9

132 14 2
                                    

💞 Noor

9

Bani da burin daya wuce na ganin yan uwana sun sami farinciki da rayuwa me kyau, wanda hakan bazai yiwu ba sai sun sami 'yanci daga bauta. Bani da zabin daya wuce na amsa bukatar Yarima Fu'ad.
"Zan fada masa na amince sai ku fara shiri nan da kwana biyu watakila mu wuce" na fada a sanyaye.
"Alhamdulillah! Wlh sai fargaba nake kada kice a'a" Mimi ta fada cike da murna.
"Alhamdulillah! Duk zamu shirya, bara naje na karasa aiki na" Yaya Asma'u ta fada tana mikewa.
Sallama muka mata ta wuce na bita da ido cike da tausayin ta, aikin nasu da yawa kuma babu wani hutu.

Washe gari da safe bangaren Yareema Ameen na shiga, gaidashi nayi na fara goge-goge daga bisani kuma na fita hado mishi shayi. Bayan na kawo shayin ne yace inje Lambu in jirashi, fita nayi zuwa lambun. Ina nan zaune a gefe sai gashi nan ya fito cikin wasu fararen kaya wanda suka karbi jikinshi sosai, nan na shagalta wajen kallonshi, maganar sa kawai naji don bansan ma ya karaso inda nake ba.
"Kallon na menene?" Ya fada, kunya naji ta kamani nayi kasa da kaina.
Mikomin wani kwari da baka yayi me kyau an kawata shi sosai, ba musu nasa hannu biyu na karba. Tafiya ya farayi na bishi a baya har sai da mukayi nisa cikin lambun naga ya tsaya yana fuskantar wani mutum-mutumi na katako daga dan nesa da mu. Kibiya ya mikomin yace in harba, karba nayi na seta shi sosai na harba amma ban samu katakon ba, karba yayi ya sake sa wata kibiyar sannan ya kalleni wanda hakan na nufin in kalla sosai kenen sannan ya harba aikam a kan abin ta sauka.
"Matso" naji ya fada, matsowa nayi amma sai ya sake maimaitawa, tsayawa nayi don ni bansan inda kuma zan matso ba. Fisgoni yayi ya saka kibiya ya seta min hannuna daidai sannan ya daura hannunsa bisa nawa. Wannan wane irin abune? Na tambayi kaina
"Ki nutsu" ya umurta. Tsayawa nayi, sai da ya saita sosai sannan yace in saki, kibiyar ta sauka kan katakon. Sakin hannuna yayi ya juya tare da fadin
"ki cire na jiki, kiyi ta gwadawa zan dawo in duba" yana gama fadin haka ya wuce ba tare daya saurari amsata ba.
Gwadawa nayi tayi tun bana samun tsakiya har na koma samun tsakiyar, ciresu nayi gaba daya na sake harba su duk a tsakiyar suka cunkushe. Neman guri nayi na zauna don in huta, jin kiraye-kirayen sallah yasa na tashi don inje in gabatar. Karo naji nayi da mutum nayi saurin matsa sai na tafi taga-taga zan fadi naji an rike ni, dago kai nayi idanunsa duk a kaina, mun kai minti biyu a haka sannan ya sakeni na mike sosai.

 Karo naji nayi da mutum nayi saurin matsa sai na tafi taga-taga zan fadi naji an rike ni, dago kai nayi idanunsa duk a kaina, mun kai minti biyu a haka sannan ya sakeni na mike sosai

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Mamaki ne ya kamani don banyi tsammanin ko zan fadi zai rikoni ba, Yarima Ameen kenen, murmushi ne ya subuce min.
Wucewa yayi ya tafi masallaci ni kuma na tafi namu bangaren.

Bayan na iddar ina zaune ina azaune sai ga wata baiwa wai inzo inji Yarima Fu'ad, tashi nayi nabi bayanta, mun danyi tafiya me nisa sannan muka isa wani bangare me kyau an kawata shi sosai. Shiga nayi nan naga cikin ma yayi kyau sosai amma bai kai na Yarima Ameen kayatuwa ba, gishingide yake akan wata shimfida ta alfarma ga kayan marmari nan gabansa, dagowa yayi ya kalleni fuskarsa dauke da murmushi kamar kullum, bansan sanda na mayar masa ba. Tasowa yayi ya taho guna tare da fadin
"Maraba da Noor, maraba da labari me dadi" murmushi na sake yi bance komai ba.
Kallona ya tsaya yi hade da fadin "wannan murmushin kam na farin ciki ne don in ba labari me dadi kikazo da shi ba bana tunanin zanga murmushin nan"
Kau da kaina nayi nace "na amince zan bika amma dole sai da yan uwana"
Katse ni yayi da cewa "wannan duk na gama da shi, don nasa anmin bincike a kansu kuma na kammala komi, tasu tafiyar gobe ce" saurin kallonsa nayi, jin yace tasu tafiyar gobe, ni kuma fa?
"Bazan tafi ba tare da 'yan uwa na ba" na fada ina kallonsa.
Murmushi yayi sannan yace "tabbas tare zaku tafi amma zasu bar garin nan gbe su jira mu a hanya, mu kuma jibi zamu tadda su In Sha Allah"
Da "to" kawai na amsa, sannan nace mishi zan tafi.
"Baki isa ba ko zama bakiyi ba balle insa ran zaki cin wani abu" ya fada yana hararata
Yar dariya nayi nace "Kayi hakuri ranka ya dade wani lokacin zanci"
"Wani lokacin ma bayi zakiyi ba, sai anjima" ya fada yana bata rai wai shi a lalle yayi fushi. Sallama na mishi na fita.

Bangaren Yareema Ameen na wuce don inji ko akwai abinda yake bukata. Tunda na shika kamshinsa ya gauraye ko ina amma nasan yana dakin karatun shi, can naje nayi sallama ina jiran iso, na jima tsaye sannan yace shigo. Tambayar sa nayi ko akwai abinda yake so a kawo mai amma baice komai ba, na jima nan tsugunne sanin halin shi sai yaga dama zai tanka. Ji nayi yace "Wani hukunci kika yanke game da tafiya Milan?"
Dago kai nayi muka hada ido, ganin yaki kauda nasa nayi gefe da kaina hadi fa fadin
"Na amince zan bishi" na fada kai tsaye. Jin shiru yasa na kai dubana garesa, ganin bacin rai nayi kwance a fuskarsa, jikina ne yayi sanyi, na tashi na fita.

#follow
#vote
#comment.


💞NOORWhere stories live. Discover now