💞NOOR
4
Yarima Ameen, Yarima Fu'ad, Yarima kassim, Yarima Faruk sannan Yarima Haisam sune 'ya'yan sarakunan da akaji dasu gaba daya Ming Empire.
Yarima Ameen ya kasance dan Sarki Hassan wanda ya rasu shekaru 10 da suka wuce a fagen yaki. Yarima kassim kuma dan Sarki Ahmad ne wanda yake sarauta na Ming bayan rasuwar Sarki Hassan. Yarima Fu'ad dan Sarkin Milan ne wadda take karkashin Ming , Yarima Haisam shi ma mahaifinsa shine Sarkin Tandu wadda itama karkashin Ming take sannan Yarima Faruk dan Sarkin Wambi ne shi, itama karkashin Ming take.
Wa'inan 'ya'yan sarakuna sun tashi tare tun yarinta, Ming suke haduwa. Sauran suna fin wata biyar anan kamin su koma gidajen masarautun su.
Akwai gasar da sukeyi a tsakaninsu amma banda Yarima Ameen don abin baya birgeshi kuma dama ya girmesu.
Yadda ake wannan gasar shine kowa zai bada bayi mata goma diga bangaren sa, zasu baro masarautar dasu, sai su sakesu a fili babba su umarcesu da suyi ta gudu. Da sun fara nisa zasuyi ta harba kibiya dole bayin su kara gudu saboda inka tsaya za'a iya saminka, bayan bayin sunkai matsaya sai a fara irgawa aga bayin kowa. Wanda bayinsa sukafi jin ciwo ya fadi, duk shekara haka sukeyi. Yarima Ameen kam bayason wannan gasar, a ganinsa tsantsar zalunci ne kawai. Shekaru biyar kenen, duk shekara dani a bayin bangaren Sarauniya Aminatu mahaifiyar Yarima Ameen wanda Yarima Fu'ad ke amfani dasu a cewar su jarumai ne.
Sarkin Milan aminin Sarki Ahmad ne tun kuruciyar su zuwa yanzu da makiya keson rabasu, wanda Sarkin Milan yasan da hakan kuma kokarinsa bai wuce na ganin makiyannan basu kai ga cimma burinsu ba.Cigaban Labari
Yau da wuri na shiga bangaren Yarima Ameen don in gyara. Shara na farayi na dakin da yake karatu na goge babban teburin, wuta na samo nasa turaren wuta ko ina ya dauki kamshi. Shayi naje na hada, ina dawowa na taddashi yana karanta wani littafi. Sallama nayi bai ko kalli inda nake ba ya amsa , karasawa nayi na ajiye tiren ina gaidashi "Barka da safiya ranka ya dade, an tashi lafiya" bai amsaba dama bansa rai ba. Fita nayi na dauko dauko takardun aikin daya sani, don jiya kwana nayi zaune ina rubutu kaina ma ciwo yake.
Bayan na kawo bai ko duba ba yamin alama inje kawai. Daki na tafi na kwanta sabida kaina dake ciwo ga kuma baccin da nakeji. Kamar daga sama naji saukar ruwa a jikina, tashi nayi a firgice naga Fanna tsaye tanamin kallon tsana
"to isasshiya sai ki tashi uban gidanki na kira, sakara" tana gama fadin haka ta fita, mamaki ma ya hanani furta komai. Tabbas sai nayi maganin Fanna a masarautar nan zan sami lafiya, cire jikakkun kayan nayi na canza wasu farare masu ratsin blue a jiki. Raina a bace yake don haka koda na hadu da Khairiyya a hanya tamin magana ban amsa mata ba dama inda sabo ta saba.
Daidai zan shiga bangaren nashi naci karo da baiwar nan ta jiya data kawo turaren wuta tayi saurin sakin murmushi tana cewa "Noor ya gajiyan jiya? Nagode da taimakon da kikamin. Dama sirace ne na Yarima na kawo kin ganshi nan, ki karasa masa da shi don Allah" nace "to" tayi murmushi ta wuce. Daukan siracen nayi na na nufi kofan dakin karatun sa na kwankwasa shiru baamin iso ba kuma na tabbata ya ciki. Tsayawa nayi a bakin kofar da siracen a hannuna tiririn sai bugan hancina yake ina shaka, gaba daya na fara fita diga hayyacina kuma na galabaita bansan dalili ba, ina nan tsaye sai zufa nake ga ciwo yana cina ta ko ina. Ruwan siracen har ya huce a hannuna ban ajiye ba ina nan tsaye kaman an dasa ni.
Bude kofar da akayi yasa na dago kaina muka hada ido, dauke kanshi yayi. Wani dogari ya kwalawa kira sai gashi yazo, ce mishi yayi ya kira bayi mata su kaini daki su kira likitan masarautar ya duba ni. Komawa ciki yayi ya rufe kofar, ina nan tsaye banko motsa ba sai ga su Khairiyya da saurinsu karbar kwanon sukayi daga hannuna. Kamani sukayi suka kaini daki, bayan minti kadan saiga likitan. Dubani ya shigayi, magunguna ya bani sannan ya tafi. Yana fita bacci yayi gaba da ni.

YOU ARE READING
💞NOOR
Ficción GeneralStory of Noor and the 5 princes of Ming Empire. Betrayal among them and read as love turns to hatred.