💞 NOOR
22
Na dade ina karatun sannan na fara addu'a akan Allah Ya kawo min dauki cikin halin da nake, sannan na yima iyayena da yan uwana na. Tuna Yaya Asma'u da nayi ya sani sakin wani kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, sanyayyen kamshinsa naji amma hakan baisa na daina kuka na ba. Neman guri yayi ya zauna yana fuskanta ta, saida na gaji dan kaina sannan nayi shiru amma ban dago ba.
"Goge fuskarki" Yarima Ameen ya fada yana mikomin hankici, hannu na mika don in karba tsautsayi yasa yatsunmu suka gogi na juna, saurin janye hannuna nayi tare dayin kasa da kaina. Tabe baki yayi sannan ya ajiye hankicin nan kusa dani, dauka nayi amma tunda ya doshi fuskata dashi kamshinsa ya addabe ni, goge fuskata nayi.
"Nagode" na fada a sanyaye.
"Meyasa ki kuka?" Ya tambaya ba alamar wasa a fuskarsa.
"Ba komai" na amsa kai tsaye.
"Meyasa ki kuka" ya maimaita a kausashe.
"Yaya Asma'u nakeson gani" na bashi amsa.
"Ki jirayi zuwanta bayan Maghriba" yana gama fadin haka ya mike. Har ya fara tafiya ya juyo, kallona yayi na dan dakiku sannan yace "Bani hankici na tunda kin gama kukan"
Murmushi nayi sannan nace "Saina wanke tukunna"
Kafada ya daga sannan ya wuce, binshi nayi har ya fita daga lambun sannan na sauke ajiyar zuciyar da ban san dalili ba.Tun jiya Yawale yake baza ido ko zaiga Yaya Asma'u amma babu alamunta. Yau kam zaune yake ta hanyar mawanka ko Allah zaisa tazo wucewa ko kawarta Habi. Wasu yammata ya hango su uku, tun daga nasan ya gane Yaya Asma'u da Habi dayar ce dai bai santa ba, rikicewa yayi sabida baisan ta inda zai fara mata maganar dake tafe dashi ba. Mikewa yayi tsaye, yana nan tsaye har suka kusa karasowa.
Habi ce tace "Asma'u ga mutuminki fa"
"Kyaleshi kawai" ta amsa mata.
Karasawa sukayi zasu giftashi yayi musu sallama dukansu suka amsa banda Yaya Asma'u, rashin jin muryarta yasa jikinshi yayi sanyi. Tafiya sukaci gaba dayi, sun danyi nisa ta gaji da magiyar su Habi kawai ta tsaya tace su tafi zata taho.
Dama idonsa na kanta, ganin ta tsaya yasa ya juyar da kansa gudun karta kamashi yana kallonta ya sake wani laifin.
"Sauri nake fa" ya tsinkayo muryarta.
"Afuwan" ya fada yana sauri don ya isa gareta.
Yana zuwa ya tsaya yayi shiru, itama shirun tayi batace komai ba. Daurewa yayi ya bude baki ya fara magana "Asma'u nasan kinsan abinda ke tafe dani amma dai kyaun magana ajita a bakin mai shi"
Ya danyi shiru kana ya cigaba
"Asma'u inasonki, ma'ana inason auren ki, ki zama abokiyar rayuwata kuma uwar 'ya'yana"
"Yawale kana tunanin a cikin wannan rayuwar zamu rayu har mu hayayyafa?" Tayi tambayar tana kallonshi.
"Yarima Kassim yamin alkawarin indai nayi aure zai 'yanta ni da matata, zai bani gida a ko'ina nake bukata a daular Ming" Ya fada cike da zumudi.
Murmushi Yaya Asma'u tayi sannan tace "Zanyi tunani" sannan ta wuce abinta.
Binta yayi da ido harta kurewa ganinsa sannan ya tafi inda zashi.Tana shiga sashen dakunansu ta wuce ta ajiye kayanta sannan ta fito ta nufi dakin girki, ji tayi an dafa ta
"Yawwa Asma'u keko meya hadaki da Yarima Ameen ya aiko kiranki?" Habi ta karaso gurinta da sauri tare da fadin hakan.
Kana kallon fuskar Yaya Asma'u zakasan tana cikin tashin hankali, jin batace komai ba kuma ga yanayin data shiga yasa Habi ta kwantar da murya da sigar lallashi tace "Ki kwantar da hankalinki Asma'u, kinsan Yarima Ameen shi mai adalci ne, kuma banji ance laifi kikayi ba don na tambaya dogarin"
"Tam, nagode Habi"
Sannan ta juya ta fita, a hanya banda tunani na ba abinda takeyi fatanta Allah Ya sa ba wani abun ne ya sameni ba. A haka tana tafiya tana sake-sake taci karo da Yawale amma ko magana bata mishi ba kasancewar bata tare da nutsuwar ta.
Tana zuwa dogarin kofa suka mata iso har cikin dakin da yake wanda aka kayata shi da kilisai da tum-tum. Sallama tayi ya amsa sannan ta gaidashi bai amsa ba sabida a ganinsa sallamar ta wadatar, ganin bai amsa ba yasa ta kara shiga tashin hankali.
"Ki shirya bayan Maghriba akwai dogarin da zai zo ya kaiki gurin Noor" muryarsa ta katse mata tunane-tunanen da take.
"Nagode ranka ya dade, Allah Ya saka da Alkhairi, Allah Ya kareka daga sharrin makiya"
"Ameen, zaki iya tafiya"
"A huta lafiya" ta fada tare da ficewa da sauri fuskarta dauke da murmushi, bakinta kam yaki rufuwa.
A haka ta isa gurin aikin nata, nan Habi wadda tun bayan fitar Yaya Asma'u ta kasa zaune , ganin tana yanayin farin ciki yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Nan Yaya Asma'u ta kwashe komai ta gaya mata, murna suka cigaba dayi su duka.Wali ne ya shigo sashen na Yarima Ameen, nan aka masa iso ya shiga ciki. Zaune ya tadda Yarima Ameen yana duba wasu takaddu masu tarin yawa. Gaisuwa sukayi sannan ya zauna tare da fiddo wata yar takarda daga aljihunsa ya mikawa Yarima Ameen.
Mamakine ya kama Yarima Ameen ganin sunayen dake rubuce jiki. Dago kansa yayi ya kalli Wali sannan yace "Salma kuma? Na zargi da sa hannun Faruk dama amma bana tunanin Gimbiya Salma zata aikata hakan"
Murmushi Wali yayi sannan yace "Sabida Noor Gimbiya Salma ta shigo ciki"
Sai a sannan Yarima Ameen ya tuna dumbin soyayyar da Gimbiya Salma take yima Yarima Fu'ad din. Tabbas a yanzu kam baiyi mamaki ba, kenan ita Noor ta kaima hari shi kuma Yarima Faruk, Yarima Fu'ad.
Wali ne ya cigaba da magana "Bawan da na tambaya cewa yayi akai-akai duka su biyun suna kiran Balelen, sannan akan idonshi Gimbiya Salma taje gurin Balele"
"Naji taje gurinsa a kurkuku ma" Yarima Ameen ya fada.
"Ai har can naje bincike ancemin da baiwarta taje, baiwar zansa a kamo mu tuhume ta watakila mu samu wani abun" Wali ya fada
"A'a Wali! Duk hanzari ba namu bane, mubi a sannu. Baiwar kuma karka damu da ita zansan yadda za'ayi, zan neme ka zuwa gobe" Yarima Ameen ya fada.
"To shikenen ranka ya dade, a huta lafiya" Wali ya fada yana barin dakin.Na matsu Maghriba tayi, gashi ma ba'a dade da sallar La'asar ba, garin yayi sanyi sakamakon damina data fara kawo kai. Ina nan zaune aka kwankwasa kofa, Tala tayi iso, Yarima Fu'ad ya shigo, zama yayi a kujerar dakin yana fuskanta ta. Fita Tala tayi, hakan ya bashi damar fara magana .
"Noor yau kwata kwata ban sanyaki a idona ba sai yanzu, ke kuma baki neme ni ba"
"Ayi min afuwa ranka ya dade" na fada a sanyaye
"Bana iya fushi dake, kema kin sani" Ya fada a sanyaye kamar yadda nayi.
Murmushi nayi don na gane tsokana ta yayi.
Kwankwasa kofa akayi, kallonsa nayi sannan na bada iso, Tala ce ta shigo ta mikomin yan kayan data wanke ciki ko harda hankicin Yarima Ameen. Ajiyewa tayi bakin gado zata fita Yarima Fu'ad yace ta mikomi shi hankicin, kallona tayi, kai kawai na daga mata. Mika mishi tayi ya karba sannan ta fita.
"Me kikeyi da hankicin Yarima Ameen?" Naji tambayar wadda a gurina bata da amsa amma saina daure nace
"Aro aka bani"
Murmushi yayi amma hakan bai hanani hango tsananin kishin dake tare dashi ba.
"Shikenen, ni zan wuce" ya fada tare da ajiye hankicin sannan ya fita.Assalam alaikum! Ayi min afuwan rashin jina kwana biyu, nayi yar tafiya ne.
#Vote
#Follow
#Comment

YOU ARE READING
💞NOOR
Tiểu Thuyết ChungStory of Noor and the 5 princes of Ming Empire. Betrayal among them and read as love turns to hatred.