💞NOOR
6Dogarai na isa da Ya Ali sashen, aka musu iso amma Ya Ali kadai zai shiga, zaune ya tadda Yarima Ameen kyakkyawar fuskarsa dauke da bacin rai. Gaban Ya Ali sai lugude yake sabida bai san meya aikata ba ko kuma me yake shirin faruwa ba.
"Waya baka zuma ka kawo don dazu?" Yarima Ameen ya mishi tambayar.
Tsoro ne ya kama Ya Ali don shi baisan meye a ciki ba, ganin yayi shiru Yarima Ameen ya mike tsaye cikin bacin rai ya zare takobi ya nunashi da ita.
"Mecece hujjar ka ta neman hallaka Babba? Waya saka?" Ya mishi tambayar a jere.
Tsoro ne ya cika Ya Ali yayi saurin cewa " Allah Ya huci zuciyarka Yarima, wlh sako aka bani kuma asali ma bansan meye a ciki ba. Ta ya kaskantaccen bawa kamata zai nemi kashe Babba"
Wali yayi charaf yace "Karya kakeyi , in gaskiya kake fadi to waya baka sakon?"
"Habu dogari ne na kofa" Ya Ali ya fada a tsorace.
"A kira Habu dogari na kofa " Wali ya fada da karfi, daga waje aka amsa da toh.
Murkususu Ya Ali ya fara nan ya baje rike da ciki kumfa na fita ta bakin shi, da kyar Ya Ali ya bude baki yace wa Yarima "Don Allah ka taimaka ka karasa kasheni in huta da azabar nan don nasan mutuwa zan... nn" ya kasa karasawa sai ga jini ta bakin shi .
Nan Yarima Ameen ya daga takobin ya yanki hannunsa da ita wanda dai dai da bude kofar da nayi. Tsayawa nayi kallon Yarima Ameen wanda mamaki ne ya kamasa na ganina a gurin, tunani yake to me nazo yi? Karasawa nayi da gudu gurin Ya Ali ina kuka na shiga jijjiga shi. Ganin baya motsi kuma ba alamar numfashi na tabbatar daya mutu, wani sabon kuka na saki nan Mimi ta karaso ta rikeni, itama kukan take.
Yarima Ameen kuwa yanzu ya gane meke faruwa, dama tana da yaya? dama dan uwanta ne? To wa yake ma aiki? Shi kadai yake maganar sa a zuciya. Fita yayi, dakin da aka ajiye Babba ya shiga, mahaifiyarsa na zaune idonta sunyi jajur dalilin kukan da tasha. Karasawa yayi gareta, ya riko hannunta cikin sigar lallashi ya fara magana "Hajja don Allah ki daina kukan haka, In Sha Allah zai sami lafiya amma fa sai an dage da Addy's don likitan yace koda ya warke ba lalle gabbansa su dinga amfani ba"
Shiru yayi nadan lokaci sannan yaci gaba "Hajja Mama don Allah alfarma nake nema a gunki hade da goyan bayanki"
Shiru tayi Kawai batace komi ba sai kallonshi da take. Cigaba yayi da magana ganin taki cewa komi
"So nakeyi mu boye Babba a gininsa na cikin kasa wanda sirri ne ba wanda ya san dashi digani sai ke sai kuma Wali mukasan da shi. Zansa a isar da sakon mutuwar sa yanzu gurin sarki"
Sai yanzu tayi magana "Naji duk bayanan ka amma baka tunanin Sarki ya kamata ya sani? Bakayi tunanin abinda zai biyo baya ba inka sukayi tunanin ya mutu. Maganar gawar fa"
itakam har da Allah wannan abin bai mata ba amma tasan halin dan nata da kafiya. Katse mata tunani yayi da cewa "Karki damu komi a shirye yake. Yanzu zanje inna dawo zan sanar dake sauran bayanin"
"Allah Ya tsare sai ka kula da hadimanka" amsawa yayi da amin ya fice. Sai a lokacin na sake fado mishi a rai
"Noor" Ya fada hade da sakin murmushi.
Yasan yi min bayani ma batawa kai lokaci ne don ba wanda zai gansa a wannan yanayin yace bashi ya kasheshi ba. Ka kyaleta kawai, baiwar ka ce fa wata zuciyar ta fada mai.Tunda Mimi ta kawoni daki ba abinda nakeyi sai kuka, lalle mugu bashi da kama, duk da bansan me Ya Ali ya aikata ba amma ni a ganina bai kamata ya kasheshi ba kuma ma duk cewa yana da tausayin da akace. Khairiyya ce ta shigo tana cewa yanzu taji ance Babba ya rasu, nan na fara tunani to menene hadin mutuwar Babba da Ya Ali ? Tabbas akwai wani abu, amma hakan bazai hanani daukar fansar ran dan uwana ba.
Ganin kukan da nake yasa Khairiyya tambayar ko lafiya? Nan Mimi ta shaida mata mutuwar Ya Ali amma bata fada mata kasheshi akai ba. Nan Khairiyya ta fara kuka saboda ta dauki shi tamkar wa a gurinta.
Tunani na farayi akan yadda zan kashe Yarima Ameen , yanke shawara nayi akan guba zan zuba mishi ya mutu amma ina tsoron a bincika a gane nice ban damu ba koda zaa kashe ni amma yan uwana biyu nake tsoron wani abu ya same su.
Tuna wannan turaren da baiwar nan ta kawo nayi, kayana na shiga dubawa ko zan gansa aiko sai gashi. Maidashi nayi na boye ina jiran lokacin da zanyi amfani dashi yayi.

YOU ARE READING
💞NOOR
General FictionStory of Noor and the 5 princes of Ming Empire. Betrayal among them and read as love turns to hatred.