwa dare" nayi saurin cewa "to ranka ya dade" tashi nayi da niyyar tafiya inyi rubutun ya dakatar dani ta hanyar daga hannunsa, na tsaya yace "Ki zauna anan kiyi" badan naso ba na dawo na zauna.
Rubutu na nakeyi kurum amma hankalina baya gurin, burina kawai in hadu dasu ya Ali kamin gobe don in gaya musu shirin da nayi.
"Mage" shine abinda ya katse min tunani na nayi saurin dagowa Inga me maganar idona suka sauka akan fuskar Yarima Fu'ad daya zubamin ido yana kallo na.
"Barka da isowa Yarima Fu'ad" nayi sauri cewa
Dariya yayi yana cewa "ashe ke jaruma ce bansani ba, ai kamata yayi ace ni na karbeki ba Ameen ba" ya fada yana kallon Yarima Ameen wanda ko alamun yasan damu bai nuna ba.
"Zaki dawo hannuna daga yau, tashi ki dauko kayanki maza" Yarima Fu'ad ya fada kai tsaye. Sai sannan ya dago ya kallemu, kawar da kai yayi yana cewa
"duk bayin dake bangaren ka basu isa bane insa a karo maka?"
Murmushi Yarima Fu'ad yayi sannan yace " Sun isa kawai kari nake nema"
Yarima Ameen yace " Gata nan ai"
"Biyo ni" Yarima Fu'ad ya umurta
Kasa tashi nayi sai da ya sake maimaitawa na tsugunna ina cewa "tuba nake ranka ya dade"
Ya fara tafiya na tashi nabi bayansa kenen na tsinkayo muryar Yarima Ameen yana cewa "Kina kara taku a bakin ranki" cak na tsaya tare da juyowa na tsugunna bance komai ba. Yarima Fu'ad kuwa dariya yayi yayi gaba abinsa.
Tun dazu nake a tsugunne duk kafafu na sun sage, har aka kira Maghriba ina nan a haka. Tashi yayi yana tafiya kaman bazai taka kasa ba yayi tafiyar sa ya barni nan. Kwashe komi nayi na tafi don inyi sallah in karasa rubutun daya sani, hankalina duk a tashe yake don nasan ko kwatan littafin bazan kaiba zai karba.
Ina shiga bangaren na hadu da wata baiwa tace na biyota ta nunamin dakina. Bangaren bayi muka nufa, ta kaini wani daki da yake ware ba jerin sauran dakunan ba. Dakin babba ne, da gado da duk wani abin bukata. Alwala nayi, nayi sallah.
Bangaren Yareema Ameen na nufa don na kai mishi shayi, in kuma yi gyare-gyare. Na kusa karasawa naji muryar Fannah tana magana da wata
"ki tabbatar kin bata ta kai mishi kinga ita zaa kashe ace ta nemi kasheshi ke kuma sai a maidoki madadinta. Umarni na baki kamar yadda aka bani nima, kar kuma sunana ya fito"
Gabana ne ya fadi jin abinda tace, don na gane muryar Ladi ce, amintacciyar baiwar Sarauniya Bintu Mahaifiyar Yarima Kassim. Fannah ce ta katse min tunani ta hanyar cewa "Na miki alkawari zan aikata yadda kika ce amma nima wata zan bawa ta mika mata banaso a sami matsa"
"Shikenen amma ki tabbatar wadda kika sa din zata yi kuma kada sunana ya fito don bansanki ba" Ladi ta fada. Labewa nayi har suka wuce. Shiga bangaren nayi kai tsaye shayi na hada na kai masa yana zaune yana duba wasu takardu.
"Ranka ya dade ga shayi" na fada a sanyaye, daga hannu kawai yayi, na tashi na tafi. Sallama wata baiwa dauke da kaskon turaren wuta a hannunta, amsawa nayi , tace "gashi turare ne kullum ana sawa a parlour a wannan lokacin, ga turaren " ta mikomin wani abu a leda. Karba nayi na juya zan tafi tacemin "in kin saka don Allah ki taimaka ki tayani wani aiki a kitchen"
nace "to bara inzo"
"Zan jiraki ma ki fito " ta fada tana jingina da bango. Bance komi ba na wuce ciki. Wasu turarurrukan na gani na iba na saka na fita. Na hannu na boyeshi nayi a jikina.
Tayata aikin nayi a kitchen nama manta da rubutun da ya sani. Sai gurin 10 na tafi don in tambaya koda abinda yake bukata. Sallama nayi na Shiga nayi na taddashi a inda na barshi, karasawa nayi na tsugunna tare ta fadin "Ranka ya dade ko akwai abinda kake da bukata a kawoka?" Alama yamin da hannu in tafi, tashi nayi na fara tafiya naji ance "Ke"
Dawowa nayi na tsugunna "gani ranka ya dade"
"Ina aikin da nasa ki?"
"Na shiga uku" na fada a zuciya. Hawaye ne ya fara ambaliya a fuska ta nace "Allah Ya huci zuciyarka, kayi hakuri don Allah wlh aiki aka samu ban karasa ba, Don Allah kayi hakuri, a shirye nake in karbi hukunci na"
Ya dade kamin yayi magana "Duk wanda ya saki aiki kice na hanaki wani aiki Inba na bangaren nan ba. Sannan gbe ki tabbatar kin kawo aikin dana saki"
"Godiya nake ranka ya dade, In Sha Allah gbe zan kawo"
Ganin naki tashi in tafi yasa yamin nuni da hannu in tafi.*THE CIRCLE*
YOU ARE READING
💞NOOR
General FictionStory of Noor and the 5 princes of Ming Empire. Betrayal among them and read as love turns to hatred.