💖💖 Matar Baba na💖💖
💖💖 (My step mom)💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖
💖 💖 Page 5💖💖
💖💖 Written by Hanerh💖💖
Ganin mutum sukai atsaye cikin gida har ya shigo, da rawan jiki Malam yafara magana, haba bawan Allah ai tunda kai sallama Kam kasan za'a fito ko?
Razaki: Na ga bame niyyar fitowa shiyasa, yanzu ba wannan ba ya batunmu na wannan yarinya Hanne ne?
Baba: ni agaskia bazan iya bawa 'yata Wanda besan muhimmancin aureba, Dan shaye-shaye, me neman mata, uba nagari yanazabawa 'yarsa Wanda zekula da ita haqiqan ba wanda besan darajartaba, don Allah don Allah kayi hakuri kanema dadan ka, bugu da qari kaika kashe mata babbar qawar... Kafin yaqarasa bashi dinba har Hanne kuka suka fashe dashi, nanne mutuwar Laila tadawo musu sabo gal aleda, abangaren Gwaggo ko se yamutsa fuska take dama mutuwar be shigetaba sosai.
Razaki: Malam ba maganar banza nazo kamin ba, uban wa yace maka ba tsakani da Allah zanriqe maka 'ya ba, ni har cikin zuciyata inason tane, yana gamawa yai ficewarsa.
Ba wanda yaqara yiwa Dan uwansa magana har safiya, Baba yafita kasuwa, Hanne ko dama suna hutu, Gwaggo ne takirata, tashigo dakin kanta aqasa.
Gwaggo: Wallahi ke bansan wata irin jaka bane, tsakani da Allah arziqi nabinmu kina kaucewa, so kike muzauna atalauci ne ko me?
Hanne: Gwaggo ba haka bane amma karki manta shiyai sanadiyyar mutuwar Laila fa kuma babu wanda besan saba da neman 'yan mata da shaye-shaye, haka kikeso naje gidan yakashen ya lalatamin rayuwa?
Gwaggo: Kinga dabbiya me sauraron zancen maqiya, yanzu haka ba shi yakashe Laila ba sharrine irinna 'yan gari, yanzu de kawai kiyadda kinji diyata?
Babu abunda Hanne tace illa tawuce tacigaba da aikin gabanta.
Gwaggo na zaune adaki wayarta tadau qara, sabon number ne yakirata kamar bazata daukaba amma ta cije, tana sawa akunne taji muryan da har tafidda tsammanin qara jinsa a duniya.
Lantana: Gwaggo kina lapiya?
Gwaggo: Lantana! Takira sunanta da qarfi.
Lantana: Na'am Gwaggo yakuke yasu Baba?
Gwaggo: Lapiyan kowa qlau Alhmdllh don Allah kiyi hakuri kidawo gida Lantana, wallahi hankalina ba akwance ba bansan wani hali kike ba, gashi Babanki ya azalzalawa rayuwata, don Allah kidawo.
Lantana: Gwaggo inacikin daula kice nadawo qauye wallahi Gwaggo har da mota fa nakeda, Kinga wayoyina, ai Nikam nacarawa qauye wallahi.
Gwaggo: Haba 'yarnan karki fadamin, ubankima bai taba Jan motaba arayuwarsa se ke maqaryaciya kawai.
Lantana: wallahi Gwaggo nake fada Miki. Inshallah nakusa nazo nadaukeku mukoma birni ma.
Gwaggo: Don Allah kizo yau wallahi ni harnaji kaman nadawo tsuntsuwa naje inga daulan da kike sha .
Lantana: Karki damu Gwaggo inshallah zanzoni bada jimawaba, dukanku harda su Hanne, da Baba duk da nasan dakyar Baba ya yarda.
Gwaggo: Kibar talakan banza, ga talauci ga baqar zuciya, wallahi ko bejeba mu ma tafi.
Lantana: Gwaggo zamufitane se anjima.
Gwaggo: To yashe zaki qara kirana to mugaisa?
Lantana: Karkidamu Gwaggo zankiraki zuwa gobe, don yau munada party agabanmu.
![](https://img.wattpad.com/cover/228102194-288-k135738.jpg)
YOU ARE READING
Matar Baba na (My step mom)
Mystery / ThrillerA story of a girl who lost her mother at the age of 2, and start a new life in another family. It's all about the difficulty of life, when people you leave around 'em dislike you. The story is about a girl who receive all sorts of maltreatment from...