(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
🤍💚🤍
*ƘARAMAR BAZAWARA*
💚🤍💚_(Cigaban matar kulle)_
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA
WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd*BY UMMU NAJMA*
*DEDICATED TO, MAI DAMBU*
And *AISHA ALTO*23🧝🏻♀️
Tunanin halin da Zayyad yake ciki ya addabe ji tunda na dawo gidan aunty Yusrah na rasa sukuni, aikin ranan ma dai kawai inayin shi ne amman hankali na bayi jiki na domin yau ya zamo min ɗaya daga cikin baƙin ranaku da na gani a rayuwata,Ga abinci amman na kasa ci ga TV abin sona amman na kasa kallo, duk yawan surutu na bakina ya mutu abin har mamaki ya bawa aunty Yusrah don bata saba gani na a haka ba,
Dukda basu kallo a azumi amman na musamman ta kunna min draman hausa bayan munyi sallan tarawih da mamakin ta ko kai duba na wurin da tvn yake banyi ba na koma ɗaki, na ɗau alƙur'ani ina karantawa ko zan samu sauƙi a cikin zuciyata,
sannan ita Al-ƙur'ani ayoyinta waraka ne ga duk wani cuta idan Allah yaso,Koda nayi musu sallama na nufi ɗaki da niyyar kwanciya, barci ƙaurace ma idanuna sukayi ina ji a jiki na Zayyad ma baiyi barci ba kuma yana cikin damuwa gashi bani kusa dashi balle na taimaka mishi da wani abun,
Tashi nayi na kunna Torchlight sannan na buɗe jakar da na dawo dashi na ciro zoben da Zayyad ya bani na cire wani chain ɗin necklace ɗina na zura a jiki na saka a wuya na, na koma gado na sake kwanciya naci gaba da tunani,
******
Sulaiman bai san da hawan ruwan da ya saka ma sadiya ba har saida ya shiga mota zai koma gida don a nan ya bar wayan nashi, yana dubawa yaga 35 missed calls ta ajiye mishi, ba mamaki ba har tsoro sai da ya kama shi don ya san haka siddin ba zata kira shi a waya ba saidai idan wani abu take nema,"Allah yasa ba wani abu ne ya faru ba" ya furta a fili sannan yaja motar ya bar gidan,
Da shigan shi ya same ta a parlo sai kai komo takeyi idanun ta sunyi jaa alamun tasha kuka, amman duk da haka ba ƙaramin tafiya dashi tayi ba shigan ta ya matuƙar birge shi, tasha lace da jewelries ko ina sai ƙyalli take yi ga ɗaurin kanta ya zauna amman fuskar ta babu kwalliya ko kaɗan,
"Sadiya kenan, damuwa bayi hana ki gayu" ya faɗa a ƙasan maƙoshi tare da gimste murmushin shi gudun raini ya shiga haɗe da sallama,
Bata amsa sallamar ba sai tsayawa tayi tana kallon shi cike da takaici har ya ƙaraso kusa da ita zai wuce,
"Tun kafin ka ƙaro auren ne zaka fara wulaƙantani?"
Cakk ya tsaya sannan ya juyo yana kallon ta kishi ya gama cinye ta ji takeyi kaman tayi bindiga, sai yanzu ne ya gano inda ta nufa wato maganar da sukayi da safe ne ya tsaya mata a rai shi yama manta,
"Dan Allah kai ko kunya baka ji ba idanma kishiya zaka min sai da wannan ƙanƙanuwar yarinyar sa'ar ƙanwar ka na 7! Ni ban hana ka ƙara aure ba amman kayi min adalci indan zaka yi aure ka auro babba wanda nasan zan iya haɗa ƙirji da ita mu bugu idan ta nemi raina min hankali ba yarinyar da zan zaune ta ba haba!"
Bata yi tsammanin zai tankata ta ba kwata_kwata, amman sai jinshi tayi yana dariya ta kalle shi with full suprise, dariyan shi shine abinda zata iya ƙirgawa a rayuwan ta, ta yuyu ma yanzu ma wani muguntar yake shirya mata shiyasa yake yi,
YOU ARE READING
ƘARAMAR BAZAWARA (Completed)✅
Ficção Geral"Nafi son Hamma Zayyad aunty Yusrah amman idan na zaɓe shi a kan Hamma sulaiman kaman nayi butulci ne, zuciya ta ta cunkushe na rasa wanda zan zaba a cikin su ki bani shawara yaya zanyi?"... Her destiny is complicated, she is so young to face all th...