page**23

212 22 0
                                    

💖💖 Matar Baba na💖💖
💖💖 (My step mom)💖💖

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖

💖 💖 Page 23💖💖

💖💖 Written by Hanerh💖💖

Yau ya kama satin ta guda da 'bata, bangaren ta Kuma sati guda tana kulle, yanzu kamma da kyar take motsawa tsan tsan yunwa.
A ranan Razaki ya yanke shawaran 'balla qofan don ba fitowa zatai ba.

Yakira carpenter akan ya 'balla kofan bayan ya 'balla ya qara gyara Masa. Carpenter yazo da kayan gyaran sa yai daba runsa na makanikai ya 'ballo qofan ta fadai. Idon sa yakak fuskan Hanerh, idonta a rufe Amma be hana ya gane ta Wacce ake nema bane, zaro ido yai yana kallonta amma dayaga alamun za'a gane sa, se ya basar kawae, amma yaqudurci niyyan yau inshaAllah seya ci ku'din da akasa na nemota don baqaramin ku'di bane faaa.

Ya gama aikin qofansa anbasa ku'din aiki, yana sauri saurin yaje police station yafa'da.

Razaki ne yashigo 'dakin binta yai da kallon takaici, se kuma yaga alama bata numfashi. 'Debo ruwar a cup ya sheqa mata, haba da hanzari ta bu'de ido amman ta gagara tashi coz bazata iyaba yunwa yaci qarfinta, harara ya galla mata sannan yasa a kawo mata abinci. ci ta fara kaman hungry loin in da yasamu 'danyen na'ma. se da ta cinye abincin kulan tas sannan tafara dawowa hayacinta, ruwa ya kawo mata shima ta ha'de ta shanye. se da yaga tadawo hayya cinta gaba 'daya sanna yacigaba da mata kallon baki da wayo, ya fara magana.

Ke ajinki kinfin wayyo ko, kimyi ka'dan wallahi, yau se kin rena kanki.

Bata kula saba, illa taci gaba da hawayen da ta ke. tashi tai a hankali tawuje ta gefensa tai van'daki zatai alwala don rama sallolin da ake binta. shiga tai ban'daki bada jima waba segata ta fito tana murmushi.

Tambayarta yai meya faru ta ke cikin fara'a, ta sunkuyar da kai tace masa...

'Bangaren carpenter, jan machine insa yai da gudu don qara sawa police station, gudun da yake ya jawo masa mugun accident agun traffic, inda babban trailer ta niqe shi da machine in nasa, police ne suka zo gurin din temakon gaggawa, amma inaa aikin gama yariga ya gama don kwana ya qare.

Areef ne zaune a parlon Abu shida gaba 'daya siblings insa da iyayensa, sasu a gaba yai yanata rero kuka bashi ka'daiba harda twins da abyaan, me jego ma (Afeena) jurewa kawae ta ke don halin da yayansu ya shiga, sosai abun ya ta'ba zuqatan kowa kai harda ba're ma. police, 'yan sanda ko tawani 'bangare kowa yana iya kacin qoqarinsa amma abu yaci tira.

'Bangaren su Farha ma ba'a magana don iya tashin hankali sunshiga, mommy kam bata iya bacci se sallolin dare take tayi, don har ga Allah jin Hanerh ta ke kamar 'yar cikinta.

Gwaggo duniya ta mata zafi, ta dawo kaman wanda aljanu sukai mata bu'dan kai, inka ganta ta fiffige, gwara sanda ta ke qauye ma akan yanzu kam ba'a magana, ta dawo siri mandi, ga wani ba'kin da tai don rashin wanka da wahala, bata da abincin da zata ci se in taroqa agun masu abinci, namma se an mata wulaqanci.

Tayi deciding ta koma qauyr gidansu itada late Baba, se da tai bara tai bara dakyar ta ha'da ku'din zuwa qauye. Da isarta tasha ta nemi 'dan ku'din data tara ta rasa, an jidesu. Da qafa tun daga tasha har anguwan da ta baro, da isarta taga wayam babu gida ba alamansa, an rushe. anan ne tai kuka me lasisi kam, makwaf tansu ta shiga shima sabin qaurowa ne, taita shiga gidaje, daga ace mata sun qaura, se ace mata me gidan ya rasu matarvta tattara 'yayanta sun koma gidansu, ahaka da kyar. Gidan me anguwa taje, shiko yace daman yana neman me aiki.

Tafara musu aikin wankewanke da shara, da kyar ta ke iya yi, coz abuncin da ake bata ko me 6years iyaka, ahaka take managing. tayi aikin wata guda aka bata salarynta 1500, dagaanan ta qara mai, don dama neman ku'di ta ke wanda zata garinsu da shi.

Tahau motan garinsu, azuciyarta tana ko kwanto ko zata anguwan, amma daga isowarta a hankali taita tafiya har gidansu, tana shiga taga wani dattijo yana zaune a zauren gidan, gaishesa tai ya amsa cikin fara'a sannan ta tambayesa mutanen gidan, irgo sunansu tai amma inaa, dattijo yace mata ai yanzu qaurowansa ma nan gidan yayi kusan shekara ashirin in befiba. jikin tane yai sanyi tace kuma besan inda mutan gidan suka koma ba? yace mata wallahi shi besani ba. Haka ta tashi tafita bakin qofa tai kuka har ta gaji.

Tagumi tai aqofar gidan har kusan maghrib, mutuminnan ne yafito don shiga masallaci ya isketa agurin. magana yai mata akan taahiga gidansa, in Allah ya kaimu gobe seta cigaba da nema ko ta koma gida.

Godia tai masa sosai sannan tashiga, bayani yai wa matansa suma suka amsheta aka bata 'dakin yara. matan mutumin 3 da yara kusan 8, babu laifi mutumin yana da na rufin asiri.

Bayan ya dawo daga masallaci ne suka zauna da iyalensa yace akirata, zuwa tai ta zauna yace ta basu taqaitaccen labarinta.

Labarinta tabasu tun sanda tai aure bata qara zuwa gidansu ba, don gani take 'dan ku'din da ta keda 'yan gidansu zasu kwace mata, har zuwa labarin ta da baba har zuwa yanzu presently.

Sosai labarin ya ta'basu inda mutumin yace ze barta tai sati ta huta sosai, sai asan yanda za'ae. sosai tagode musu gaba 'dayansu. sannan aka kawo mata tuwon shinkafa miyan zogale da purewater me sanyi, su gwaggo an da'de ba'a gamuba ci take hannun baka hannu kwarya.

'Bangaren su Hanerh tambayanta Razaki yai, anan take fa'da masa tanada buqatan pad, wani baqin ciki ne ya maqale masa a maqogaro amma yace ai tananan da shi dan ubanta. aikan yaransa yai, harda kayayyaki ma ya sai mata masu kyau. itako murna kaman ze kasheta sannan tasa a ranta inshAllah kafin ta gama period zata samu wani barar imshaAllah burinsa baze ta ba cikaba.

Matar Baba na FANS ma haka sukace. Don suma basa iya bacci kullum addu'a kawae da salloli ko kuwa....

💖💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖💖💖

Alhamdulillah
Page 23 is already here🤗
Hope you're I'll enjoying my book?

💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖💖


Tell your friends to tell their friends, if they don't have the app (Wattpad) tell them to download it, install it to their phone, open their own acc, follow me @Hanerh Yahya and search my book Matar Baba na (My step mom).


And

Don't forget to hit that little star 🌟 and the bottom, and also don't forget to visit my comments section to pour out your heart 💓 you guyz will bring a smile to my face 😊
Lots Of Love 💖
Hanerh Yahya💗

Matar Baba na (My step mom) Where stories live. Discover now