28

153 6 4
                                    

💞 NOOR

28

A min afuwa na jina shiru kwana biyu. In Sha Allah zaku dinga jina akai-akai.

Da kyar na karasa sashenmu, raina a bace amma fuskata bata nuna ba, saidai kirjina dake mun zafi. Ina shiga cikin daki na shiga na kwanta, biyoni Tala tayi tana tambaya ko lafiya? Shiru na mata ban amsa ba. Ganin haka yasa ta kwasomin kayana tace"gashi ranki ya dade, inkin tashi saiki canza"
Sannan ta fita,

*****
"Wacece ta kwankwasa?" Ya tambaya da muryarsa mai rikita ta.
A daburce ta amsa da "wata baiwa ce ranka ya dade"
Baice komi ba ya cigaba da rubutun da yake.
Shayin ta hada ta ajiye nan gabanshi sannan ta dauke ragowan kayan ta fita.
Dan dafe kirjinshi yayi, jikinshi na bashi Noor ce .
"Nayi kewarki Noor" ya fada a fili. Ajiye rubutun yayi ya shiga ciki don ya huta.

*****
"An gama hada kan sojojin, umarninka kawai suke jira ranka ya dade" Jafar ya fada.
"A jira da sauran lokaci tukunna, zaka iya tafiya"
Jafar ya juya zai tafi.
"Jafar" Yarima Fu'ad ya dakatar dashi kafin ya fita. Juyowa yayi yana jiran umarni.
"Ba wanda ya ganka lokacin daka shigo ko?
"Eh ranka ya dade"
Gyada kai kawai Yarima Fu'ad yayi.
Tashi yayi ya nufi sashe na. Nan Tala ta fadamishi banason ganin kowa. Baiso komawa ba amma ba yadda ya iya.
A hanya ya hadu da Yarima Ameen, gaisawa sukayi kawai ya wuce. Har ya gotasa ya dakata da tafiya, ganin sashena ya nufa yasa ya bisa a baya. Tala na fadin isowar Yarima Ameen naki bada iso.
Banson ganin kowa banson ganinka a yanzu Yarima na. Na fada a zuciya ta.

*****
"Fu'ad"
"Naam ranka ya dade"
Gyara zama Sarki Ahmad sannan yace "inaso zamuyi magana ta fahimta, mahaifinka abokina ne tun muna yara kuma tare muka taso. Qaddara ta ratsa saidai abisa da addu'a. Allah Yaji kansa"
Yarima Fu'ad ya amsa da "Ameen"
Daurewa kawai yakeyi don ji yakeyi kaman ya tashi ya shake Sarki Ahmad har lahira.
"Saura wata daya tsaronka ya kare, washegari za'a daura maka aure da Ummusalma In Allah Ya yarda. A ranar kuma zan nada ka Sarkin Milan, sai ka tafi da matarka"
"To" shine kawai abinda Yarima Fu'ad ya iya fada.
Kallonsa Sarki Ahmad yayi tare da fadin "zaka iya tafiya"
Yana fitowa yakai hannu ya daki bango wanda hakan yasa yaji ciwo a yatsunsa. Huci yake kamar wani zaki, ransa a tsananin bace amma wani sashi na zuciyarsa na murna da hakan idan ya tuna shirinsa. Kenen zai jefi tsuntsu biyu da tarko daya. Sashensa ya nufa ransa kal amma yana fargaban yadda yadda zan dauki zancen nasa.

*****
Da gudu Gimbiya Salma ta fito daga sashenta, bayinta na biye da ita suna rokon ta dena gudu ta tafi a hankali, bata saurare su ba sabida ba shine a gabanta ba. A haka ta isa sashen mahaifiyar ta sannan ta dakata ta daidaita nutsuwarta, bata karasa ciki ba har saida taji numfashinta ya daidaita sannan ta shiga.
"Barka da zuwa ranki ya dade" hadiman dake bakin kofar suka fada a tare.
Ko amsawa batayi ba tasa kai zata wuce wata ta tare ta da fadin "Afuwan ranki ya dade amma bata bukatar ganin kowa tace kanta ciwo yakeyi"
"Ke wacece da zaki taremin hanya? Bana bukatar iso gurin mahaifiya ta"
"Tuba nake ranki ya dade amma umarnin data bata kenen" hadimar ta fadi tana sunkuyar da kai.
Juyowa Gimbiya Salma tayi ga nata hadiman tace " ku budemin kofa koda hakan na nufin datsa ta gutsi-gutsi"
Nan wani dogari ya fisgota nan ta shiga bada hakuri ta tsugunna ta riko kafar Gimbiya Salma.
"Hayaniyar me nakeji ne? Mahaifiyar Gimbiya Salma ta tambaya.
Nan kowa ya shiga hankalinsa, bata sake cewa komaiba ta koma, nan Gimbiya Salma tabi bayanta.

"Barka da hutawa ranki ya dade" Gimbiya Salma ta fada.
"Baki taba zuwa bakiyi hayaniya ba" mahaifiyar ta ta amsa
"Tuba nake ranki ya dade, amma na gaji da neman iso wajen ganinki"
"Haka dokar take kuma dole ki bi"
"To" ta amsa a sanyaye.
"Fadi maganar dake tafe dake"
"Aure" ta kasa karasawa.
"Aure kuma?
Sunkuyar dakai tayi sannan tace "Aure zanyi nan da wata daya abba ya yanke hukunci"
"Masha Allah! Faruk din yana ina shi "
Nan aka aiko Sarki Ahmad na kiran Sarauniyar sa.
"Nasan ma zancen auren ne"
"Umma Fu'ad ne fa"
"Baki hakura ba kenen, maiyasa kika kasa gane Fu'ad baya sonki kuma bazai taba sonki ba. Mahaifansa da aka kashe a anan fa, a tunaninki ya manta? Wlh kika aureshi bazaki taba farinciki ba, ki hakura ki aure Faruk"
"Meyasa kika kasa gane tawa damuwar, inna rasasa kema zaki rasa ni" tana fadin haka a fusace ta mike ta fita tana hawaye.

*****

Koda Yareema Ameen ya koma sashen shi mamaki ne fal ranshi yadda nace bazan ganshi ba. Zama yayi yasa a kira mishi Fannah . Nan Wali ke shaida masa maganar bikin Gimbiya Salma da Yarima Fu'ad wanda zaayi wata mai kamawa.

Pls
#Vote
#Follow
#comment

💞NOORWhere stories live. Discover now