chapter 13

585 99 15
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

         *BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
  And *AISHA ALTO*

13🧝🏻‍♀️
Shagwaɓe fuska nayi kaman zanyi kuka Ruma ta janyo ni jikin ta tana dariya,
"Haba ƙawata ba gani nan ba idan ma tsoro kike ji sai muje ɗaki na ki kwana, kinga aunty Yusran taki da kanta tace ki kwana gari babu lafiya ba zamu barki ki tafi ba gaskiya"

Shikkenan ni rayuwata a yawo da kwanan gidan mutane zai ƙare? Babu gida guda ɗaya da za'a kira da namu wanda nake zaune a ciki daga nayi kwanaki a nan sai a cilla ni can,

Saka ƙasan hijab ɗina nayi na share hawayen da ya fara sauƙo min, ina ɗagowa naci karo da nana tana watsamin wani mugun Kallo, ta miƙe tare da faɗin
"Idan bata son zama ku barta ta tafi mana! Duk abinda ya same ta ai ita taso" ta ƙarasa haɗe da tsaki ta bar parlorn,

Ohh Allah, ni bansan me nayi wa baiwar Allan nan ba zuwa na gidan nan kwata_kwata baifi awa 4 ba amman duk ta ƙuntata ma ranta tana neman hana ni sukuni,

"Hmm auntyn sakalci, bamu cinye mutane a cikin gidan nan ki kwantar da hankali na kwana ɗaya dai ko babu komai comfort ɗin yafi na wurin da kika fito, ga kuma luxury"

"Haba Sulthana, wannan wani irin magana ne?" Cewar Batool "idan ba zaku lallaɓa ta ba ku rabu da ita, yau ta fara zama cikin gidan nan amman sai kun nuna mata hali? Ao ko babu komai ita baƙuwar mu ce ya kamata mu karrama ta"

Taɓe baki tayi ta miƙe tabi hanyar da Nana tabi, karere ba'a iya samun wuri ba yanda take bragging ɗin nan sai ka rantse da Allah gidan su ne, don nima abinda nayi tunani kenan itama ƙanwar Sitifid ce,

Muna kam abin duniya ya ishe ta ita bama tamu take ba, ta zurfafa cikin tunanin yanda zata nima ma kanta hanyar tafiya ibadan, niman sirrin nan take ruwa a jallo dan shine kaɗai makamin da zata yi amfani dashi wajen cikar burin ta,

Jin an fara kiran sallah yasa duk muka tashi suka jagorance ni zuwa ɗakin su aunty Zaytoon muka yi alwala, ina fitowa na samu sun shimfiɗa min darduma ga hijab a kai na ɗauka nayi sallah,

Daga nan muka fito wasu suka shiga kitchen suna fito da warmers ɗin abinci wasu kuma suna shirya kan dining, nima don kar ayi babu ni na shiga cikin masu shirya dining saboda manyan ne su aunty Batool, na san ban isa na shiga cikin wa'incan ba yanzu fitinannu biyun nan su saka ni a gaba,

Ruma na ganin haka ta barsu ta dawo cikin mu sai arhantar mun da kyakkyawar murmushin ta take yi, cikin nutsuwa tace
"Saudat amman ke ba ƙanwar aunty Yusrah bace ko?"

Girgiza kai nayi nace "A'a ni ƴar uwan mijinta ne, daga ƙauye nazo zaki ma iya kira na da boɗɗi haka aka fi sani na da..."

Da sauri ta matso jiki na cikin kunne na ta raɗa min "kada kiyi su Nana suji, kawai idan an tambaye ki kice ke ƴar garin nan ne"
Kinji?
Gyada mata kai nayi muka ci gaba da aikin gaban mu,

Muna gamawa aka sake tattare parlor sannan aka sauƙe duka curtains ɗin gidan aka bulbule ko ina da turaren wuta muka shiga yin sallan isha,

**********
"Allah sarki ƴar ƙanwa ta, bansan yanzu a cikin wani hali take ba"

ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅Where stories live. Discover now