💞 NOOR
16
Duk yanda yaso na farfado hakan ya faskara, tabbas ba numfashi jikina kuma zuciyata bata bugawa amma ya kasa gasgata hakan. Wasu dogarai ne su hudu suka iso da gudu jin ihun kiransu da yakeyi. Babban cikinsu ne ya aiki mutum biyu don kiran likita, dan dubani yayi shima sai yaga kamar na mutu, shiru yayi ya shiga bawa Yarima Fu'ad hakuri akan yanzu likitan zaizo In Sha Allah.
Likitan ne ya shigo da sauri ya umurci su kwantar da ni a kan gado da sauri Yarima Fu'ad yayi hakan. Dubani likitan ya shigayi nan ya tabbatar da gubace mai tsananin karfi amma kuma yanajin alaman bugawan zuciyata kasa-kasa. Wani magani ya bata nan na farfado ba'a cikin hankalina ba na shiga kelaya amai sosai. Ganin aman baki ne yasa Yarima Fu'ad wanda ya gama rikicewa fadin "Jini".
Likitan ne ya fada musu cewa dafin ne ke fita a jikina, wasu magunguna da saiwoyi ya bayar a dafa a dinga bani. Ya mishi bayanin cewa indai ana bani maganin akan lokaci zan warke na farfado a cikin kwanakin In Sha Allah amma kar susa ran farfadowata yau ko gobe.Labarin rashin lafiya ta ya karade ko ina cikin masarautar wanda hakan na nufin har gurin Sarki Ahmad. Nan da nan yasa a kira Barde. Barde na isowa ya haushi da fada akan ya bada umarnin a maida Yarima Fu'ad gidan da yake sauka a tsaresa meyasa ba'a aikata hakan ba? Nan Barde ya shiga bada hakuri sannan ya fita don cika umarnin Sarki.
Ina nan kwance rai a hannun Allah wasu dogarai tare da hadimai mata suka shigo suka fadi sakon tafiya damu can gidan. Dauka ta sukayi Yarima Fu'ad na biye damu har gidan nashi, a wani daki aka kwantar dani. Nan duk sauran hadiman suka bayyana gaban Yarima Fu'ad, nan yaga gabadayan su an canza su, babbar su ce ta fara gabatar da kanta kamin ta gabatar da sauran tare da bangaren da zasuyi aiki. Sallamar su yayi suka tafi.
Kwanciya yayi don ya huta, kamin Maghriba don yana dawowa sallah akwai maganin da za'a bani. Koda zai tafi masallaci ya kira wata hadima ya bata maganin ya umurce ta da ta dafa kamin ya dawo. Yana dawowa daga masallaci dakin da nake ya shigo ya tadda wata baiwa nan kusa da ni, umurtar ta yayi data kira mishi waccan baiwar mai suna Tala kuma ta taho da sakonsa.
Tana kawowa yasa su dagani zaune su jinginar dani, hakan sukayi yanda yace, Tala ya bawa maganin yace ta bani, tana bani tana goge wanda yake zubowa cikin kulawa. Nan zuciyar sa ta sake aminta da ita akan ita zaisa ta dinga kula da ni kan duk wani abu daya shafeni.
Tunda Yaya Asma'u taji labarin abinda ya faru kullum cikin dare sai taci kulanta take bacci. Ina zata saka ranta bayan ta yiwa mahaifinmu alkawarin kula dani, gashi ba Mimi ba Ya Ali, wannan wace irin masifa ce? Tabbas gobe zatasan yadda za'ayi ta ganni.Koda labarin rashin lafiya ta ya isa kunnen Gimbiya Salma ba haka taso ba ita, taso ace na mutu kamar yadda ta umurta, nan ranta ya baci tasa a kira mata Balele.
Balele ne durkushe gaban Yarima Faruk yana ta zazzaga mishi masifa akan aikin daya sashi kan Yarima Fu'ad amma labari ya iske sa cewan lafiya lau yake. Tabbas ba haka yaso ba, amma ya akayi Noor taci abincin shi baici ba, bayan majiyarsa ta shaida mishi tare suke cin abincin? Amma In abincin taci ai zasuji? Lalle bashi kadai bane keson ganin bayansu, tabbas yanzu zamana kusa da Yarima Fu'ad zai zama kariya a gareshi, in har yanason samun yadda yakeso sai ya kawar dani. Kallon Balele yayi cikin bacin rai yace "Kasan yadda zakayi kar a sake samun kuskure, ka kawar da duk wanda zai kawo maka cikas"
"To ranka ya dade, Allah Ya huci zuciyarka" ya amsa don fahimci me Yariman ke nufi.
"Zaka iya tafiya" Yarima Faruk ya fada.
"A huta lafiya" Balele ya fada yana mikewa.Balele na fitowa daga sashen Yarima Faruk saiga bawan da Gimbiya Salma ta aiko kiranshi, nan ya gaya masa sakon suka juya tare sashen nata. Da shigarsa aka masa iso cikin gurin ganawarta na sirri, nan ya shiga hade da sallama, ko kallonsa batayi ba balle yasa ran zata amsa.
Sai da ta jima sannan ta bude baki cike da izza ta fara magana "Ya akayi kayi kuskure?"
"Allah Ya huci zuciyarki, wallahi yanda na mata banyi tunanin zata rayu ba, a jijiyar wuyanta na saka yadda zaiyi saurin isa zuciyarta. Kum..."
"Dalla rufemin baki" Gimbiya Salma ta katseshi a tsawace sannan ta cigaba da fadin
"Ban tambayeka yanda kayi ba, yadda take raye nake tambaya" ta fada rai a bace.
"Kiyi hakuri ranki ya dade amma wlh bansani ba" ya fada a darare.
"Inason kamin ta farfado ta bar duniyar nan, bana bukatar wani kuskuren don hakan na nufin rasa taka rayuwar. Bace min da gani" ta fada tana harararsa
"Allah Ya huci zuciyarki uwargijiyata, a huta lafiya"
Ya fada yana ficewa da sauri.#follow
#vote
#comment

YOU ARE READING
💞NOOR
General FictionStory of Noor and the 5 princes of Ming Empire. Betrayal among them and read as love turns to hatred.