25

107 11 3
                                    

💞 NOOR

25

jujjuya abun na shiga yi amma banga wani alama ta komi jikinshi ba, ajiyewa nayi cikin wani dan akwati. Karin kumallo nasa a kawomin nan na zauna naci sosai don yau da yunwa na tashi. Tala nasa ta hadamin ruwan wanka na shiga, wanke kaina nayi daga nan, na dan jima kamin na fito. Koda na fito ban lura da mutum a dakin ba kwata-kwata, sai da na isa gurin kayana na bude na dauka, juyowar da zanyi na hangi Yarima Kassim zaune bisa kujera. Idanunsa a rufe suke da alama ya dan jima a zaune, bandakin na koma na saka kayan sannan na fito. Cike da fargaba nayi sallama tare da daga murya, firgigit yayi ya farka, ko bacci yake Oho😮 .
Bata fuska😡 nayi sannan nace "Lafiya na ganka a cikin dakina?" Na mishi tambayar ina kallonsa.
Washe baki yayi😀 sannan yace "Noor dama gurinki nazo aka ce kina wanka shine na zaune jiranki"
Lallai ma baka da hankali na fada a zuciya ta.
Harara na watsa mishi sannan nace "Shine saika shigomin har cikin daki kamar dakinka? Wannan ai rashin tunani ne"
Shiru yayi baice komai ba, a zuciyarsa yana cewa nine mara tunanin? Zakiga rashin tunani kuwa.

Mikewa kawai yayi baice komai ba ya fita a dakin.
Zama nayi na karasa Shiryawa. Ina gamawa na fito sai kamshi nakeyi don jiya Yarima Fu'ad da kansa Ya kawomin su. Ina isa sashen nasa aka min iso, zaune na taddasa yana ganina ya fara murmushin sa mai kashemin zuciya.
"Barka da zuwa Noor" ya furta yana kallona.
Murmushi nayi sannan nace "Yawwa" tare da zama akan kujerar dake kusa dani.
Hira muka farayi nan yake tambayata ko ina riga kwanakin mu?
"Ina tunaninma na fika son tafiya" na fada ina murmushi.
"Kai! Ba lallai ba kam"
Dariya nayi sabida yanayin da yayi maganar.
Nutsuwar ya tattaro sannan yace "Noor"
"Na'am" na amsa
"A daura mana aure kafin mu tafi" ya furta
"Tambaya ce ko shawara?" Na tambaya ina kauda kaina gefe don bana so mu hada ido.
"Duka" ya bani amsa a takaice.
"Zanyi tunani akan hakan" ina gama fadin haka na mike na bar dakin ko sallama ban masa ba. Bina yayi da ido ba tare da yace komai ba har na fita daga dakin, ajiyar zuciya ya saki sannan yace "Bazan iya fassara yanayin fuskarta ba, Allah kasa shirina bai wargatse ba"

Sarki Ahmad ne zaune yana tattaunawa da mahaifiyar Gimbiya Salma akan aurenta da Yarima Faruk da takeso ayi.
"Ni bazance ta auri Faruk ba, duk wanda ta kawo tana so shi zan aura mata" Sarki Ahmad ya fada yana kallon matar tasa.
"To Allah Ya zaba mata na gari" tayi furucin a sanyaye sabida taso ace ya amince da maganar Yarima Faruk din.
"Assalam alaikum" muryar Gimbiya Salma ta karade dakin.
"Shigo" mahaifiyar ta tayi umarnin.
Shigowa tayi ta zauna bisa kilisar dakin tare da gaidasu.
"Ummusalma" Sarki Ahmad ya kira sunanta.
"Na'am Abba" ta amsa.
"Kinason Yarima Faruk?" Ya tambayeta.
Tambayar ta dake ta amma sai ta kawar da tsoron ta sanin cewa bazai taba mata auren dole ba.
"A'a" ta furta kai tsaye.
"To fiddo wanda kikeso nan bada jimawa ba"
"To Abba"
"Tashi ki tafi" ya furta.
"A huta lafiya" ta fada tare da mikewa tabar dakin.

*****

"Ki gayamin duk abinda kika sani game da kashe su Yarima Fu'ad da Noor" Wali ya fada a tsawace.
Amintacciyar baiwar Gimbiya Salma ce tsaye jikin wani katon katako da aka kawata dakin dashi, a daure take jiki duk ta fita kamaninta sabida tsabar wahalar da aka bata. Sai nishi take tana fitar da numfashi dai'dai.
"Wallahi bansan komai ba game da maganar da kakeyi" ta furta a wahale.
"Gara ki fada tun wuri inba haka ba azabar sai tafi haka" Wali ya fada rai a bace.
Juyawa yayi ga wani dogari tare da fadin "Karka kuskura ka bata koda ruwa ne, ni zan wuce sai gobe In Allah Ya kaimu"
"Toh yallabai! Sai da safe" bawan ya fada.
Fita Wali yayi, daganan gida ya wuce gurin iyalinsa.

Bayan nayi Maghriba na dauko wannan abun da Yarima Ameen ya kawomin, na dade zaune ina dubashi amma ba abinda na gano game da shi. Tala ce ta shigo nan nake tambayar ta ko ta san menene.
"Lah ranki ya dade ai ma'adanar sakon sirri ce, kakana yana da guda kuwa"
"Yawwa! Kinsan yadda ake budewa?" Na tambayeta cike da zumudi.
"A'a ranki ya dade" ta furta a sanyaye.
"Ba wanda kika sani yasan yadda ake budewa?" Na sake tambayar ta.
"Wlh ba wanda na sani" ta fada.
"Shikenen" na furta jiki a mace.
Kama hanya tayi zata fita, harta isa bakin kofar ta dawo da saurinta tace "Ranki ya dade me zai hana ki tambaya Yarima Ameen" ta fada da fara'arta.
"Ai bamu sani ba ko ya sani shima" na bata amsa.
"Amma ai yana da ilimi sosai ko bai sani ba watakila ya karanta wani abu akai"
"Kai amma na gode Tala, sam banyi wannan tunanin ba. Allah Ya kaimu gobe zanyi mishi magana" na fada da fara'a ta nima.

#Vote
#

💞NOORWhere stories live. Discover now