💖💖 Matar Baba na💖💖
💖💖 (My step mom)💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖
💖 💖 Page 6💖💖
💖💖 Written by Hanerh💖💖
Washe gari qarfe 11 daidai Razaki yabugo sallamansa, amsawa tai cikin murmushin mugunta sannan taimasa iso, shigowa yai harda kawo masa ruwansha.Razaki: Kinga nacika alqawari ko?
Gwaggo: ai ka kyauta kuwa.
Razaki: to aje gashi.
Gwaggo: Ai Kai kasan yanda tsarinku yake.
Razaki: Wai ma mutuminnan ni yadaga hannu ya mara.
Gwaggo: Innalillahi mari????
Razaki: Mari Mana.
Gwaggo: Da yaushe akai abunnan bansaniba?
Razaki: Jiyafa nazo fita muka hadu dashi.
Gwaggo: Karka damu aikin gama ae ya gama.
Razaki: Nayi alqawarin sena sasa baqin cikin dabai taba zata ba, sena sasa kukan zuci dana hawaye lokaci daya, nayi alqawarin kafin mutuwarsa see ya gwanmace sanin Razaki arayuwarsa kuma bana alqawari ban cikaba wallahi.
Gwaggo: shiru tai tana nazari irin mutuwar da Malam zeyi, Amma dake tamai da zuciyarta na kafurai ga kuma son kudi bazata janye qudirintaba.
Gaskia nima bangoyi bayan abarsa ba, ai wallahi acikie nake da Malam kabari kawai.Razaki: to Kinga ae. Yanzu de daga wani sati aikinmu zefara.
Gwaggo: to nawane kasona?
Razaki: karki damu, inde nabiya buqata na zanbaki dubu dari bakwai (7hundred thousand).
Gwaggo: Ayyiririiiiii don Allah karka fadamin wasa muyi maganan gskia.
Razaki: Yamiki kadan me?
Gwaggo: Ah ni na'isa ashe akwai randa zanriqe dubu har dari bakwai a hannuna, Kai Allah nagode maka.
Bankwana sukai yawuce abunsa.
Abangaren Lantana tashirya tsaf ita da Dan birni zasuzo gida.
Ranan Kam Gwaggo tai farin ciki mara misaltuwa, dan kayan abinci harda kaji😋 Baba ko baikula takansuba dukda gaisuwar dasuka tamasa amma kaman Rayha da bata gurin. Tawuni liqis se around 5pm suka shirya zasu tafi, sannan tayiwa Gwaggo alqawarin inshallah ranan alhamis zatazo sutafi, kwana 3 nangaba kenan, har tazo fita daga gidan Baba yafito daga daki yace Wallahi Wallahi Wallahi idan kikasa qafa kikafita daga gidannan Allah ya isa, tsayuwa tai tana jiran umurnin uwarta, zaki fita ko sena takaki, bawan Allah yananan yana jiranki Amma kina tsaye, juyawa tai tawuce mota. Al'ajabi Kam ya cika Baba Yanzu yarinyar nan tazabi tsinuwa kenan to ai hikenan zamugani.
Ranan Wednesday Baba yafita shikadai, Gwaggo tai Kiran Hanne, jikintane yai la'asar da taji kiran batasan mesa ba, Amma tajure ta je.
Da sallamarta tashiga dakin Gwaggo, inda Gwaggo ta amsa tace tashigo tazauna, shiga tai tasamu gefe tazauna Gwaggo tafara da..Gwaggo: Hanne inason mui magana dake Amma bansan yazakidau abumba, inason nafada Miki gaskia ne don boye-boyen yayi yawa.
Hanne: Toh fa Gwaggo wanna wata muhimmiyar magana ce haka?
Gwaggo: Zakijita yanzu banason kinuna tashin hankalinki, kinmn alqawari?
Hanne: Inshallah zanjore koma meye ne.
YOU ARE READING
Matar Baba na (My step mom)
Mystery / ThrillerA story of a girl who lost her mother at the age of 2, and start a new life in another family. It's all about the difficulty of life, when people you leave around 'em dislike you. The story is about a girl who receive all sorts of maltreatment from...