(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO**Sorry for the delay👏👏, ina ɗan fama da mura ne na kwana biyun nan irin mai saka ciwon kai shiyasa kuka jini shiru*
49🧝🏻♀️ (A)
kwance nake a ɗaki tare da wasu daga cikin ƙawayena dake ta faman shiri domin da an sauƙo daga ɗaurin aure za'a zo ɗaukan amarya saboda wuni ɗaya za'ayi a yau ɗin za'a kaini ɗaki na.
Wani irin mummunan bugu zuciyata tayi yayin da na jiyo sautin guɗa daga tsakar gidan mu da shewan mata suna faɗin shikkenan an ɗaura, ɗaukan wayana nayi na kunna ina kallon lokaci 11 har da minti 30, kifa wayan nayi a kan gadon da nake kwance na fasa ihu ina birgima inajin zuciyata na ƙonewa.
Shikkenan rayuwata ta gama lalacewa daga yanzu nayi bankwana da abin sona har abada, Zayyad ya riga da ya haramta min ni da shi mun tashi daga matsayin abu guda mun koma abubuwa guda biyu ma banbanta. Rayuwana ta ƙare..... I have no reason to live anymore.....Kuka nake yi kaman raina zai fita, wallahi sai yanzu nasan nayi kuskure da na zabi auren babban yaya, indai ba Zayd na samu a mijin aurena ba da haƙura nayi na ƙarasa rayuwana ba tare da nayi aure ba zaifi min.
Shigowa Hanan da innata sukayi da sauri da sula jiyo kukana, ta hawo gadon tana riƙoni ina zamewa kaman karkashi.
"Lafiyan ki kuwa Saudat? Ko wani abu ne ya faru dake ki faɗamin Please"Murmushi Inna tayi hawaye na bin idanunta ta, tasan wataƙila saboda taraddadin sabon rayuwan da zan shiga ne nake haka, wataƙila baƙin cikin sake rabuwa dasu ne ya jawo haka, wataƙila kuma don sai yanzu ne na girma nayi hankali nasan mai aure yale nufi shiyasa haka. Amman a aurena na farko ban gwada wani act na kunya ko damuwa ba illa murna da rawan kai da na dinga yi har saida na jawo musu magana wurin mutane.
Riƙo hannuna inna tayi ta ciro ni daga jikin Hanan sannan ta saka ni a jiknta ta rungume tana ƙoƙarin tsaida hawayenta don ta sami daman rarrashina.
Sake ruƙunƙumota nayi kuka na yana daɗa ƙuntata, inajin kaman na faɗa ma Innata na fasa auren na yafe. I cannot imagine living in the same place as Sulaiman, lying on the same bed as him, serving him, bayan ga Zayyad ɗina a can yana rayuwa shi kaɗai.Har saida naci kukana na ƙoshi kafin Inna ta gyara min kwanciya a kan gadon tace nayi barci na huta kafin muzo tafiya kada kaina yayi min ciwo.
Ciwon kai na gobe kuma?Tattaran sauran mutanen ɗakin hanan tayi suka fita don a barni na huta, ina ganin haka bayan ƴan mintuna na siɗaɗa na gudu daga gidan ba tare da na bari wani ya lura ba.
*********
Tsugunawa Sulaiman yayi a gaban aunty Amarya dake zaune a kan waiting chair na asibiti tana sharɓan kuka, riƙo hannunta ɗaya yayi ya dunƙule cikin nashi don ya sama mata nutsuwa shima idanunshi sun gama kaɗawa sun sauya kala."Aunty" ya kira sunanta cikin nutsuwa, "Zayyad will be fine i promise you, ki daina damuwa, ki daina kuka and pray for him, he will be alright insha Allah"
Ɗayan hannunta ta saka ta share hawayen dake zubo mata cikin kasashshiyar muryaa tace "idan wani abu ya shame shi fah? Ba zan iya yafe ma kaina ba, duk halin da ya shiga nine sanadi, what if zuciyan shi ta buga and i happen to lose him" ta ƙarashe maganar tare da sakin kuka mai gunji.
YOU ARE READING
ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅
Narrativa generale"Nafi son Hamma Zayyad aunty Yusrah amman idan na zaɓe shi a kan Hamma sulaiman kaman nayi butulci ne, zuciya ta ta cunkushe na rasa wanda zan zaba a cikin su ki bani shawara yaya zanyi?"... Her destiny is complicated, she is so young to face all th...