chapter 14

537 102 11
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

🤍💚🤍
    *ƘARAMAR BAZAWARA*
           💚🤍💚

    _(Cigaban matar kulle)_

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

         *BY UMMU NAJMA*

*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
  And *AISHA ALTO*

*Wannan shafin naku ne ƙanne na kuma ƙawaye na, Haleesatou ƴar mutan Niger da Saleehatou yar mutan Nigeria😅*
Godiya mara adadi❤️

14🧝🏻‍♀️
"Dadyn Arif ina kwana" muryan Zaytoon ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya lula, yafi 1 minute tsaye yana kallo na wanda ni banma lura da hakan ba tunda nayi mishi kallo ɗaya na maida hankali na kan junior yana ci gaba da bani abinci a baki,

Gyaran murya yayi yana ƙoƙarin tattaro nutsuwar shi sannan ya amsa gaisuwan ta, ɗaya bayan ɗaya suka dinga gauda shi yana amsawa cikin taƙama da jin kai, ganin haka yasa nima na gaida shi amman kuma a maimakon ya amsa sai ya haɗe rai tare da kawar da kanshi daga gare ni ya tambayi Ruma
"Wacece wannan?"

"Umm sunan ta Saudat, ita ƙanwar aunty Yusrah ne wanda take kawo man..."

Dakatar da ita yayi da hannun shi yana daɗa ɗaure fuska yace "bani buƙatar wannan bayanin"
ko Ruma da ya disga saida taji ba daɗi ballantana ni,

He made me feel out of place, ashe ba zallan Nana da Sulthana bane suke da wulaƙanci harda manyan su, daman mutane suna faɗa masu kuɗi basu ganin darajan talaka, wasu hawayen sakalci da na saba dashi naji suna ƙoƙarin sauƙo mun nayi saurin sunkuyawa tare da ɗaukan serviette ɗin dake gefen plate ɗina ina share su,

Babu wanda ya lura da haka bayan shi, ban san me ya shigo dashi ba amman muna haɗa ido bayan na ɗago naga ya juya ya tafi, a zuciya ta ina roƙon Allah yasa har na bar gidan kada na sake haɗuwa dashi don har ga Allah tsoro yake bani,

Tsayuwa yayi a ƙofar part ɗin su Zayyad don bai isa ya shiga ciki a yanayin da yake ba, sosai ranshi ya ɓaci da abinda nayi, matsalar hidima da yara kenan gaba ɗaya basu da hankali, yanzu daga yaƙi amsa gaisuwana na kama kuka, meye amfanin kukan kuma oho!
Lallai yana da aiki a gaban shi indai yana son mallaka na to dole ya tankwasa ni nabi tsarin shi,

Yana gama ayyana haka ya wuce ciki,
Aunty amarya ya samu itama tana breakfast tare da Fa'iza da sadiƙ , sai a lokacin ya samu damar karyawa don tunda aka kira shi aka faɗa mishi halin da Zayyad yake ciki ya rasa nutsuwar shi,

Suna ganawa ya shiga ɗakin shi, a kwance ya hango shi yana barci yayi wani iri gaba ɗaya jikin shi a sake bakin shi ya bushe, a saman bedside drawer ya zauna sannan ya riƙo hannun Zayyad cikin nashi ya ƙura mishi ido amman ganin raunin dake tattare dashi yasa yayi saurin kawar da kai tare da jan dogon numfashi da yayi sanadiyyar farkawan Zayd,

A raunane yake kallon cikin idon yayan shi da ya kaɗa yayi jaa yace
"Kayi haƙuri babban yaya ba abun da kake tunani bane"

"Zayd yanzu ka yarda zaka barni na tambaye ka matsalar ka? Tunda yanzu idanu na sun gane mun baka cikin yanayi mai kyau, Zayd me yasa kake ma kanka haka ne? Baka kiyaye abinda zai saka hankalin mu tashi"

Da ƙyar ya iya daddafawa da taimakon Sulaiman ya tashi ya zauna, sai yanzu ya lura da ramar da yayi a wuni ɗaya kawai,
Cikin low voice yace
"Babban yaya nima bansan dalilin hakan ba, kwana biyu na kasa gane wa kaina kwata_kwata, sannan duk wasu sharaɗi da dokoki da rayuwa na ya ɗauru a kai har gobe ina kiyaye su, duk abinda na san zai jawo mana damuwa bani son..

ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅Where stories live. Discover now