💞 NOOR
18
Tsayawa yayi cak sakamakon wani numfashi mai karfi da yaji na saki, juyowa yayi bakinsa dauke addu'ar Allah Ya sa na farka. Bakin gadon ya dawo ya zauna ya riko hannuna cikin nasa sannan ya kafeni da ido. A hankali ya furta "Noor" kamar me rada.
Kokarin bude idona wanda yayi nauyi na shiga yi, ganin hakan ya sashi matse hannuna dake cikin nasa tare da sake kiran sunan nawa.
"Bude idonki a hankali" naji ya fada. Sai yanzu na tantance muryarsa, wani sanyi naji ya ziyarci zuciya ta, na saki wata ajiyar zuciya. Bude idona nayi fes na saukesu akan kyakkyawar fuskarsa mai dauke da murmushi abinda na dade ban gani ba.Tabbas Yarima Ameen kyakkyawa ne ajin farko, namijin da duk wata mace zata so ta samu. Dogo ne kakkaura, fari kal kaman ka taba jini ya fito. Fuskarsa me dan matsakaicin tsawo dauke take da manyan idanunsa farare masu kyau da girarsa me yalwataccen gashi, kyawawan labbansa masu launin ja-jaja, sai kuma dogon hancinsa wanda ya kara masa kyau. Gashin kansa me dan tsawo kwance yake a bayansa.
Iskar da ya huramin a idona ita ta dawo dani daga duniyar kyawunsa, murmushi ne ya subuce min. Kokarin tashi na shigayi nan ya taimaka min na zauna, "Sannu Noor" sassanyar muryarsa ta daki kunnena, tabbas bazan manta da ranar nan ba, domin yau itace rana ta farko da Yarima Ameen ya taba kirana da sunana. Tala ce ta shigo hannunta dauke da maganin da take bani, ganina zaune yasa ta sakin kofin hannunta. Yarima Ameen ne ya juyo ya watsa mata wani kallo nan da nan ta tsugunna kasa tana "Tuba nake ranka ya dade" daukan kofin tayi ta fita don dauko abu ta goge maganin daya zuba. Dakin Yarima Fu'ad ta dosa kamin ta dauko, nan dogarin dake tsaron kofarsa ya tambayeta lafiya, cewa tayi a shaidawa Yarima Fu'ad farfadowata, sannan ta wuce.
Dogarin na sanar mishi ya mike cikin azama jikinshi har rawa yake sabida tsabar farin ciki, su kansu dogaran sunsha mamaki don basu taba ganinshi a haka ba duk kuwa da da shi mai fara'a ne.
Yana shiga dakin sam bai kula da Yarima Ameen ba don shi hankalinsa gaba daya yana gurina baya ganin kowa in ba niba. Har yanzu fuskarsa da murmushi ya karaso bakin gadon zai rungumeni nayi saurin yin baya, matsowa ya sakeyi sai tsintar muryar Yarima Ameen yayi yana cewa "Lafiya dai?"
Juyowa yayi tare da bata rai sabida yanzu haka kawai bayason wani abu ya hadani da Yarima Ameen.
Bai amsa shi ba sai ma zama da yayi a kujerar dake gefen gadon, murmushin dake fuskarsa ya dawo. Hannu yasa zai riqo hannuna Yarima Ameen yayi saurin kai nasa hannun ya riqo nawa yana fadin "Kamar ma ba wani isasshen jini a jikinki" yana dudduba hannun tare da juyawa. Ni mamaki ma ya hanani magana, duk wannan fadan na menene? Na tambayi kaina. Ji nayi an fusgi hannuna da karfi wanda yayi sanadiyyar sani sakin kara tare da fusge hannuna daga riqon da Yarima Fu'ad yamin.
"Yi hakuri" Yarima Fu'ad ya fada tare da mikewa ya fice a dakin. Murmushi ne ya subucewa Yarima Ameen. Nan yasa Tala data kawomin abinci, sannan ya tambayeni inda abinda nake buqata nace "babu. Sallama yamin sannan ya fita.
Yana fita na sakin ajiyar zuciya ganin a yanayin da Yarima Fu'ad ya fita tabbas da alama fushi yayi. Mikewa nayi da taimakon Tala kasancewar ba wani isasshen karfi ne dani ba a yanzu. Bayi na shiga nayi wanka sannan dauro alwala, ina fitowa na tadda Tala ta shimfida min sallaya da hijab a kai, ga kuma doguwar riganan a kan gado. Rigan na saka sannan na tada sallah, salloli nayi tayi sabida Tala ta fita kuma bansan kwana nawa nayi ina kwance ba. Ina sallah ta shigo ta ajiye abinci ta fita, na dade ina rama sallolin sannan na zauna azkhar. Abincin na janyo na fara ci, sai da naji na koshi sannan na rurrufe akushin, mamakin yawan abincin da naci nayi.
Tashi nayi na fito sabida yanzu na danji karfin jikina, dogarin dake bakin kofata na tambaya gurin Yarima Fu'ad, binshi nayi don ya nunamin sannan wasu biyu kuma suka biyoni suma. A daidai kofar suka tsaya wanda suke tsaron kofar tasa suka bude na shiga, a gishingide na tadda sa kan kilisa ya rufe idonsa kamar me bacci. Karasawa nayi na zauna kan wata kujera nan kusa da kilisar da yake, bai bude ido ba balle ya motsa, na jima zaune sannan na tashi a tunanina ko bacci yake. Har na kai bakin kofa naji yace "Noor" tsayawa nayi cak amma ban juyo ba, bawai sunana ne ban saba ji a bakinsa ba a'a kawai yadda ya kira ne ya sani tsayawa. Muryarsa ta nuna akwai abinda ke damunsa, Yarima Ameen wata zuciyar ta cemin. Bude kofar kawai nayi na fita ba tare da na tsaya naji me zai ce ba."Inaso ka gayamin wanda ya saka ka kashe Fu'ad da Noor" .......
#Vote
#Follow
#Comment
![](https://img.wattpad.com/cover/194525576-288-k648333.jpg)
YOU ARE READING
💞NOOR
Genel KurguStory of Noor and the 5 princes of Ming Empire. Betrayal among them and read as love turns to hatred.