15

101 16 6
                                    

💞 NOOR

15

Washegari koda Sarauniya Bintu ta tuntubi Sarki Ahmad da maganar diyar tata cewa yayi kawai zaiyi tunani akai, jiki a salube ta tashi ta fita, dama tuntuni tasan hakan bamai yiwuwa bane.

Yau ma kamar kullum haka aka kawo mana karin kumallo amma ko kallon inda abincin yake bamuyi ba. Can dai dana gaji da zama kuma ga yunwa na damuna sai na tashi nayi amfani da awarwaron tagullan hannuna na dinga buga kofan dashi yadda dogaran zasuyi da wuri. Can sai ga wani dogari, yana zuwa yace menene yake faruwa? Nan na shaida mishi cewa abincin ne ya kife don Allah ko zai samo mana wani? Bai ce komi ba, yakai dubansa ga Yarima Fu'ad sannan ya juya ya tafi ba tare da yace komi ba. Har na fidda ran dawowarshi aikam sai gashi da akushe biyu manya. Budewa yayi ya mikomin na karba cike da mishi godiya, koda na bude akushin shake suke da abinci na alfarma. Nan muka shiga ci cike da nishadi.

Yarima Ameen kuwa kullum da kyar bacci ke daukansa ya kasa gane dalili. Kamar kullum cikin kwanakin da suka dan wuce haka yauma ya tashi da ciwon kai. Sashen Sarauniya Aminatu wato mahaifiyar sa ya nufa, da isar sa ya tadda tana karin kumallo shima ya zauna, nan ta umurci wata hadimarta data zuba mishi abinci. Sai da ya koshi sannan ya koma kan wata kujera nan gefe ya zauna, neman ciwon kan yayi ya rasa don ya manta rabon daya ci abinci haka cikin nutsuwa.
"Lafiya dai Ameen" mahaifiyar tasa tayi tambayar cike da kulawa.
"Lafiya lau Hajja" ya bata amsa.
"A'a badai lafiya ba, wannan ramar fa? Kuma na lura kwanakin nan baka cikin nutsuwa" ta fada tana kara dubanshi.
"Ba komai fa Hajja, ina dai zazzabi a tsaitsaye ne amma ina shan magani" ya fada tare da kauda kansa don kar ta gane.
"Allah Ya sawake! Sai ka ragewa kanka hidindimu ka samu ka huta" ta fada fadin hakan bawai don ta yarda zazzabi bane.
"In Sha Allah! Bari in karasa ciki. A huta lafiya" ya fada yana mikewa.
Bata ce komai ba sai binsa da tayi da ido har ya fice.

"Balele" Gimbiya Salma ta fada cike da izza.
"Na'am ranki ya dade" ya amsa tare da kara sinne kai.
"Bana son a sami wani akasi a aikin dana saka, kuma a yau nake son ka aiwatar da hakan" ta fada a kausashe.
"In Sha Allah babu za'ayi kamar yadda kikace"
"Zaka iya tafiya, akwai sako hannun sarkin kofa" ta fada tana juya baya. Tashi yayi ya fice yana fadin a huta lafiya.

"A nemo min Balele duk inda yake a kawoshi" Yarima Faruk ya umurci wani bawansa. Fita bawan yayi da sauri don aiwatar da bukatar ubangidan nasa.
Bai wani jima ba sai ga shi tafe Balele na biye masa. Gaisuwa ya mika bai ko amsa ba ya fada masa bukatar sa. Balele na fita gidan wani dogari yaje, nan ya fada masa bukatar sa. Nan take dogarin ya shiga wani daki sai gashi da wata kwalba karama da wani jan abu a ciki, karba yayi hade da yin godiya, ya bashi sulalla sabbi file cike da wani dan jaka, sannan yayi mishi sallama ya fice.

Fitowa ta wanka kenen naganshi tsaye shida Gimbiya Salma suna magana dama tun a bayin naji maganganu. Dama sun juya mun baya, jin motsina yasa ta juyowa tare da bata rai kaman taga mutuwar ta. Daga ganin idanunta kasan tasha kuka sosai, kawar da kaina nayi gefe na cigaba da abinda nakeyi. Sun jima suna magana, can naga ta riko hannunsa tana kuka, dauke kaina nayi don raina ya dan sosu da hakan da tayi. Da ta gaji don kanta ta tafi tana wurgomin kallon tsana.

Yau kam ba'a kawo mana abincin dare da wuri ba don har Yarima Fu'ad ya dan soma bacci. Wani dogari ne ya kawo abincin, fuskarsa na kalla kaman na taba ganinshi amma na kasa tunawa. Karasawa nayi na karba tare da yin godiya, juyawar da zanyi naji abu a tsikareni a wuya na, juyowa nayi nagan dogarin har ya soma tafiya . Ban damu ba na nemi guri na zauna, zama nayi don jiran Yarima Fu'ad ya tashi sannan muci abincin. Zufa ce ta fara karyomin ta ko'ina, cikin kankanin lokaci jikina ya fara tsuma na fara fita a hayyacina, magana ma na kasa, ko yatsa ban iya dagawa. Ina nan a wannan halin har na rasa inda kaina yake.
Yarima Fu'ad ne ya farka bakinshi dauke da salati, duba kan kujerar da nake zaune kamin bacci ya daukesa yayi, ganin bai ganni ba yasa ya fara bin dakin da kallo, idanuwansa ne suka sauka a kaina nan malale kan sallayar. Da sauri ya iso gareni, kiran sunana ya shiga yi amma shiru, kama hannuna yayi yaji sanyi radau, Idonsa ne ya sauka akan bakina daya bushe ya fara shudi-shudi. Jijjigani ya farayi hankalinshi a tashe yana kiran sunana ganin kaman ba rai jikina yasa shi sakin wata kara yana kiran dogarai. Rungume ni yayi kam-kam ya shiga rera kuka kaman wani karamin yaro kuma haka zalika bai daina kiran dogaran ba. "Tabbas in Noor ta mutu bazan taba yafewa kaina ba" ya fada a zuciya.

#follow
#vote
#comment

💞NOORWhere stories live. Discover now