💞 NOOR
2Ina karasawa gurin gasar a cike yake fam da manyan bayi da kanana, a gefe na hango su Fanna ita da Nana suna min kallon tsana wanda inda sabo na saba. Ban bi ta kansu ba na kutsa cikin jama'ar gurin ina dubawa ko zanga Khairiyya aminiyata, can na hango ta tana ta zuba surutu na karasa inda take nace "to zabiya! Ke baki iya neman mutane ba ne?"
Tayi dariya tace ",Wlh saboda ke ma nazo, nasan dole zakizo kuma ina fata kece zaki dace " Kallonta nayi kawai bance komi ba , ta tabe baki tana cewa "kin fara zubawa mutane kwala kwalan idon naki ko? "
Murmushi nayi mai sauti tace da dan bugun kafadarta nace "Dadina dake magana" dai dai nan wani dogari ya iso duk muka maida hankulanmu gurinshi, sai da gurin yayi tsit sannan ya fara magana kamata haka "Duk kunsan dalilinku na zuwa nan kuma kunsan yadda gasar tace, da farko zamu fara duba masu tsaftar cikinku da kyau kamin na fara, kananan bayi suyi layi daban manyan ma haka, za'a fara dubawa" yana gama fadi kowa ya fara bin layi bisa yadda ya shaida mana.
Nida Khairiyya duk mun tsallake na tsaftar da na kyaun ma wanda su Fanna ba haka suka so ba amma sun san duk mun fisu kyau dama. A haka suka rarrage mutane ya kasance bamu fi mu ishirin ba daga bangaren kanan bayi manyan bayi kuwa su biyar suka rage su Fanna su uku sai wasu biyu na bangaren Gimbiya Aneesa.
Gasar dafa shayi aka fara wanda nagan kowa yana ta saka ganyayyaki kuma duk abu iri daya aka bamu, ina dube dube na hango wasu tsirrai a cikin tukunyan fulawoyi da sauri na karasa gun na tsinka na shinshina ina son tuno inda nasan kamshin, kawai na yanke shawarar amfani dashi don nasan bazai kashe mutum ba ai. Zuwa nayi na dafa shi tare da sauran ganyayyakin da aka bamu. Komi auna shi nake yi da kwakwalwa ta sabida kar yayi yawa ko kada. An gama dafa shayi kowa ta zuba a butar shayi tare da jera kofunan shayi guda biyu, daya bayan daya muka dinga kaiwa ana sha diga baya aka kori mutum bakwai a cikin su biyu bayin Gimbiya Aneesa ne.
Bangaren rubutu a ka tafi, an bamu takarda da rubutu a jiki wanda zamu kwafa, kallo daya na mishi ba fariya ba na rubuta da sauri na gama na bayar, nan ma a cikinmu aka zubar da mutane mutum goma har da kuma kawayen Fanna, Rahina da Mariya.
Bangaren karatu kuwa shima nayi dai dai sai ya kasance ni da Fanna ne mukayi dai dai sauran kuma akace su tsaya a bangare daya. Nida Fanna aka nunawa wata kofa aka ce mu shiga nidai gabana faduwa yake. Muna zuwa kofar dogari ya mana iso muka shiga.
Zaune yake yana rubutu a takarda ko kallo dama nasan bamu ise shi ba, abun tawaddan ya daga ya tsiyaya a kasa da sauri Fanna ta karasa tasa hannu tana gogewa, nikam dubawa nayi nagan wani kyalle a gefen shi wanda nasan don hakan aka ajiye, dauka nayi na karaso gurin na fara gogewa, saida na gama nagan Fanna duk ta bata jikinta.
Hannu ya daga wani dogari ya karaso inda yake, ya mishi magana yanda bamu ji ba. Dogarin yazo ya cewa Fanna ta fita, kallona tayi idonta cike da hawaye sannan ta tashi ta fita. Na fi minti talatin a gurin amma baice komi ba ko kallo na baiba sai rubutunsa yake. Can ya dago kai cike da isa yace "Dauko akwatin can" na kai idona inda yake kallo na tashi da sauri na isa gurin Akwatin karfen nasa hannu na dago kawai ya fadi a kafata sabida nauyi kuma ciwona bai gama warke wa ba, Yar kara na saki amma kamarma baisan inayi ba kuma dama banyi tunanin zai tanka ba. A haka na dauko duk da azabar da hannuna keyi na ajiye a gabansa baiko nuna yasan da ni gurin ba. Tsugunnawa nayi can gefe ina jiran umarni.
Nafi awa a tsugunne daganan bansan me ya faru ba, na farka na ganni a wani lallusan shimfida kalle kalle na fara yi tabbas dakin ya tsaru amma nasan ba dakinshi bane wannan sai dai bazai wuce bangaren sa bane nan din. Yunkurawa nayi zan tashi naji zafi sosai a kafada ta kallon jikina nayi nagan ba kayana bane a jikina wasu farare ne, mamaki ne ya kamani. Cigaba nayi da kallon dakin na hango kayana a gefe, tashi nayi na dauka.
Fita nayi waje na hadu da wata baiwa ta nuna min bangaren wanki, duk inda nayi bina aka da ido ha na karasa na hango wasu sun taru sai hayaniya suke. Har zan wucesu naji muryar Mimi tana kuka na dawo baya daidai Fanna zata mareta na rike hannun. Tsaya wa tayi kallona na saki hannunta naja Mimi mukai gaba, ban tambayeta komi ba don nasan halin Fanna ta tsanemu babu gaira babu dalili. Ce mata nayi ta tafi gurin aikinta ni kuma na karasa gurin wankin na wanke kayana anan naga tun daga kafadar rigar sosai rigar ta fadi hakan na nufin ciwon ne ya bude garin daukan akwatin daya sani.
Na shanya na juya zan tafi naji an zubarmin da kaya a kasa na juyo nagan Fanna ce ta kureni da ido, saiga su Rahina suma. Nan suka fara zagina wai dama sunsan ni Yar iska ce har na bashi kaina shima suna ganinshi shiru shiru amma ashe dan iska ne, bance komaima na tsugunna zan kwashe kayana Rahina ta taka na dago na dauketa da mari ta fadi gefe, Fanna da Mariya sukayo kaina suma nan muka fara fada amma sai nagan Fanna ta iya fada sosai ta makeni nayi baya na fadi, ina tashi nagan wani kwanan karfe anan kusa dani nasa kafa nayi kwallo dashi ya bigeta a ciki ta fadi kasa.
Kaman daga sama naji muryarshi "Biyo ni" gaba na ne yayi mugun faduwa na bishi a baya. Ashe tunda muka fara fadan yana tsaye yana kallo daga dan nesa da mu. Yana shiga bangaren sa ya juyo nayi kasa da kaina ina tsugunna wa yace "tashi tsaye"
The_Circle
![](https://img.wattpad.com/cover/194525576-288-k648333.jpg)
YOU ARE READING
💞NOOR
Ficción GeneralStory of Noor and the 5 princes of Ming Empire. Betrayal among them and read as love turns to hatred.