💞 Noor
7
Yau sati biyu kenen da rasuwar Ya Ali kuma a yau ne nasa ran zan koma aiki kasancewar shugabar bayi mata ta sashen namu tamin magana akan rashin zuwa aiki.
Da wuri na shirya na duba cikin kayana na dauki wannan kullin turaren wutar, dakin su Khairiyya na biya don musu sallama sannan na fice.
Tunda na fito gabana ke faduwa sosai, ina tsoron abinda zan aikata amma wata zuciyar na tunamin da Ya Ali wanda mutuwar sa har yanzu sabuwa take a guna. Kwallar data sauko sannan na tura kofar da zata sadani da sashen nashi, cin karo nayi da mutum naja baya da sauri.
"Yaushe muka fara 'yar boye ne?" Ya fada yana kafeni da ido.
"Kayi hakuri ranka ya dade aiyuka ne sukamin yawa" na fada ina sinne kai. A cikin satin biyun da suka wuce kullum ya takura min kullum sai ya zo gurina wanda tun bana kulashi har na fara sakin jiki dashi. Kwana biyu kenen rabon da nasa shi a idona.
"Anjima zan shigo in kin gama ayyukan" ya fada yana kokarin wucewa, sauri amsa masa nayi da "toh"
Bin bayansa nayi da kallo har ya kurewa gani na, mamakin zakewarsa nakeyi, a ganina bai kamata yana wannan rawar kafar a kaina ba.
Shiga nayi kai tsaye hade da sallama, ciki-ciki ya amsa. Karasawa nayi inda yake na tsugunna ina gaiseshi "Barka da safiya ranka ya dade! An tashi lafiya?"
Bai amsa ba, na dade tsugunne, na mike da niyyar fara aiki na kawai naji yace "waya baki daman tashi?"
Komawa nayi na tsugunna ina jiran umarni diga gareshi.
Can ya sake gishingida yace "Sai lokacin da kikaga dama kike zuwa aiki? Karfe nawa lokacin da kika shigo?"
"Ayi min afuwa ranka ya dade wallahi bada gangan nayi hakan ba, tuba nake" na fada, bai ko amsa min ba sai shiru daya biyo baya ,na kusa rabin awa a haka sannan yace in tashi inje.
Direct garwashi na samo dan kunna turaren wuta, ashe bayan fita ta ya tambaya ina nake. Ina dawowa wata baiwa ke sanar dani cewan yana nema na, karasawa dakin nayi, sallama nayi ina jiran iso can yace "shigo"
Shiga nayi na ajiye kaskon turaren na karasa inda ake ajiye turarurrukan na dauko wani a kwalba, budewa nayi kaman zan iba sai na ciro na jikina zan zuba kenen naji an rike hannuna. Cike da fargaba na juyo muka hada ido dashi, jikina ne ya fara rawa kwalbar turaren da kuma dayan kunshin duk suka fadi, baya nayi cike da tsoro na taka kwalba bansani ba amma ni ba shine damuwa ta ba a yanzu.
Fisko ni yayi ya fara tafiya sai da yaje lambu ya saki hannuna ya tsaya. "Ke har kin isa ki kasheni? Wacece ke?" Ya fada a tsawace
"Ka kashemin dan uwa ni kuma nayi alkawarin daukar fansa, in kashe ni zakayi ka kashe ni kamar yadda ka kashe dan uwan nawa" na fada nima da daga murya, saukar mari naji a kunchi na nayi saurin dafe gurin hawaye na fita idona.
Nan ya shiga zayyana min yanda sukayi shi da Ya Ali, a ganinsa ya wanke kanshi amma ni sam ba abinda ya ragu a guna. Wucewa yayi ya barni nan durkushe ina kuka."Amma baka tunanin Fu'ad dan gidan Sarkin Milan yana Ming, a ganina Sarkin Ming bazai yadda da wannan maganar taka ba ranka ya dade" Ahmadu Barde ya fada yana kallon Sarkin Wambi . Dariya yayi sannan yace "Ai kasancewar sa a Milan ne zai bani damar cimma burina"
da haka suka cigaba da tattaunawa akan shirin nasu.Yarima Faruk ne ya bude wasikar da wani bawan Barde ya kawo mishi, karantawa yake a tsanake sabida yanaso ya gane me mahaifin nashi ke nufi da wannan sakon. Hankalinshi yayi masifar tashi amma ba yadda zaiyi tunda dai mahaifinshi ne kuma bankade sirrinshi yana nufin rasa mahaifin nasa da masarautar su baki daya.
Yana nan zaune Yarima Kassim Ya shigo da takunsa na isa, biye dashi kuma Gimbiya Salma ce tana ta zuba shagwaba akan lalle sai yayan nata ya yarda ta bisu gurin shakatawa dake wajen masarautar. Kallon ta Yarima Faruk yayi cike da so don shi a rayuwar sa yana tsananin sonta amma bata shi take ba.
Ana haka Yarima Fu'ad ya shigo, da sauri ta karasa gareshi ta rungume shi tana kukan shagwaba, shi kam dama kallon kanwa yake mata duk kuwa da sanin son da take mishi.
"Ya Fu'ad don Allah zan biku kaji?" Ta fada cike da shagwaba. Murmushin dake burge ta yayi kana yace
"Me yasa kikeso ki dinga yawo cikin maza?"
"Ni bani da kawaye kuma na gaji da zama cikin hadimai na" ta bashi amsa. Sanin halin Gimbiya Salma ko kwana za suyi yana cewa ta hakura ba yadda zatayi ba yace taje ta shirya, a sauri ta fice tana murna hade da mishi godiya.Sun firfito bisa dawakan su, Yarima Ameen kawai suke jira, sai ga dan aike daga gurin shi cewar suyi hakuri bazai sami zuwa ba sabida wani dalili. Jin haka Yarima Fu'ad shima yace suyi gaba yana zuwa, ya kada dokinshi ya koma ciki.
#Follow
#Vote
#Comment
![](https://img.wattpad.com/cover/194525576-288-k648333.jpg)
YOU ARE READING
💞NOOR
General FictionStory of Noor and the 5 princes of Ming Empire. Betrayal among them and read as love turns to hatred.