21

137 19 3
                                    

💞 NOOR

         21

Cikinsu ba wanda yace komai, ganin bata da niyyar magana yasa Yarima Faruk mikewa don barin wajen.
"Dakata" ta fada a karaje.
Mamaki ne ya kama Yarima Faruk, idan yaji daidai kamar umurtarsa take, Gimbiya Salma ce fa 'yar Sarki Ahmad na Ming wata zuciyar tace mishi. Ranshi in yayi dubu ya baci amma haka ya daure ya koma ya zauna.
Bata gama shayar dashi mamaki ba sai da yaji tace
"Ina ganinka haka ashe kura ce da fatar rago" ta fada tana yatsina tana karkada kafa.
"Bangane ba" ya fada yana hade rai.
Dariya tayi sannan tace "Kisan Yarima Fu'ad da Noor da kasa ayi" ta fada tana kashe mishi ido daya.
Ba karamin kaduwa yayi da jin furucin ta ba amma dake namijin duniya ne sai yayi bakam harda 'yar dariyar sa sannan yace "Bansan maganar da kikeyi akai ba"
Yana fadin hakan ya mike yayi ficewarsa.
Binsa tayi da ido tana mamakin taurin kai irin nashi amma da kanta zatasa ya fada laifinsa da kansa a gaban kowa.

"Sannu da fatan ban bigeki da yawa ba" Yarima Ameen ya fada yana kallona.
"Ban bige ba" na fada tare da sa kai zan wuce. Shan gabana yayi sannan yace "Dago kanki ki kalleni"
Har ga Allah bazan iya kallon idanunsa ba amma kuma bazan iya mishi musu ba, tsintar kaina nayi dayin yadda yace din. Muna hada ido nayi saurin rintse nawa sakamakon wani abu da naji yana shiga jikina ta kallon da yake min.
"Bude mana" ya fada da wata iriryar murya.
Kin budewa nayi sai jin saukar iska da nayi a fuskata, iskar bakinshi ce ashe yake huramin. Ta gefen sa nabi na wuce harda dan gudu na. 
Karasawa gurin Yarima Fu'ad yayi ba tare da an mishi iso ba ya Shiga. Yarima Fu'ad dake gishingide tashi yayi ya zauna yana mamakin yadda akayi ya shigo, amma daya tuna kaf Masarautar babu wanda ya isa ya hanashi abinda yayi niyya yasa ya cire mamakin hakan.
"Fu'ad kayi kuskure, amma zan maka afuwa kasancewar wannan ne na farko. Bana bukatar sake ganin faruwar hakan don hukuncin bazai maka dadi ba" yana gama fada ya juya.
"Ameen kaine kake neman min shisshigi a rayuwa ta, wanda bana bukatar hakan" Yarima Fu'ad ya fada tare da mikewa tsaye.
"Abinda yasa nake zuwa nan dole in biyo Haske na" Yarima Ameen ya fada tare da bude kofar yana ficewa.
"Zaka sha mamaki Ameen! Zakayi dana sanin sanin wannan Hasken don tabbas sai ya dawo maka duhu"
Yarima Fu'ad ya fada yana zagaye dakin.

Yaya Asma'u yau tunda ta tashi komai sukuku takeyin shi, walwalar ta ba kamar kullum ba kuma hakan baya wuce nasaba da rashina da takeyi, gashi an hana kowa zuwa garemu tun a kurkuku. Gurin uwargijiyarta taje, ta dan jima kamin aka mata iso, shiga tayi ta tsugunna a darare.
"Barka da hutawa ranki ya dade" Yaya Asma'u ta fada a sanyaye.
"Barkanki dai Asma'u yarinyar kirki! Meke tafe dake ne, nasan ba banza ba wannan zuwan da sassafe" Mahaifiyar Yarima Kassim ta fada tana murmushi.
"Dama, dama ranki ya dade akan Noor ne kanwata. Don Allah ko da yadda za ayi in ganta?" Ta fada hade da sunkuyar da kai.
"Asma'u ina tunanin kowa a Daular Ming yasan umarnin da aka bada game dasu" Ta amsa mata a takaice.
"Hakane ranki ya dade! Nagode, a huta lfy" ta fada jikinta duk ya mutu.
"Zaki iya tafiya"
Fita tayi amma gaba daya hankalinta baya jikinta, wani kukane yazo mata ba tare data shirya ba. Can ta bayan wani gini taje ta zauna tare da cigaba da rusa kukanta.
"Allah ka fidda mu daga wannan rayuwar kuncin" ta fada da dan karfi tare da cigaba da kukan da takeyi.

"Subhanallah" Wata murya ma'abociyar dadi da sanyi ta fada.
Saurin dagowa tayi, nan idanunta suka sauka kan Yawale, yana daya daga cikin dogaran dake kula da bangaren nasu. Sauke idonta tayi tare da mikewa tana kakkabe jikinta kasancewar a kasa ta zauna.
"Asma'u meya sameki kike kuka haka?" Yayi tambayar cike da kulawa.
"Ba komai" ta fada tare da wucewa ta barshi a gurin. Binta yayi da kallo har ta kule wa ganinshi sannan ya bar gurin shima.
Yana tafiya yana tunanin ta fuskarsa dauke da murmushi, ya dade yana son Asma'u amma tsoron fada mata yake. Da abokinsa ya hadu, nan yake tambayarsa ganin murmushin yayi yawa. Take ya bashi labarin komai ciki ko harda dumbin son da yake mata, nan abokin ya bashi shawarar ya fada mata kamin lokaci ya kure mishi. Har abokin ya tashi don komawa bakin aikinsa, nan Yawale ya tuna a gidan Yarima Fu'ad yake, aiko baiyi kasa a gwiwa ba ya shiga tambayarsa game dasu Noor, nan abokin ya kwashe labarin duk abinda ya faru kamar a gabansa akayi ya fada masa. Da haka sukayi sallama kowa ya koma bakin aikinsa.

Har dare ban sake sa Yarima Fu'ad ko Yarima Ameen a idona ba, addu'ar bacci nayi na kwanta. Kasa baccin nayi sai juye-juye nakeyi tare da tunanin haduwarmu ni da Yarima Ameen da safe, da haka bacci barawo yayi gaba dani.😴

*****

Yau da tunanin su Mimi dasu Ya Ali na tashi, duk zuciya ta tamin daci, haka dai na daure tsatsakuri karin kumallo na bawai don inajin yunwa ba. Fitowa nayi bayan na dauki Qur'ani, kai tsaye Lambu na shiga, har Tala ta biyoni nace ta koma ina bukatar kadaici. Kai tsaye kasan bishiyar nan me fararen furanni naje na zauna tare da bude Qur'ani na nafara karatu.

#Vote
#Follow
#Comment

💞NOORWhere stories live. Discover now