page**9

311 20 0
                                    


💖💖 Matar Baba na💖💖
💖💖 (My step mom)💖💖

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖

💖 💖 Page 9💖💖

💖💖 Written by Hanerh💖💖

Abba ne yafara tambayanta..

Abba: Baiwar Allah mesunanki?

Hanne: Sunana Hanne.

Abba: awani gari kike?.

Hanne: fadamasa qauyensu tayi.

Abba: ina iyayenki?

Hanne: Bansan inda sukeba

Abba: kaman yaya? To meya fito dake dagudu har kikai accident.

Hanne: guduwa nai.

Abba: Daga gidanku?

Hanne: eh.

Abba: medalilin hakan?

Hanne: kasheni zasuyi shiyasa.

Abba: iyayennaki?

Hanne: kukatasa tanacewa wasu mutanene sukeson kashemu Ni da Baba.

Labari tabasu kaf akan abunda ke faruwa, har tsintanta da akai, babu wanda be zubda kwalla agun ba don tausayi, Abba ne yamata alqawari inshallah duk inda iyayenta suke na asali zeyi qoqarin nemosu, Amma abunda ke ruda masa tunani shine, tace lokacin bata wuce 2 to 3years ba to ai iyayenma bazasu ganetaba. Shiga daki yai yana nazari inda yatuno da 'yarsa Hanerh, wacce har yau besan inda takeba, tamutu bata mutuba oho se Allah, namma matarsa tafado masa kuka yai sosai inyatuno gawanta da aka kawo masa, irin mutuwar wulaqanci da akamata

Abba da Haydar da Hanne ne suka dau hanyan qauyensu Hanne, suna isa suka iske abunda yafaru, labari akabasu na irin kisan da akaiwa Baba, Hanne Tasha kuka har na auzubillah, hakuri sukaita bata, anan akasanar musu Gwaggo ma tagudu bata garin haka Razaki ma, dawowa sukai kowa jikinsa yai sanyi.

Some years later

Duk irin mu'amalan da Hanne keyi akan idon Abba, don tuni yamayar mata sunan Hanerh wai zena tuno da 'yarsa, duk abunda take akan idonsa, mu'amalanta sak na matarsa, kullum yahada ido da ita se gabansa ya fadi, haka itama, kamanninta sun fara canzawa zuwa na Margayiya sak. Ranan yanazaune a parlon yayo Kiran Hajja da Haydar, Zama zukayi sannan yafara musu magana..

Abba: Haydar da Hajja don Allah baku lura da abunda nake lura agidannanba.

Hajja: Ni nafika kura Alhaji don ta ita muke kwana, wallahi duk halayen Margayiya shitake.

Haydar: wallahi ban luraba se da kukai magana.

Abba: Inaji ajikina wannan jinanace.

Hajja: Tabbas ban fidda tsammani ba, don inkalura dakyau kamanninta yafara canzawa zuwa na Margayiya.

Haydar: Ni kasan meke damuna Abba? Kagade Umma mahaifiyata ce ko, Amma wallahi inazarginta dasa hannu akisan Margayiya, abunda besaniba Abba yadade da abun aransa.

Abba: shiru yai na wadansu lokuta sannan yace me abunyi?

Haydar: wallahi Abba kakaita wani gidan tazauna, semuna zuwa dubata, inbahakaba wallahi bazamu taba gano bakin zaren ba.

Hajja: Tabbas haka za'ayi.

Abba: to Amma gidan wa zankaita?

Haydar: ina amininka Daddy?

Abba: kana nufin Alh. Ibrahim bula?

Haydar: eh shinake nufi Abba.

Abba: kasanfa ba mazauna Nigeria bane.

Matar Baba na (My step mom) Where stories live. Discover now