11

111 14 4
                                    

💞 NOOR

     11

Duk inda nake sa ran zanga su Mimi ita da Khairiyya  na duba bangansu ba, wata da suke aiki guri daya da Khairiyya na tambaya ko tagan su tace a'a, dubawa na shigayi ko ina cikin masarautar. Nazo wucewa ta wani gurina na hango mutane sun taru a kusa da wani rafi, haka kawai naji gabana ya fadi bansan dalili ba, kaman an tunkuda ni haka na nufi gurin rafin. Mata biyu na hango saman ruwa duk da fuskarsu kife take saman ruwan hakan bai hanani hango awarwaron dana taba bama Khairiyya ba, bansan lokacin dana fada ruwan ba na juyo da ita saboda na kasa gasgata abinda na gani, Tabbas Khairiyya ce, da sauri na janyo ta kusa da ita ina addu'a Allah Ya sa ba ita bace. Bansan sanda na saki wani kuka mai ratsa zukatan masu saurare na rungume ta ina cigaba da kuka na, bibbiyu na fara gani, ji nayi an daukeni kamin komi ya zama duhu.
                                                            Zaune yake gefen gadon da nake, idonsa ya kada yayi jajur kallo daya zaka masa kasan ransa a matukar bace yake, ashe tun lokacin dana fito na nufi cincirindon mutanen ya hango ni, ganin na shiga ruwan yasa shi karasowa gurin, jin sautin kukana ya sashi kutsawa cikin jama'ar wanda sam basu lura da shi ba sai da ya shiga ruwan. Tunda ya daukoni yayi umarni da a daukesu aje a musu sutura, duk inda yayi idon kowa na kanshi, ganinsa dauke da mace macen ma baiwarsa yasa kowa ke fadin albarkacin bakinshi. 
                                               A firgice na farka hade da kiran sunan Mimi da karfi, ajiyar zuciya mai karfi ya saki  tare da saurin riqo hannuna hakan ya sani kallonshi hawaye na tsiyaya a idona, ci gaba nayi da kuka na.
"Kiyi hakuri Noor ki daina kukan haka don Allah! Addu'a ya kamata kiyi musu. An kaisu tun dazu, Allah Yaji kansu" yana fadin haka ya tashi ya fita.
Meyasa koda yaushe Yarima Fu'ad me taimako nane? Meyasa zuciyata take jin wani abu game dashi? Ya zanyi? Tabbas saina dauki fansar kashemin yan uwa da akayi kuma hanya daya zanbi shine in tafi Milan, na dawo a 'yantacciya in dauki fansar ransu cikin sauki, dole na bar garin nan. Yaya Asma'u ce ta fado min a rai, ko tana ina? Mikewa nayi na nufi kofa, a rufe na jita hakan yasa na dawo na zauna.
                                

Yarima Haisam ne ya shigo cike da isa ya nemi guri ya zauna ba tare da ya musu kallon kirki ba shi a lalle isasshe. Ganin ba wanda ya tanka masa yasa ya fara binsu dai dai da kallo.
"Meya sameka Fu'ad?" Yayi tambayar yana kallon Yarima Fu'ad.
"Soyayya" Yarima Kassim yayi caraf ya fada.
Tabe baki Yarima Haisam yayi tare da fadin "wata dayan da nayi bana nan komi ya canza kenen?" Ba wanda ya amsa mishi. 
Yareema Ameen ne yayi sallama ya shigo, amsawa sukayi, zama yayi kusa da Yarima Haisam yana fadin
"Saukar yaushe?"
"Dazu" ya fada a takaice.
"Ina ka kai ta don naje sashen naka banganta ba?" Yarima Ameen ya tambaya yana kallon Yarima Fu'ad.
Bai kalleshi bama balle yasa ran zai samu amsar tambayar sa.
"Ashe ba shi kadai bane" Yarima Haisam ya fada ya fuske kamar bashi yayi maganar ba.
"Mene" suka fada dukansu a tare banda Yarima Fu'ad.
Bai basu amsa ba kawai ya mike ya fita.

Washegari, wadda saura kwana daya su Yarima Fu'ad su bar Milan, Barde ne tafe da dakarunsa ya kusa shiga Milan, dai-dai nan sai ga Sarkin Milan da nasa dakarun, nan Barde ya umurci da a karantawa  Sarki  Harun hukuncin sarki a garesa, nan Sarki Harun ya tabbatar da su Barde sunyi nasara a kanshi amma bazai taba bari yayi mutuwar wulakanci ba, zaiyi yaki harsai sunci galaba a kanshi sun kasheshi.
Nan yaki ya hargitse ba abinda kakeji sai karan takubba, nan akai ta fafatawa, Barde duk ya yayyanki sarkin Milan amma shi yanka daya ne a hannunsa. Yaki dai yaki karewa har saida Barde ya cire kan sarkin Milan, nan suka kada dakarunsa suka karasa Milan, Mijin Batula kanwar Fu'ad yasa aka kawo mishi nan yace a cire kansa shima. Sun kashe mutane da yawa kamin suka bar garin suka kama hanyar Ming.
                   Mahaifiyarsa Yarima Fu'ad da Batula kanwar sa basu dade da shigowa Ming ba don ganin Yarima Fu'ad in, bangaren da suka saba sauka aka kaisu da nufin insun huta a fadama Fu'ad sun iso. 
Barde ne zaune gaban sarki da akwatunan katako wanda kan Sarkin Milan ke ciki shida sirikinsa. Murmushin jindadi sarki yayi tare da sallamar Barde.

Wata baiwa ce ta shigo gurin Mahaifiyarsa Yarima Fu'ad, magana ta fada mata kasa-kasa sai gata ta mike a firgice cikin kaduwa tace a tado Batula da take bacci. Umurta tayi da ta saka wasu kaya da aka bata, wasu bayi suka fita da ita. Ta can baya suka bi, suna isa wani guri wasu suna jiransu da dawakai da kuma abin daukar Batula, shiga tayi aka rufe ta, kada dawakan sukayi da gudu suka fita garin. Mahaifiyarsa kam ta rantse akan bazata taba barin Milan Fu'ad na ciki ba, hadimanta sai kuka sukeyi suna rokonta akan ta gudu amma taqi sauraron kowa cikinsu. Wani bawa ta kira ta bashi wasika ya kaiwa Yarima Ameen, fita yayi da sauri don cika umarnin uwar gijiyar tashi.

#Follow
#Vote
#Comment

   

💞NOORWhere stories live. Discover now