💞 NOOR
13
Kurkuku aka maida ni wasu dogarai suka dauki Yarima Fu'ad. Ina nan zaune ni kadai sai kuka nake nan mutuwar yan uwana da aminiya ta suka dawo min, na dade ina kuka sannan na tashi nayi alwala nayi sallah ko zan samu sassaucin abinda nake ji. Ina nan zaune ina azkhar aka dawo da Yarima Fu'ad aka kwantar da shi, dogaran na fita na koma kusa dashi ina kallon fuskarsa idona cike da hawayen dana keta rikewa tunda aka shigo da shi. Kuka na shiga rerawa ina jin wani sonshi na shigata. Shesshekar kukana ne ya sashi farkawa ya zuba min jajayen idanunsa da suka kada sabida tsananin bacin rai, ya jima yana kallona ina ta kuka abina ba tare da nasan ya farka ba.
"Kukan ya isa haka" ya fada yana cigaba da kallona, saurin dagowa nayi sai kuma naji kunya nayi kasa da kaina, kukan na cigaba da yi abuna. Bai kuma ce min komi ba har na gaji da kaina na daina.
Tashi yayi ya shiga bandaki yayi wanka hade da dauro alwala, ya dade bisa sallayar yana addu'o'i ga mahaifansa da duk wasu wanda Sarki Ahmad ya kashe a yau din. Yana tuna kanwarsa abar kaunarsa, saboda rashin imani ma tana dauke da tsohon ciki aka kashe ta, Kukane yaci karfinsa.
"Kayi kuka Yarima ko ka samu sassauci" ya tsinkayo murya ta, bai ce komi ba bai kuma dena kukan ba.
Anan kan sallayar bacci yayi gaba da shi."Kassim sanin kanka ne mai martaba bayajin maganar kowa kaf Masarautar nan" Yarima Haisam ya fada yana cigaba da kai komo a tsakar dakin.
"Faruk kasa mahaifinka yayi mai martaba magana mana, ni a ganina zai iya sauraronsa" Yarima Kassim ya fada yana kallon Yarima Faruk.
"Hmm! Ni a ganina mai zai hana duka mu hudun muje gunsa mu rokar ma Fu'ad saussauci?" Yarima Faruk ya fada sanin halin mahaifin nashi da kuma abinda ya aikata. Da haka suka yanke shawarar zuwa gurin Sarkin bayan la'asar.Yarima Ameen ne durkushe gaban me martaba kansa a sunkuye.
"Fadi abinda kake son cewa Ameenu ni ai mahaifine a wajenka" Sarki Ahmad ya fada yana murmusawa don yasan halin Yarima Ameen ba kasafai ya fiya zuwa garesa ba sai in abu yaci tura.
"Baffa alfarma nazo nema a gurinka sanin cewa ban taba neman wata alfarma daga gareka ba yasa yau nazo akan batun Fu'ad. Baffa ina neman alfarmar ayi masa sassauci sabida laifin mahaifinsa ne ba nasa ba kuma Fu'ad ya daukeka tamkar mahaifi, bai cancanci haka daga gareka ba." Shiru Yarima Ameen yayi na wasu dakiku, ganin ko kallonsa Sarki baiyi ba yasa yaci gaba da magana.
"Ina fata wannan adalin sarki kuma mahaifi a gareni zai duba buqata ta cikin haske"
"Zan neme ka, zaka iya tafiya" Sarki ya fada a kagauce.
"A huta lafiya" Yarima Ameen ya fada tare da ficewa.
Yarima Ameen bai dade da fita ba su Yarima Faruk suka isa ga sarki, iso suka sa jakadiya ta musu sannan suka shiga. Gaidashi sukayi cikin ladabi, sannan suka zauna kowa yayi shiru. Ganin shirun nasu yasa Sarki magana.
"Meke tafe daku ne 'ya'yana naga alamar da magana kukazo?"
Haisam ne ya tsunguli Yarima Kassim, hakan na nufin shi zaiyi magana. Kasa yayi da kansa kamin ya soma magana "Abba d-ddama alfarma mukazo nema wurinka"
"Wacce irin alfarma kenen alkassim?" Sarki ya tambaya yana kafeshi da ido.
"Abba dama akan Fu'ad ne, Abba don Allah kayi hakuri a duba lamarinshi ko dan abotar dake tsakaninmu"
"Sannu Alkassim, ai banyi tunanin kunyi tsaurin da zaku nemi ja da hukunci na ba" Sarki ya fada a fusace.
""Tuba muke ranka ya dade" su duka suka hada baki wajen fada.
"Ko shi Fu'ad din ne ya turo ku?" Ya kuma tambayar su.
"A'a ranka ya dade tuba muke" suka amsa tare
"To ku tashi ku bace min da gani" ya fada a tsawace, dan da nan suka fice cikin sauri.
Bayan fitarsu ya aika a kira mishi Barde, yana zuwa ya fada mishi ya aika da sako ga Yarima Fu'ad akan ya gama bada duk wata wasiyya tashi zuwa gobe da maraice za'a yanke mishi hukuncin kisa ta hanyar rataya. Sallama Barde yayi tare da fita, wani dogarinsa ya aika kurkuku don isar da sakon. Koda su kaje yana bacci sai ni kadai, nan suka shaida min hukuncin nasa wanda ya sanyani sulalewa na zauna dabas hade da sakin kuka mai cin rai.Washegari, Gimbiya Salma ta shiga turakar mahaifin nata ba tare da ta saurari jakadiya akan fadan da take mata na jiran iso ba. Gaban mahaifin nata ta isa tana kuka ta riqo hannunshi tana fadin "Abba.......
#Vote
#comment
#follow

YOU ARE READING
💞NOOR
Fiksi UmumStory of Noor and the 5 princes of Ming Empire. Betrayal among them and read as love turns to hatred.