(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd
*BY*
*UMMU NAJMA**DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO**Babban jin daɗin rayuwa shine ki kasance cikin rufin asiri a gidan iyayen ki ko gidan mijin ki, a duk yanayin da muke ciki na ƙasa damu zamu dinga dubawa ba na sama ba, Allah yayi mana babbar ni'ima mu gode masa*💡
03🧝🏻♀️
"Ƙwaya fa kace??"Dariya Khamis yaci gaba dayi har hawaye suna sauƙa saman fuskar shi, yana gyada mata kai ko magana ya kasa,
"That means duk abinda nake ji kaman a saman ɗakin nake kwance ko inji na fita hayyaci na ko in dinga ganin abubuwan dake zagaye dani suna motsi da kuma abubuwa da yawa dake caza min ƙwaƙwalwa ko tashi na kasa yi ashe duk effect ɗin ƙwaya ne?"
"Over dose ma kuwa, biyu sukace ake sha ni kuma nake baki uku" ya faɗa tare da sake saka dariya yana riƙe cikin shi, Yusrah kuwa sake baki tayi shaaa kawai tana kallon ikon Allah gaba ɗaya Khamis ya gama goge mata hadda, ta rasa me zatayi masa ko kuma me zata ce masa ɗaya,
"Ashe ba laifin Jannat bane da take da gagara kaman rainon maza, ka gama mata training tun tana ciki" sai kuma tayi tagumi cikin jimami tace "oh Allah yayi yarinya ta tana da tsawon rai ne ba don anyi gaggawar bani agaji ba da na rasa ta, maybe nima da ka daɗe da rasa ni wallahi banyi tunanin zanyi rai ba lokacin da nake kwance a asibiti, ban taba shiga mawuyacin hali irin wannan ba" ta ƙarasa hawaye na zuba a idon ta ba tare da ta sani ba,
Barin dariyan Khamis yayi ganin sauƙar hawayen ta, ya cire hannun da tayi tagumi dashi sannan ya rungumeta suna a zaune yana shafa bayan ta a hankali,
"Shiyasa nake roƙon ki ki yafe min baby, nasan halin da na saka ki abu ne mai wuyar mantawa, it's ok ma idan baki son ki yafe min amman ki daina zubda hawayen ki don Allah, na faɗa miki ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba suna ƙona min zuciya sosai"A maimakon tayi shirun saboda rarrashin ta da yake yi sai ƙara sautin kuka tayi tana yinshi mai gunji
"Wallahi na yafe maka Abban Jannat zuciyata ba zata taɓa iya zama da fushinka a cikin ta ba tana son ka da yawa, i just can't help it when I think of the past""Then it's better if you stop thinking about it, it might affect my baby ummm" ya fada yana share mata hawayen fuskar ta,
"kinga kin manta ma baki rama kiss dinki na dazu ba, idan ya kai gobe kuma ba zan yarda ki rama ba idan kin yafe kuma Shikkenan"
Jan hanci tayi ta juyo tana kallon shi da rinannun idanuwanta ta murguda mishi baki haɗe da faɗin "na yafe"
"Bazai yiwu ba, idan kin yafe ni ban yafe ba so silently come here ki rama abun ki"
**********
"Tsoro ɗaya? Kinsan Allah yanda naji muryan shi kaman mayunwacin zaki yayi kururuwa wai Rumaaaaaa saida na saki fitsari a jiki na"Dariya suka saka gaba ɗaya dakin banda Nana da Sulthana da suka haɗe fuska suna faman harare_harare, timm suka ji ƙaran faɗuwan Batool a ƙasa saboda tsananin dariya,
YOU ARE READING
ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅
General Fiction"Nafi son Hamma Zayyad aunty Yusrah amman idan na zaɓe shi a kan Hamma sulaiman kaman nayi butulci ne, zuciya ta ta cunkushe na rasa wanda zan zaba a cikin su ki bani shawara yaya zanyi?"... Her destiny is complicated, she is so young to face all th...