💞 NOOR
23
Duk wani abu mallakin Yarima Ameen da tambarinsa a jiki wanda duk masarautar kowa ya sani harta bayi, don tun kamin na zama baiwarsa nasani nima. Tambarin zaki ne da takobi a jikinshi, dalilin kenen da yasa Yarima Fu'ad yasan hankicin nasa ne.
Bayan fitar Yarima Fu'ad Tala ta shigo, nan muka zauna muna hira har nake fada mata muna cika shekara a ranar zamu tafi Milan mu kadai bada kowa ba.
"Nidai zan biku koda Daular Ming zaku bari baki daya" ta fada tana 'yar dariya.
"Babu bayi a Milan tun kafin Sarkinsu ya rasu, hakanne ma yasa ba zamu tafi da bawa ko daya ba"
"Ranki ya dade duk da haka zan biki"
Murmushi nayi kawai bance komai ba, tunani na farayi, idan har Yarima Fu'ad ya enta bayi kamin mu tafi tabbas sai dai gawarmu tabar garin amma bamu ba, a hakan ma idon Sarki Ahmad akan mu yake koda yaushe. Da wannan tunanin aka kira Maghriba na tashi na dauro alwala, Tala ma ta fita don gabatar da sallah itama. Bayan na idar nayi addu'o'i na kaman yadda na saba, ina nan zaune bisa sallayar sai ga Tala ta shigo
"Ranki ya dade Yarima Ameen zai shigo" ta fada a ladabce.
"Yi masa iso" na fada tare da mikewa ina ninke sallayar.Anayin Maghriba Yarima Ameen ya aika bawansa kiran Yaya Asma'u, shigo da ita har cikin dakin da yake bawan yayi bisa umarnin Yarima Ameen din.
"Dauki kisa" ya fada yana nuna wata tsadaddiyar alkyabba da wasu kaya dake kan wani tebur.
"To ranka ya dade" ta fada sannan ta dauka ta fito bawan ya nuna mata wani daki, nan ta shiga t saka. Dawowa gurin Yarima Ameen tayi, tayi sallama ya amsa
, kallo daya Yarima Ameen ya mata ya dauke kanshi "Tabbas me kyau ce" ya fada a zuciyarsa.
Mikewa yayi tare da fadin biyoni, binshi tayi a baya, suna fitowa sukaci karo da Wali, nan Yarima Ameen ya nema kujera ya zauna. Wali ne ya fara mata bayanin canza tafiya, yanayin amsa gaisuwa in bayi sun gaidata ko taki amsawa ma baki daya, kada ta bude fuskarta kuma, wani turaren mai kamshin dadi ya bata yace ta fesa, aikam nan dakin ya kaure da kamshinsa.Mikewa Yarima Ameen yayi, hakan yasa tabi bayansa, sashen Yarima Fu'ad suka tasamma dogarai na biye dashi suna mamakin wannan wacece tare da Yarima Ameen din. Suna isa bakin kofa, dogarai suka fara miko gaisuwa, Yarima Ameen kadai ya amsa amma ita hannu kawai ta daga. Murmushi Yarima Ameen yayi tare da fadin "Noor fa fiki nuna sarauta" a zuciyarsa. Suna shiga sashen da dakina yake suka dosa, sai gaishesu bayi keyi amma ba wanda ya amsa sai daga hannu kawai. Suna isa bakin dakin, aka neman musu iso, nan Tala ta shaidamin nace ta shigo dasu.
Yarima Ameen na shigowa na hango wata bayansa, kanta a kasa yake rufe take da alkyabba, kanwarsa ce na fada a zuciya ta. Zama yayi bisa daya daga cikin kujerun itama haka, nan Tala ta shigo hannunta dauke da tire da kayan marmari a ciki, gabansu ta ajiye sannan ta fita, ni kam sai binsu nake da kallo ganin haka yasa Yarima Ameen cewa "Bismillah ko?" tare da kallon inda macen take. Ga mamakin saita mike tsaye ta yaye hilarious alkyabban jikinta nan fuskarta ta bayyana.
"Yaya Asma'u" na fada da dan karfi. Dama saura kira in tambayeshi tana ina don ban kawo ita bace ganin suturar dake jikin matar.
Isa nayi gareta muka rungume juna cike da murna, kuka na fara nan Yaya Asma'u tace "To sarkin kuka kin fara kenen" cike da zolaya.
Murmushi nayi na kara rungumeta. Nan idona yakai kan Yarima Ameen wanda yake aikin kallonmu tun dazu, muna hada ido ya sakarmin murmushi nima murmushin na mayar masa.
Mikewa yayi tare da fadin Ina zuwa, yana fita gurin Yarima Fu'ad ya nufa. Yayi hakan ne don ya bamu guri mu zanta nida 'yar uwata, kuma naji dadin hakan.Duk tambayoyin da Yaya Asma'u tamin na amsa mata su don kwanciyar hankalinta, ganin lafiya nake yasa ta cigaba da hamdala ga Allah. Nan ta bani labarin Yawale da duk yadda sukayi da shi, tambayar ta nayi tana sonshi ita? Nan tace min eh, to ki aure shi kawai ko don ki bar wannan bautar don Allah. Toh kawai ta iya cewa, don abinda ke ranta bai wuce yadda zata cigaba da zama a Ming ba ni kuma na tafi Milan, hakan na nufin ta kasa, amma zamana a Ming tasan bazai haifarmin da farincikin da take burin in samu ba. Sai a sannan ta tuna da wani dan abun katako da mahaifinmu yace ta bani inna mallaki hankali na.
Riko hannuna tayi tare da fadin "Akwai abinda zan baki amma banzo dashi ba, zansan yadda za'ayi in baki"
"To" na fada tare da murmushi.
Ban tambaya daga waye ba hakan taso itama."Ameen don Allah ka daina zuwa gurin Noor" Yarima Fu'ad ya fada tare da kokarin danne bacin ransa.
Murmushi Yarima Ameen yayi tare da fadin "Fu'ad kenen, ban tsammaci zaka furta hakan ba"
"Aurenta zanyi shiyasa na fada maka hakan" ya fada yana bata rai.
"Allah sanya Alkhairi" Yarima Ameen ya bashi amsa.
Hira sukayi, nan Yarima Fu'ad yake tambayar ko yaushe Yarima Haisam zai dawo? Nan Yarima Ameen ke shaida masa yace zai jima kamin ya sake dawowa. Sallama yayi mishi, yana fitowa dakina ya isa.
"Hirar ta isa haka" ya fada yana kafeni da ido
"Nagode ranka ya dade, kamin abinda ba kowa zai yimin ba. Nagode Allah Ya saka da Alkhairi yaji kan mahaifa" na fada ina sunkuyar da kaina sabida kallon nashi ya soma isa ta.
"Ameen Noor " ya fada tare da isa bakin kofa.
Nan Yaya Asma'u ta maida hularta tabi bayansa bayan tamin sallama.
Banson tafiyarta ba amma ba yadda zanyi.*****
Washegari tun safe Gimbiya Salma ke neman amintacciyar baiwar ta amma shiru, ba inda dogarai basu duba ba amma ko sama ko kasa bata. Ganin har dare yasa ta shirya don zuwa gurin Yarima Faruk don shi take zargi yasa aka saceta. Fargabar ta daya kada ace mata ta mutu don sun shaku, tun suna yara suke tare da ita.
#Vote
#Follow
#Comment
![](https://img.wattpad.com/cover/194525576-288-k648333.jpg)
YOU ARE READING
💞NOOR
Ficción GeneralStory of Noor and the 5 princes of Ming Empire. Betrayal among them and read as love turns to hatred.