page**2

526 37 4
                                    

💖💖 Matar Baba na💖💖
💖💖 (My step mom)💖💖

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖

💖 💖 Page 2💖💖

💖💖 Written by Hanerh💖💖

Hanne: Dasauri Hanne ta tareta, ke Laila kibari wallahi zaki jaza mana fitina a garinnan, kiyi hakuri don Allah.

Laila: wallahi kaci sa'a badan kadanba, da karena kanka yau😙.

Razaki: Ai wallahi dakin barta da tagane ita qaramar 'yar barikine, lallai yarinya da sede uwarki tahaifo wata bade keba wallahi.
Seda mutane suka cika suna basa hakuri, kowa mamakin qarfin hali irinna Laila yai, yarinya da ita Amma har ta iya tsayuwa agaban wannan makashin da kowa yasansa, lallai batasan ciwon kantaba.

Hanne tana zaune a tsakar gida gefenta kuna Lantana da Gwaggo suna hada plan yanda Lamtana zatai tafiya itada saurayinta za'a nuna mata gari afadarsa, sungama hada komai sun tsayar akan zasuce zataje gidan qanwar Gwaggo a kauyen da take aure.
Dawowar Baba gidan yaga Gwaggo ta tarbesa bakaman yanda tasaba ba, mamaki yacikasa amma ya fusge kawai.
Bayan yahuta ankawo masa ruwa yasha saiga Gwaggo tashigo.

Gwaggo: Malam daman magana nakeson kuyi.

Baba: inajinki Fatsuma, yaukuma wani maganane haka me muhimmanci.

Gwaggo: Daman qanwata shatu ce takirani se mita take wai Lantana bata taba zuwaba, shine nayanke shawaran gobe inshallah zata je.

Baba: To ai kingama yanke hukunci tunda har zata tafi gobe.
Tasan gidanne?

Gwaggo: zatai amfani da wayan hannuta suna kwatance tunda ai motoci nashiga qauyen.

Baba: Allah yakaimu.
Abunda Baba ya iya cewa, don begamsu da maganan ba, musamman yanda se biyayya take masa, Amma babu yanda ya iya.

Washe gari qarfe 7am Baba da Hanne suka fito zasu tafi, Baba zeje gun sana'arsa inda Hanne zataje makarantar. Sallama sukai da Lantana inda Baba yace tamika masa gaisuwansa sosai, Hanne mamaki kawai take don ita batamasan sunada 'yan uwa ba, to meya hana ajeda ita taga 'yan uwanta? Allah yabarwa kansa sani. Fitarsu waje Baba ya mata nasiha daidai akan karta damu itama zataje inshallah.

Lantana tagama shiri tsaf tadau kayanta 'yan kasan akwati don za'aje cikin birni, misalin qarfe 8:20am saurayinta wato Umar suna cemar Dan birni yakirata awaya akan yana bayan gidansu da motarsa tafito su tafi, bankwana sukai da Gwaggo inda Gwaggo tace takawo mata tsarabar wannan salular da ake shafa ta dinnan (Android Phone)
To kawae tacemata don tana sauri ta fice, shiga motarsa tayi qirar 406 2019 ga AC na tashi MashaAllah.
Gaisawa sukai sannan yaja mota suka fara tafiya.

******Birnin Abuja*******

Wani qerarrun gida jene acikin wani estate, Wanda bazaka gane Wanda yafi haduwa ba agurin, tsarin gidajen iri daya amma kala daban_daban, na sha'afa akallon aljannar duniya seji nayi anyi horn a bakin wani gida, bude gate in akai sannan motar tashige, MashaAllah garin dadi na nesa don gidan Kam yatafi ta marubuciya.
Shiga yayi tana biye dashi abaya har suka qarasa babban parlor, shima babu laifi ya tsaru, 2bed rooms, single parlor and kitchen ne agidan, takasa Zama saboda kalle kallen qauyanci. Zauna mana, muryansa ta tsinta inda ya dawo da ita daga tunane tunanen da take, Zama tai ahankali kan lallausar kujeru brown clour, inda akai musu kwalliya da white stones, shiga daki yai yaahige toilet yai wanka sannan yashirya cikin maroon 3qtr da blach shirt, sannan yacemata tashiga tai wanka itama, dayan dakin yanuna mata dake ryt side insa, tashi tai tana taku ahankali don ita adole tsoron carpet in dakin take, bema lura da itaba se zaman da yai a kan kujera.

Da shigarta dakin takai 5mns tana qarewa dakin kallo don tunda Baba da Gwaggo suka aifeta bata taba ganin gida irinsaba, infact ko kamarsama. Wani door tagani take gun tadan tura se taga abude ma yake, Wai! Wai!! Wai!!! Abunda yafara zuwa bakinta kenan, kafarta tasa ahankali tashiga toilet in, girmansa ba sosai ba, tamarasa yazatai tasamu pampo, hannu tasa tadebo ruwan cikin toilet sit tasa abaki harda santi wai ruwan birni.

Matar Baba na (My step mom) Where stories live. Discover now