💖💖 Matar Baba na💖💖
💖💖 (My step mom)💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖
💖 💖 Page 1💖💖
💖💖 Written by Hanerh💖💖
Baba sannu da isowa, yawwa diyata kina lapiya ko?
Eh Baba ya kasuwan de? Alhamdulillah.
Wata matashiyar yarinyace da bazata wuce 13years ba, fara ce Amma wahala yasa ta dishe, doguwa ba siririya ba ce, shiko babban mutum ne me kimanin shekaru 52 aduniya, riqe hannunta yayi yace, Ina gwaggon naku? Tace Baba tana daki ka isa zanyi wanke_wanke ne yanzu, ba dazu kafin nafita kinyi ba? Kafin ta bude baki wata matashiyar mata ce da bazata wuce 39years ba aduniya ba, yawwa kadawo ae kai da bakason anasa yarinya aiki, yanzu intai aure ni za'a zaga wannan bayi bane wallahi malam, kada mata kai yayi kawai yawuce yana me mamakin irin halin fatsuma, itako yarinyar kanta a kasa tanufa gun wanke_wanke. Ke Dan ubanki inbaki kiyayenba agidannan wlh senaga uban daya tsayamiki, shegiya mummuna😲 as if tafita kyau ni 'yasu🤣. Kiyi hakuri Gwaggo abunda yarinyar ta it cewa kenan tayi wucewarta tafara aiki.Batadau wani lokaciba tagama, shiga daki tai baida girma sosai se katifa a gefe tashirya Don zuwa islamia, wani madaidaicin daki tashiga na hango Wanda takira da Baba yana shimfide akan sallaya alamun yayi sallah me yake hutawa, da sallama tashiga ya amsa, tsugunnawa har qasa tai tabasa hakurin abunda yafaru sannan tace masa zata tafi islamia, nasiha yai mata sosai akan abubuwan da ake mata agidan, gyada kai tai ta fita daga dakin ta mufa makaranta.
Hawayen daya maqale masane ya fara zubuwa ahankali yana gogesu, babu abunda ke tayar masa da hankali see irin abunda Fatsuma da Lantana ke ma hanne a gidannan, Amma babu abunda yadameta har basa hakuri take ikon Allah kenan.Hanyan makarantasu take tafiya cikin nutsuwa sega wata budurwa da alama sa'anni suke da yarinyar danaji ancemata hanne, Laila kinga munfito atare ko, wlh kekam da zanbiyo Miki nefa, gaisawa sukai suka riqe hannun juna suka cigaba da tafiya.
Karatu ne ke tashi acikin ajin, malamine yashigo yace hanne ina lantana yau kwana 7 kenan batazuwa makaranta lapiya de ko? Malam fitowana bata gida, ok to shikenan.
**********
Sallan asuba ta tashi tai tazauna a sallayanta tana zikiri, acan gefenta kuma yarinyar da ake Kira lantana ce akwance tanata bacci hankalinta a kwance bazata wuce 11years ba, tashinta ta tafara cikin nutsuwa, Amma Ina yarinyar daga tashi ta bata Almighty slap a both cheeks inta, riqe kumatunta tai wasu hawayen baqin ciki da azaba yafara zuba, ke badaman mutum yana bacci yana mafarkinsa me dadi zaki tashesa banza aladiya, tureta tai da qafarta ta juya tacigaba da baccinta.
Tashi tai tafuto waje, marafi tashiga tahada ice tadaura musu abun kari, sannan tafara sharan tsakar gida.
Tagama aikin gida tsaf tsaf gidan kaman bashiba ta shiga daki don Shirin makarantar boko, tagama shiri kenan tafito Sega Baba shima zetafi gun sana'arsa har qasa ta tsugunna tagaisheshi ya amsa cikin sakin fuska, sunkuyar da kanta take Kar ya gane shatin Marin dake fuskan ta, kungaisa da Gwaggo ne, a'a Baba nashiga tana bacci, to ina Lantana ita bazata jebane? Bacci take.
Lantana! Lantana!! Kitashi kishirya kiwuce makaranta, da tsaki ta tashi tana turo baki to Baba, riqe hannun Hanne Baba yai suka fita, Nasiha yaqara mata sannan suka wuce yai gun sana'arsa itama tai makaranta.Babu laifi Hanne yarinya ce me hazaqa don tana gane karatun da ake, aturanci ma babu laifi ita da qawayenta basa magana da junansu da hausa se turanci.
*********************
Alh. Muhammadu shine mahaifin Laila, babu laifi yanada hali dai_dai gwargwado, 'Ya daya tal Allah yabasa, sede Laila bata tolerating nonsense,
da matarsa me kirkin gaske Haj. Maryam itama tana business na gwanjo kuma tanasamun ciniki MashaAllah,
Laila babbar qawar hanne ce tun tele_tele, sun shaqu sosai yanda ba'a tsammani, tana makarantar kudi ita, a makarantar islamia suka Zama qawaye.
YOU ARE READING
Matar Baba na (My step mom)
Mistero / ThrillerA story of a girl who lost her mother at the age of 2, and start a new life in another family. It's all about the difficulty of life, when people you leave around 'em dislike you. The story is about a girl who receive all sorts of maltreatment from...